mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Zira kwai ta hanyar tiyo

Assalamu alaikum
Malam ni me aurene ina da yaya har uku duka mata amma na kasance me son da namiji, shin zan iya zuwa asibiti a sanya kwan wani sannan na bukacesu suyi wani hanya da dan cikin zai kasance namiji?
Ko kuma mu jira ikon Allah?
Bazan boye ba amma ina tunanin kara aure amma maudu’in anan shine menene hukuncin zuwan mu asibiti don yin wannan aiki da na Ambato? Wani shawara zaku bamu?
Da sunan Allah me rahama me jin kai


Kar ka ke tunanin Karin aure sannan kuma ka hakura da rabon da Allah ya baka, hala in kayi hakan sai kaga Allah ya baka da nan gaba wanda zai cece ka nan gaba kuma ya kasance ya kare maka mutuncin ka a idon mutane  amma su mata zasu tafi gidan mijin su kamar fadin sheikh Ansari: ya kasance bashi da yaya maza sai mata amma in muka duba zumaga har yanzu akwai zuri’ar sa, kar ka kasance ka yanke tsammani daga Allah, ka mika duk kannin lamuran ka da na matar ka zuwa ga Allah, zaka iya duba wasu khutumat a cikin wannan site na mu na alawy.net domin samin biyan bukatu.


Tarihi: [2016/9/8]     Ziyara: [680]

Tura tambaya