sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
  • Laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye cikin dandali sadar da zumunci na Instagram
  • Muhadarorin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Ramadan Mai albarka a shekara ta 1442 hijiri
  • Allah ya farantawa kwanakinmu da naku, muna farin cikin nuna murna da farin ciki ga al’umma musulmi shi’a da sunna kan haihuwar Imam Mahadi
  • MUNA TAYA KU MURNAR TUNAWA DA RANAR HAIHUWAR IMAM HUSAINI A.S
  • Allah ya faranta kwanakinku da namu cikin tunawa da ranar da aka aiko da Annabi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar kofar samun biyan bukatu Imam Musa Alkazim (A.S)
  • muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
  • Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
  • Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
  • Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
  • Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
  • Shahadar Fatima Azzahra A.S
  • Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
  • Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
  • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
  • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
  • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
  • sababun labare

    TUNAWA DA SHAHADAR IMAM MUHAMMAD JAWAD MUTUM NA TARA DAGA IMAMAI (AS)




     

    Imam Jawad (as) yayi zamani da wani yanki daga halifancin Mamun Abbasi. da kuma shekara biyu daga halifancin Mu’utasim, amma Mamun wanda shine ake zargin ya kasha Imam Rida (as) hakika yayi bakin kokarinsa cikin jawo `dan Imam Rida (as) Al’imamul Jawad (as) domin yayi amfanin da hakan cikin kare kasan daga tuhumar da take kansa ta kashe masa mahaifi, sai ya mike da kiransa daga Madina ya bijiro masa da diyarsa Umma Fadal domin ya aura masa ita yana mai saran surukanta da shi zata kwace shi ta cece shi cikin mantawa da jinin mahaifinsa da ya zubar, sai dia cewa kuma wannan hukuncida fuskar saura mazajen da suke kewaye da Mamun , hakan ya sanya musu damuwa kan makomar karagar Abbasiyawa, sakamakon tajribar da aka samu daga wilayatul ahad (mai jiran gado) da ya baiwa mahaifinsa Imam Rida (as) wqacce da ga baya ta zamarwa Mamun kadangaren bakin tulu, lallai sanin hakan ya sanya musu damuwa ba karama ba, fadawan Mamaun sun yi bakin kokarin gamsar da Mamun da ya janya wannan shahawar da ya yanke ta baiwa Imam Jawad (as) diyarsa , sai dai cewa bai saurare su daga karshe sai suka mika wuya suka janye , suka ce masa lallai shi yaro karami bai da fahimtar ilimi da addini da wayewa, ka kyale shi lokacin da yayi karatu ya samu ilimi ya cika sharudda cancantuwa da ya kasance surikinka sai ka bashi ita, sai Mamun ya kyakyace da dariya daga wadannan hujjoji na su da suka kawo domin hana shi zartar da wannan shawara da yanke ko kuma dai alal akalla ya jinkirta al’amarin, shi Mamun mutum ne mai kaifin basira ya sa matsayin wannan gida da ma’abotansa, lallai kuma su iliminsu ba ya samuwa ta hanyar koyo d aka saba da shi, sai ya basu shawara da su jarraba shi cikin duk abinda suke so daga ilimummuka idna ya zama ya gaza bada amsa ya fadi jarrabawa to zai dauki shawararsu, amma kuma idna ya amsa ya ci jarrabawa to zai zartar da shawararsu ba su kuma da hakkin kin mika wuya.

    Sai fadawan nasa suka yadda, suka zabi ranar da zasu jarraba sho aka kira Alkalin Alkalai na zamanin wato Yahaya ibn Aksam, suka nemi ya zabo matsananta mas’loli masu wuyar amsawa wadanda zasu rusa shirin Halifa suka sanya su cimma haduffansuna hana yin wannan aure, rana bata karya sai lokaci yayi mutane suka taru, Alkalin Alkalai ya nemi izinin Mamun cikin bashi dama ya fara yiwa Imam Jawad (as) tambaya kan ba’arin wasu mas’alolin fikhu, sai yayi yana mai bashi damar faraway, sai Alkali ya matso ya kalli fuskar wannan karamin yaro yana mamakin ma ta yaya za a ce ya kawo wadannan manya-mayan tambayoyi ga wannan `dan karamin yaro, sai dai babu yada dole ya gudanar da bukatar wadancan fadawan Halifa tunda dai sune suka kirawo kan wannan batu, tana ma iya yiwuwa sun yi masa alkawarin bashi kyautuka idna ya tabbatar musu da bukatarsu da burinsu cikin rusa shirin Halifa na aurar da diyarsa ga Imam Jawad (as).

    Sai Yahaya ibn Aksam ya cewa Imam (as) raina fansarka shin ka yi mini izini cikin tambaya, sai yace masa: tambayi abinda kake so.

    Sai Yahaya ibn Aksam yace: me zaka ce cikin mutumin da ya daura ihrami sai kuma ya kashe abin farauta?

    Imam (as) yace: shin ya kashe shi wajen harami ko cikin harami, shin yana sane ko kuma cikin jahilci, shin ya kashe shi bisa ganganci ko cikin kuskure, shin mutumin bawa ne ko kuma yantacce, shin yaro ne karami ko babba, shin yanzu ne ya fara kisan ko kuma dama a baya ya taba yi, shin abin ya kashe daga cikin masu tashi sama ne ko kuma waninsu ne, shin daga kananan dabbobi ko daga cikin manyansu, shin ya kafe kan abinda ya aikata ko kuma yayi nadama, da daddare ne lamarin ya faru ko da tsakar rana, ya dau haramin umara ko ko hajji?

    Wannan tambaya da jawo ambaliyar tambayoyi wanda hakan ya bayyanar da jahilcin mai yin tambayar da rashin kewayar sa da filla-fillan maudu’in, ya kamata ne ace shi mai tambaya yayi ta cikin dandakewa ya iyakance abinda yake nufi cikin tambayar ta sa daga rassa ta yanda amsa ba za ta kasance gamammiya ba da ta shafi wasu abubuwa da ba it aba.

    Imam (as) bai bashi amsa ta hanyar da aka al’adantu da it aba, domin tun farko ya san cewa shi mai tambayar bai yi tambayar domin neman fahimtar hukuncin shari’a da ya buya gareshi ba, kadai dai yayi tambayar ne da niyyar kure da kalubale da jarraba ma’arifa da sanin Imam (as) domin sanin shin ya sani ko bai sani ba, sai amsa ta kasance mai gamsarw amai warwarewa mai wadatarwa da cikawa, bayan ya Imam (as) ya sauke nauyi, sannan bawai kawai ya tabbatarwa abokin rigima cikar iliminsa kadai ba, bari dai ya tabbatar da jahilci abokin husumarsa cikin yiwa tambayarsa filla-filla.

    Wannan raddi ya sauka kan Alkalin Alkalai kama misalin tsawa, ta kai ga a bai san mai yake fadi sakamakon rudewa, sannan yan fada sun fi kowa shiga dimuw ada dimauta da shan mamaki, babu wanda ya iya buda bakinsa yayi Magana daga cikinsu, Mamun yaji cewa yayi nasara, ya nemi Imam (as) a take wannan lokaci ya karanta hudubar aure a zartar da bukukuwan, Mamun ya cimma abinda yake son cimma, bayan haka sai Mamun ya nemi Imam (as) yayi bayani dalla-dalla kan tambayar da Alkali yayi tareda dukkanin fuskokin da ya kawo cikinta, sai yayi bayani filla-filla ya bada amsa ga kowacce fuska da ya kawo.

    Kari kan cikin gamsar da fadawan Sarki kan kuskuren su sai ya nemi Imam (as) da yayi tambaya ga Alkali domin ya jarraba shi, tambayar ta kasance mai dimautarwa Alkali ya bayyana gazawarsa daga bada amsa sai ya nemi Imam (as) ya bada amsa da kansa.

    Dole dai fadawan su ka rungumi wannan sabuwar hakika mai radadi cikin zukatansu, su ka zauna suna jira da dakon abinda zai zo daga baya kan girgiza karagar da rsuhewarta, daga afkuwar hakan a hannun waninsu daga Abbasiyawa.

    Imam (as) ya dauki amaryarsa ya dawo madina, abind ayafi damunsa shine cigaba da isar da sakon kakanninsa masu daraja kan daukar wannan nauyi da dukkanin wahalhalun da suke kunshe cikinsa don yada ilimin gidna Manzon Allah (s.a.w) sannan ya kara dawowa birnin Bagdaza, jiga-jigan malaman fikhu da hadisi sun kasance cikin jiransa domin su kwankwada daga iliminsa su bijio masa da tambayoyi da kuma dukkanin abinda ya shige musu duhu, daga karshe dai halifancin Mamun Abbasi ya zo karshe, danan ne kuma Almu’utasim ya karfi jan ragamar halifanci bayan dan’uwansa Mamun.

    Almu’utasim bai jin dadin matsayi da girmamawar da Imam Jawad (as) yake tare da ita ba tsakankanin sahabbansa ko kuma a wurin wanda ya gabace shi Mamun. Da’imam Almu’utasin yana ambaton tajribobin da magabatansa su ka fuskanta daga daidaikun mutanen wannan gida wanda ya wanzu tsahon zamani cibiyar girgiza karagun mulkinsu, Almu’utasim ya jibanci halifanci a shekara ta 218 bayan wafatin Mamun, Almu’utasim ya kasance yana jira da dakon wata dama ta samu domin kashe Imam Jawad (as), kwatsam sai gas hi damar da yake ta tsimayi ya sameta ta yanda ya sadada ta hanyar diyar `dan’uwansa Mamun matar Imam (as) wato Ummu Fadal, ya samu labarin cewa sun samu rashin daidaito tsakaninsu da rashin zaman lafiya sakamakon kishin da take kan sauran matansa, sai Almu’utasim ya nemi ta shayar da shi guba cikin inibi, sai ta aikata bukatar Almu’utasim , lokacinda ta ga Imam (as) yana shan radadin mutuwa yana kokawa da ita sakamakon radadin sammun da gubar da shayar da shi sai ta yi nadama kan abinda ta aikata ta fashe da kuka, sai dai cewa lokaci ya rigaya ya kure ga wannan kuka nata kuma nadamar ta ba zata amfane da komai ba ta rigaya ta kashe hujjar a doran kasa jagoran musulmai, tsarkakakken ruhinsa ya cirata ya daukaka zuwa sama domin ya riski kakansa (s.a.w) da sauran babanninsa tsarkaka wadanda suka gabace shi, an binne shi kusa kakansa Imam Kazim (as) a Kazimiyya tsohuwar makabarta da ake kira da makabartar Kuraishi.