sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
 • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
 • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
 • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
 • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
 • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
 • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
 • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
 • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
 • Shahadar Fatima Azzahra A.S
 • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
 • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
 • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
 • sababun labare

  Labarun da ba tsammani

  Muna daukaka mafi daukakar ayoyin taya murna da farin ciki zuwa ga mukamin manzon Allah (s.a.w) da Ahlin gidansa tsarkaka aminicin Allah ya kara tabbata a gare su baki dayansu dangane da munasabar mauludin imam Bakir (as)
  Idan musibu sun tsananta kanka to ka dadada rayuwarka mara dadi da mai danne fushi Musa da Jawad muhammad, ya kai mai kudurin ziyara nufi yamma daga wadancan matsugunai domin kayi tuntube da aminta da aminci ka kwadaitar da ayari idan suna bukatar samun nasara, kayi dawafi mai yalwa ka ziyarce ta ka amsa kira ka yi sallama cikin zuciyarka da kan fatar bakinka ta haskakar ya yin da kira ya zo daga sama cewa har abada ba zakat aba ganina ba wancan wuta haske ne na Allah cikinta ka cire fadenka (takalmanka) biyu ka Kankan da kai idan kubbobi biyu suka bayyanu gabanka, na rantse da mai rike da rayuwarka karkashinwannan kubbobi guda biyu wutar Musa take da hasken Muhammad suna masu kusantar juna da makotaka da juna. و

  Muna daga mafi daukakar murna da taya farin ciki da murna ga mukamin manzo mafi girma (s.a.w) da Ahalin gidansa amincin Allah ya kara tabbata garesu haka ma ga mukamin bakiyatullah fi ardihi rayukanmu fansar takun kurar kafarsa haka ma ga baki dayan al'ummar musulmi da muminai mazansu da matansu ga malamanmu  masu girma dangane da munasabar zagayowar ranar haihuwar imam jawad amincin Allah ya kara tabbata gareshi.

  Daga cikin hikimomin imam Jawad (as)

  قال (عليه السلام ) :
  ((من وثق بالله أراه السرور ، ومن توكل عليه كفاه الأمور و الثقة بالله حصن لا يتحصن فيه إلا مؤمن أمين و التوكل على الله نجاة من كل سوء و حرز من كل عدو و الدين عز و العلم كنز و الصمت نور و غاية الزهد الورع و لا هدم للدين مثل البدع و لا أفسد للرجال من الطمع و بالراعي تصلح الرعية و بالدعاء تصرف البلية و من ركب مركب الصبر اهتدى إلى مضمار النصر و من عاب عيب و من شتم أجيب و من غرس أشجار التقى اجتنى ثمار المنى )) 

  Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (duk wanda ya yarda da Allah zai nuna masa farin ciki, duk wanda ya dogara da shi zai isar masa cikin al'amurra, shi yarda da Allah karfaffen shinge babu mai fakewa cikinsa sai mumini amintacce shi tawakkali da Allah tsira ne daga dukkanin mummuna hirji ne daga dukkanin makiyi addini kuma izza ce ilimu taskace yin shiru haske ne magaryar tukewar zuhudu tsantseni, babu abin da yake rushe kamar misalin bidi'oi, babu abin da ke lalata mazaje da gurbata su kamar misalin kwadayi, da shugaba ne mabiya ke gyaruwa, da addu'a musibu ke tunkudewa, dukkanin wanda ya hau dokin hakuri ya shiriya zuwa ga fagen sukuwa dukkaninwanda ya aibata shima ya aibatu dukkan wanda ya yi zagi an amsa masa, dukkanin wanda ya shuka bishiyar tsoran Allah zai tsoni kayan marmarin burace-burace.

    
  قال ( عليه السلام ) :

  (( من أمل إنسانا فقد هابه و من جهل شيئا عابه و الفرصة خلسة و من كثر همه سقم جسده و المؤمن لا يشتفي غيظه و عنوان صحيفة المؤمن حسن خلقه))

  شةهamincin Allah ya kara tabbata gareshi ya ce: ( dukkanin wanda ya yi fata daga mutum to hakika ya kwarjantar da shi dukkanin wanda ya jahilci wani abu ya aibata ita dama abu ne da yake boye yake zuwa ba zato ba tsammani, dukkanin wanda damuwarsa ta yawaita jikinsa zai rashin lafiya mumini fushinsa bai karewa, taken littafin mumini takardarsa kyawuntar halayensa.

   قال عليه السلام :
  (( العلماء غرباء لكثرة الجهال بينهم ))

  Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: ( su malamai baki ne sakamakon yawaitar jahilai tsakankaninsu)


  قال عليه السلام :
  ((لو سكت الجاهل ما اختلف الناس )) . 

  Amincin Allah ya tabbata gareshi ya ce: ( da jahili zai yi shiru da mutane ba suyi sabani da juna ba)


  قال (عليه السلام )
  ((لا يفسدك الظن على صديق و قد أصلحك اليقين له و من وعظ أخاه سرا فقد زانه و من وعظه علانية فقد شانه استصلاح الأخيار بإكرامهم و الأشرار بتأديبهم و المودة قرابة مستفادة و كفى بالأجل حرزا و لا يزال العقل و الحمق يتغالبان على الرجل إلى ثماني عشرة سنة فإذا بلغها غلب عليه أكثرهما فيه و ما أنعم الله عز و جل على عبد نعمة فعلم أنها من الله إلا كتب الله جل اسمه له شكرها قبل أن يحمده عليها و لا أذنب ذنبا فعلم أن الله مطلع عليه إن شاء عذبه و إن شاء غفر له إلا غفر الله له قبل أن يستغفره))

  Amincin Allah ya tabbata gareshi ya ce: (ka da zato ya lalataka kan aboki bacin yakini ya kyawuntaka gareshi, dukkan wanda ya yiwa dan'uwansa wa'azi a boye hakika ya yi mas ado dukkan wanda ya yi masa a bayyane hakika ya muzanta shi, mutanen kirki sun gyarantu ne da karamcinsu mutanen banza kuma sun gyaru ne ta hanyar ladabtar da su, kauna kusanci ce abar fa'idantuwa, Ajali ya isa zama hirzi, hankali da wauta basu gushe ba suna mubalaga da juna suna rigima da juna kan mutum har zuwa shekaru 18 idan ya kai wannan shekaru sai dayansu da yafi yawaita cikinsa ya yi galaba kansa, Allah bai taba ni'imta wani bawa da wata ni'ima sai bawan ya san cewa daga Allah take face Allah ya rubuta masa godiyarta gabanin ya gode masa kanta, bawa bai taba aikata wani zunubi ba sai ya san cewa Allah yana tsinkaya kansa kuma idan ya so zai iya yi masa azaba ko yafe masa face Allah ya gafarta masa gabanin neman gafarar Allah kan zunubin)

   قال (عليه السلام ) 
  (( الشريف كل الشريف من شرفه علمه و السؤدد حق السؤدد لمن اتقى الله ربه و الكريم من أكرم عن ذل النار وجهه )) 

  Amincin Allah ya tabbata gare shi ya ce: (madaukaki dukkan madaukaki shi ne wanda Iliminsa ya daukaka shi, shugabanci hakikar shugabanci na ga wanda yaji tsoran ubangijinsa karimi shi ne wanda ya karrama fuskarsa daga kaskancin wuta)