mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Mene ne ya sa Fakihai suke kokarin tsarkake ijtihadinsu da fatawowinsu

Salamu Alaikum.
Hakika mun san cewa taklidi na nufin Jahili cikin ayyananniyar mas’ala ya koma ga Malami domin yi masa bayani da yaye jahilcinsa cikin mas’alar, sai dai cewa kuma me yasa muke ganin Fakihai na kokarin samawa fatawowinsu tsarkaka, mene ne ya sanya suke baiwa kawunkansu gaskiya kan haka? Shin akwai wani dalili na shari’a na yankan shakku tabbatacce cikin hakan domin mu yi riko da ijtihadin wani mutu ko kuma ba wani dalili da hujja cikin hakan.

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Wannan ba kokari ne suke yi kadai hakika ce daga haka’ik hakan ya kasance tareda da la’akari da cewa dalilan Fikhu daga littafin Allah da sunna suke gangarowa kuma dukkanin biyun suna daga mafi tsarkaka tsarkakakku a wurin muslunci, idan ya kasance tushe tsarkaka yana da tsarkin da gaske to lallai natija da duk abinda ya bubbugo daga gareshi zai kasance tsarkakakke, na’am akwai abu guda da ya rage mu shi’a mun yi Imani cewa ra’ayin mujtahidi zai iya kasancewa kuskure bawai kamar yanda `yan’uwanmu musulmi suka tafi kan cewa daidai a kowanne hali, kamar yanda muke Imani cewa zai iya dacewa da kuma kasancewa daidai cikin istinbadi da ijtihadinsa da yayi daga littafin Allah da sunna, idan ya dace da daidai to yanada lada guda biyu, ladansa kan wahali da gumin da ya sha lada na biyu kuma kan dacewa da yayi, idan kuma ya kuskure yana da lada `daya, kan wannan Fikhu yake da girma tsarkaka, amma komawa zuw aga A’alam wannan wani abu ne da hankali da lafiyayyar dabi’a suke hukunci da shi, nayi bayani dalla dalla cikin wannan a littafina mai suna (Alkaulul rashid fi ijtihadi wat taklidi) mujalladi guda uku, akwai shi ciki sayit dinmu sai ku koma can ku duba.

Tarihi: [2020/8/5]     Ziyara: [424]

Tura tambaya