sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
  • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
  • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
  • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
  • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
  • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
  • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
  • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
  • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
  • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
  • Shahadar Fatima Azzahra A.S
  • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
  • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
  • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
  • sababun labare

    Labarun da ba tsammani

    da sunan Allah mai rahama mai jin kai hajji addini ne kuma daula ne tare da alkalmin ayatullah samahatus sayyid adil-alawi

    da sunan Allah mai rahama mai jin kai

    hajji addini ne kuma daula ne tare da alkalmin ayatullah samahatus sayyid adil-alawi

    aikin hajji ya samu kulawa da himmatuwar musulmi da manya-manyan malamansu tare da dukkanin sabanin mazhabobinsu tun ranar farko da aka wajabta shi duk da sassabawar makarantunsu na tunani da akida da fikihu, malamai sunyi rubuce-rubuce sun amfanar zaurukan nazarin muslunci da rubutunsu mai daraja game da aikin hajji da hukunce-hukuncesa  cikin litattafan fikihu, haka ma game da sirrikan hajji da hikimominsa  cikin litattafan irfani

    duk sa'ilin da  ilimi da fanni da sana'a  da fannonin fasahar zamani suka samu cigaba sai kaga mutane sun kara kusantar kara bincike kan ilimin addini,sai kwadayin samari da suke cikin kishurwar son sanin hikma da falsafar hukunce-hukunce da dalilan shari'a mai tsarki ya karu, sakamakon abin da ke cikinsa daga albarkoki da tsinkaya da sirrika, sannan kuma manufar aikin hajji da dukkanin ibadu a cikin muslunci shi ne samun azurta da rabauta da samun tsarkakakkiyar rayuwa da tsarkake zukata da haskaka kwakwale da tarbiyar ruhi haka bai tabbata face  ta hanyar aikata shari'a da fuskanta da wayewa da fikihu.

    sannan shi hajji wani karfafaffen alkawali ne da ya ke tsakanin bawa da ubangijinsa, lalle shi hajji na daga cikin mafi girman farillai tun lokacin halittar adamu har zuwa tashin kiyama. 

     


    إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكاً وَهُدىً لِلْعَالَمِينَ[1]

    lalle daki na farko da aka sanyawa mutane da ke bibakka mai albarka wanda kuma ya ke shiriya ga talikai.

    cikinsa akwai alfanun duniya da addini wadda ke tattara kan matakai daidaiku da jama'a da dukkanin zurfinta na tattalin arziki da siyasa da zamatakewa da wayewa da dai makamantansu…..

    hajji ya kasance sannan bai gushe ba ya na matsayin cibiya kuma batu da asasi ga iliman sanin Allah don tsarkake zukata da yaye su da debe haso tare da Allah matsarkaki cikin madaidaicin tsari da siradi mikakke fuskanin tsantsar kamala da kamala tsantsa gwargwadon zira’i biyu ko kuma mafi kusanci daga ubangijin talikai.

    hajji cikin ayyukansa da alamominsa na ibadu da siyasa ba komai bane face wasu damammaki da kuma masaukar imani wadda mumini da mumina ke motsawa don neman arziki madawwami, bayan canji mai zurfi na asali cikin suluki.

    lalle shi taron hajji da ake yi shekara shekara na duk duniya ya tattara kan alfanu mai girma ga dukkanin musulmi, kamar yadda cikin gundarinsa da asalinsa shi ne kusantar Allah ga dukkanin muminai

    سئل الامام الصادق  7 عن معنى المنافع في قوله تعالى : (لِيَشْهِدُوا مَنافِع ) أهي منافع الدنيا أم الآخرة ؟ فقال  7: الكلّ[2]

     an tambayi imam sadik(as) ma'anar alfanu cikin fadinsa madaukaki shin alfanun duniya ake nufi ko kuwa na lahira? Sai imam ya ce: dukkanin alfanu.

     

    bai buya ba kan cewa alfanun daidaiku da jama'a suna game dukkanin fagagen rayuwa tun daga tattalin arziki da siyasa da wayewa kai hatta alfanun askarawa da waninsu…

    shi hajji addini ne kuma daula ne, shi rayuwa ne kuma al'umma, tsakanin bangunansa biyu ya tattaro duk wata kudura ta tunani da tattalin arziki da suluki da ilimi.

     hajji mazhari ne ma'abocin haskaka ga kudurar al'umma musulma da izzarta da hadin kanta da karfinta, lalle shi akin hajji na koyar da musulmi yaya za su kasance  sai ya basu karfi da izza  ya hada sahunsu da zukatansu.

    Imam komaini ya ce shi hajji kamar misalin hajjin kirani da kowa ke amfana da shi, sai dai cewa malamai  da masu zurfafa da tsinkaya kan abubuwan da suka damu al'umma musulmi idan sun wurga zukata cikin tafkin ma'noni, sannan ba su tsaya sunyi kasa a gwiwa cikin kusanta da nitso cikin hukunce-hukunce da siyasarsa da zamantakewa  da sannu za su tsinci gwagwalan a cikin wannan tafki da ciki daga gwagawaln shiriya da hikima da `yanci, da snnu za su sha su koshi har abada daga tatacciyar hikimarsa da ilimi

    sai dai cewa yanzu meye abinyi? ina zamu tafi da wannan bakin ciki mai girma kasantuwar aikin hajji ya wayi gari abin gujewa da hijircewa kamar misalin hajjin kirani? lalle kamar yadda littafin rayuwa da kamala da kyawu ya buya gare mu dalilin hijabin da muka saka da hannuwanmu, kamar yadda aka binne taskokin sirrikan kyawawan halaye cikin turbayar tunaninmu karkatatta, harshen debe haso da shiriya ya tabarbabre ya koma harshen firgita da mutuwa da kabari…..

    haka aka jarabci hajji da wannan musiba, sai karshen al'amari ya zamanto miliyoyin musulmi suna tafiya makka duk shekara su taka kasar da annabi Ibrahim (as) ya taka tare da matarsa hajara sai dai cewa babu daya cikinsu da ke tambayar kansa game da Ibrahim da muhammadu da kuma mai suka aikata? menene hadafinsu?  me suka nufa? atakaice: lalle wajibi ne kan musulmi baki dayansu da su dage wajen sabunta rayuwar hajji da kur'ani mai girma, da dawo da su zuwa fagen rayuwarsu.

    babu shakka bayan farkawar muslunci samari sun nufi rungumar addini, lalle shi hajji ya tufatantattu da sabon bugu kadan kadan ya fara komawa hakikaninsa a cikin duniyar muslunci, muna fatan fuskantar musulmi  ga muslunci da wayewa ta karu da yunkurinsu da motsinsu na wayewa da kawo gyara.

    daga wannan tushen ne muka sanya wannan littafi muna fatan wasu ladubban ma'anawiyya da sirrikan dakin Allah mai alfarma su yaye, da alamomin wurare masu daraja da kaburbura tsarkaka, ya zama tilas ga wanda ya ke son zurfafa da nitso cikin tafkin wadannan ma'anoni  madaukaka da wannan aiki mai tsananin wahala mai albarka da ya yi bincike ya lura ya sanya hankali cikin ayoyin kur'ani da suke da alaka da hajji da ayyukansa da hukunce hukuncensa, haka ma ya duba hadisai masu daraja da aka nakalto daga annabi(saw) da imamai tsarkakan gidan wahayi da isma, lalle dukkanin sirrika da aka ambata a baya da sannu za su yaye cikin wannan ibada da waninta…. wadda ta bayyana ta yaye ga malamai da masu dandake karatu masu karamci da masana fikihu da arifai masu girma, kadai tushenta da mabubbugarta ya kasance daga ayoyin kur'ani da hadisai masu daraja.

    lalle shi hajji cikin kowacce shekara ya na ishara  da  bayyana wani babban taro na ibada da siyasar muslunci, ya zama wajibi ga wanda al'amarin ke hannunsu da su tsara da shirya masa wani tanadi don mutane su halarci alfanunsu na addini da duniya  ga dukkanin matakai da cikin kowanne fage.

    mai ya fi kyawu daga abin da mahajjata dakin Allah mai alfarma da maziyarta kabarin manzon Allah(saw) da iyalan gidansa a madina haskakakka ke dauke da shi daga wayewa da fahimta da sanin hukunce-hukunce da hikimomi cikin hajji da ziyara suna haskaka da hasken Allah suna debe haso da ambatonsa.

    a bayyana ya ke cewa shi addini bayani ne kan wasu adadin dokoki da hukunce–hukunce da ubangiji da ya sunnanta su kan bayinsa ya    aukar dasu don shiriyarsu, ya aiko da annabawa dasu don mutane su tsaya kan adalci, rayuwarsu ta kasance rayuwa ingantatta, su rayu cikin aminci su rabauta duniya da lahira.

    shi addini cikin ma'anarsa ta gama gari na nufin sallamawa ga hukunce-hukuncen Allah cikin umarninsa da haninsa shi ne musluncin da dukkanin annabawa suka zo da shi, wanda ya tattara cikin kalmar tauhidi

     (قولوا لا إله إلّا الله تُفلحوا) وقال سبحانه وتعالى : (إِنَّ آلدِّينَ عِندَ آللهِ آلاْسْلاَمُ )[3] 

    ku fadi kalmar babu sarki sai Allah za ku rabauta. Lalle addini wajen Allah shi ne muslunci.

    Hakika ya cika kuma ya kammala cika makin annabawa da manzanni muhammadu musdafa aminu (saw) ya zo da muslunci da kebantacciyar ma'ana Allah ba zai karbi sabaninsa ba daga hannun mutane kamar yadda ya ambata cikin fadinsa madaukaki:

    : (وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الاْسْلامِ ديüناً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ )[4]

    Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za a karba daga gareshi ba.

    Wannan ba ya nuni ga komai face sallamamme kammalalle cikin shari'arsa wanda babu tawaya cikinta kamar yadda annabi mafi girma ya zo da shi, sai da cewa kuma ya zama tilas a aikata shi da kiyaye sakonsa daga bata da karkata da bayanin hakikarsa da zuciyarsa da zirinsa haka na tabbata ga wanda zai tsaya kan zartar da shi da aikata wanda shi ne imami da nassi ya ayyana shi daga ubangijinsa, wanda manzon Allah ya nassaba shi, hakan ya tabbata muslunci ya kammala da shi, bayan kammalar shari'arsa- ma'ana kammalar nazari da aiki, ko kuma kace hukuma shari'a da ta zartarwa haka ya tabbata da wilayar Ali da nassaba shi a taron gadir, wanda ya kasance da umarni daga ubangiji cikin fadinsa:

     (بَلِّغْ ما أُنْزِلَ إِلَيْکَ )

    Ka isar  da sakon da aka saukar maka.

    Bayan isar da sakon da nassabawar Allah sa fadin Allah madauki ya sauka

    : (آلْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ آلاِْسْلاَمَ دِيناً([5]

    A yau ne na kammala muku addininku na cika ni'ima  na yardar muku muslunci addini.

    Wannan shi ne muslunci da kebantacciyar ma'ana, shi ne a aikace da iko da hukumar  zartarwa bayan manzon Allah(saw) har abada ba zai karbi wani addini daga wajen mutane ba koma bayan addinin muslunci kammalalle da annabta da imamanci, ma'ana da tajribar shari'a da ta zartarwa, iko da karfi biyu na shar’antarwa da zartarwa, ya zama dole a aikata shari'a da zartar da ita kamar yadda manzon Allah (saw) ya yi ishara da haka a wurare da dama ya na mai cewa:

    إنّي تارکٌ فيكم الثقلين كتاب الله وعترتي أهل بيتي ما إن تمسّكتم بهما لن تضلّوا بعديی أبداً، وانّهما لن يفترقا حتّى يردا عليّ الحوض[6]

    Lalle ni ina bar muku nauyaya biyu littafin Allah da tsatsona iyalan gidana matukar ku ka yi riko da sub a za ku bata ba bayana har abada.

    Ba zai yiwu mu ce littafin Allah ya isar mana, kamar yadda ba zai yiwu mu karbi addinin mu daga wasun alin annabi ba saboda dole ne mu komawa kur'ani da alil baiti tare cikin dukkanin sulukin mu da rayuwarmu da akidar mu da ibada da de waninsu….

    Ba boye ya ke ba cewa dukkanin mutum da tsarin halittarsa da hankalinsa lafiyayye  ya na ganin cewa shi ya na bukatuwa da addinin Allah wanda zai kaishi ga kwazazzabon rabauta da bakin gabar tafkin natsuwa da rayuwa mayalwaciya  mani'imciya duniya da lahira.

    Sannan daga cikin mafi muhimmanci da bayyana daga siffofin addinin muslunci da abin da ke tattare da shi daga kamala da kyawu da gamewarsa ta har abada, lalle shi ya game dukkanin dan adam da dukkanin hakikkaninsa ta mutumtaka da dukkanin launinsu da sabanin harshensu da garuruwansu da zamaninsu, kamar yadda ya kasance hukuma da daula duniya da lahira.

    Muslunci kamar ragowar abubuwa samammu ya zama tilas ya kasance yanada illar da ta samar da shi guda biyu cikin faruwarsa da samuwarsa, illarsa ta fa'iliya shi ne Allah matsarkaki, illarsa ta kabiliya shi ne mutum, hakan ya kasance sakamakon tsarin halittarsa ta tauhidi

    (فِطْرَةَ آللهَ آلَّتِي فَطَرَ آلنَّاسَ عَلَيْهَا لاَ تَبْدِيلَ لِخَلْقِ آللهَ) [7]

    Fidirar Allah da ya halicci mutane kanta babu canji ga halittar Allah.

    Zatin muslunci da hakikaninsa haske ne da ilimi  da rayuwa da shiriya da azurta ta har abada wanda ya zo don ya motsa hankula ya tone kasar ta fidira don ya shuka kwayar irin alherai da gaskiya da kyautatawa da adalci da karamar dan adam.

    Bai halasta ga kowanne irin mutum ya ce zai yi wasa da shi  ko kuma fassara shi da son zuciyarsa.

    (أَقِيمُوا آلدِّينَ وَلاَ تَتَفَرَّقُوا فِيهِ )[8]

    Ku tsyar da addini ka da ku rarraba cikinsa.

    Abin da ya zo daga shari'o'I mabanbanta.

    لكل منكم جعلنا شرعة ومنهاجا[9]

    Ga kowanne daya daga cikinku mun sanya shari'a da hanya.

    Kadai dai ba komai ba ne face kiyayewa ga kebanta da cigama bisa la'akari bigire da lokaci, da sassabawar da ladubba da zamantakewa ba ta fuskanin nasakinsa ba da gyara da caccanjawa wannan kenan, sannan shi hajji na daga mafi cikar alamun muslunci cikin gamewarsa ta har abada.

    قال الامام الباقر 7: «بُني الاسلام على خمسة أشياء: على الصلاة والزكاة والصوم والحجّ والولاية ، وما نودي بمثل ما نودي بالولاية[10]

    Imam bakir(as) ya ce: an gina muslunci kan abubuwa biyar: sallah,zakka,azumi,hajji,wilaya, sannan ba ayi kira da misalin kiran da akai kan wilaya ba.

    Duk wanda ke da iko kan zuwa aikin hajji amma ku yaki zuwa da gangan to lalle shi ya bar babban rukuni daga rukunan muslunci

     (وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ آللهَ غَنِيٌّ عَنِ آلْعَالَمِينَ ) [11]

    Duk wanda ya kafirce lalle Allah mawadaci ne daga talikai.

    Shi muslunci da dokokinsa da hukunce-hukuncensa ya game ya cika lalle kuma shi yak an dawwama babu tawaya babu karkata cikinsa, dukkanin ci baya da musulmi ke ciki  ba komai ya jawo musu haka face watsi da aiki da muslunci da nesantarsa, lalle imani ba wani abu bane face furuci da harshe da kuducewa cikin zuciya da aiki da gabobi. Saboda ya dole mu dage mu fahimci muslunci kamar yadda ya ke daga littafin Allah da sunnar manzonsa da hanyar imamai tsarkaka daga zuriyar annabi(as) wadanda Allah ya zabe su ya tafiyar da datti daga garesu ya tsarkakesu tsarkakewa.

    Mai ya fi yawa daga nassoshi addini da suke kwadaitar da musulmi kan neman ilimi mai alfanu da aiki nagari da fahimtar addini da sanin hukunce-hukunce da hikimomi.

    الكافي بسنده عن أبي عبدالله 7 قال : «لوددت أن أصحابي ضربت رؤوسهم بالسياط حتّى يتفقّهوا[12] .

    Alkafi da isnadinsa daga baban Abdullah(as) ya ce: ina kaunar ace an doki sahabbaina da bulala har sai sun samu fahimta.

     

    وعن مفضّل بن عمر قال : سمعت أبا عبدالله 7 يقول : «عليكم بالتفقّه في دين الله، ولا تكونوا اعراباً، فانه من لم يتفقّه في دين الله لم ينظر الله إليه يوم القيامة ، ولم يزکّ له عملاً».

    Daga mufaddal dan umar ya ce: na ji baban Abdullah(as) ya na cewa: na umarce ku da fahimtar addini, ka da ku kasance larabawan kauye, lalle al'amarin yadda ya ke shi ne dukkanin wanda bai da fahimta cikin addinin Allah, Allah bai zai kalle shi ba ranar kiyama ba kuma zai tsarkake masa aiki ba.

    وعن علي بن أبي حمزة قال : سمعت أبا عبدالله 7 يقول : «تفقّهوا في الدين فانّه من لم يتفقّه منكم في الدين فهو أعرابي ، إنّ الله يقول في كتابه : (لِيَتَفَقَّهُوا فِي آلدِّينِ وَلِيُنذِرُوا قَوْمَهُمْ إِذَا رَجَعُوا إِلَيْهِمْ لَعَلَّهُمْ يَحْذَرُونَ ) [13]

    Daga aliyu dan hamza ya ce: na ji baban Abdullah na cewa: ku fahimci addini lalle yadda al'amarin ya ke duk wanda bai da fahimta cikinku to shi matsayin balaraben kauye ya ke, Allah cikin littafinsa na cewa: don su fahimta cikin addini su gargadi al'ummarsu idan ta dawo garesu tsammaninsu sa kiyaye.

    Da makamantan wadannan hadisai masu daraja, ku taho ya zuwa fahimtar cikin addinin da sanin sirrikan hajji don mu kasance a kan basira cikin al'amarin mu, lalle Allah ya na kaunar masu neman ilimi, duk wanda ke bin hanyar cikin neman ilimi Allah zai biyar da shi hanya har zuwa aljanna, shin aljanna ba wani abu  ba ce face gidan azurtattu

     (أَمَّا آلَّذِينَ سُعِدُوا فَفِي آلْجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا) [14]

    Amma wadanda suka azurta sun a cikin aljanna madawwama cikinta.

    Misalin wannan ilimi na ubangiji mai kishi ma'abocin girma, babu mai samun haka sai ma'abocin babban rabo, ya kasance daga ahalin wannan haske mafi girma.


     



    [1] Ali imarana:96

    [2] Alkafi: juz 4 sh 422

    [3] Ali imrana:19

    [4] Ali Imran:19

    [5] Ma'ida:3

    [6] Na yi rubutu da bayni fila-filla kan wannan hadisi game daisnadinsa da mataninsa  da abin da ya ke nuni gareshi cikin littafi(fi rahabil hadisil saklaini) ya na da shafi 500 cikin mausu'atu raisalatil islamiya, mai bukata sai ya koma garehsi.

    [7] Rum:30

    [8] Shura:13

    [9]Ma'ida:48

    [10] Wsa'ilul shi'a kitabu hajji da kitabu salat

    [11] Ali Imran:97

    [12] Alkafi juz 1 sh 21

    [13] Tauba:122

    [14]Hudu:108