mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

WANNE DALILI NE YA HANA IMAMAI (A.S) BAYYANAR DA ALLON FATIMA A.S

Salam Alaikum. Samahatus Assayid Allah ya dawwamar daku cikin izza, ina kawo tambaya ta zuwa ga mukaminku ina mai sa ran samun amsa da Karin bayani da fahimtar da ni.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Salam Alaikum. Samahatus Assayid Allah ya dawwamar daku cikin izza, ina kawo tambaya ta zuwa ga mukaminku ina mai sa ran samun amsa da Karin bayani da fahimtar da ni.

Menene sababi da dalilin da ya hana A’imma (a.s) bayyanar Allon Fatima Assidika amincin Allah a kara tabbata a gareta wannan Allo da yake da aka ce yana dauke da sunayen A’imma haka zalika makamin yakin Manzon Allah tsira da aminci ya tabbata a gareshi da iyalansa tsarkaka wannan makami da yake cirata daga Imami zuwa Imami har ya zuwa Imami na karshe, haka zalika Sulken yakin Manzon Allah (s.a.w) da litattafai da gadon A’imma (a.s) daga Jifri da Jami’atu da Mus’haf, dukkanin wadannan abubuwa me ya sa basu bayyanawa mutane su musammam `ya`yan shugabanmu Hassan da kuma wasu ba’ari daga `ya`yan Husaini amincin Allah ya kara tabbata a gare shi daga cikin wadanda suka yiwa Imamai jayayya cikin imamanci da cancantuwarsu me ya sa basu fito da wadannan abubuwa sun kafa musu hujja da dalili da su.

Wassalam.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hakika wani abu daga abinda yake shiryarwa kan cewa A’imma (a.s) sun bayyanar da ba’arin abubuwa da suke ajiyar Annabta ne ga wasu kebantattu daga Sahabbansu ya zo, kana iya komawa ka duba littafin Alkafi  cikin mujalladi na farko zaka samu bayani daga A’imma amincin Allah ya kara tabbata a geresu cewa sun bayyana ajiyar Annabta zaka samu bayani filla-filla kan haka

Tarihi: [2019/9/16]     Ziyara: [564]

Tura tambaya