mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

gameda hakkokin shari'a da ya ratayu kan miji da mata da Allah ai mana karin bayani Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?

TAKATACCIYAR AMSA: dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna, addini muslunci domin iyali su samu tsayuwa da dawwama ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana wasu wajibai kansu, duk sa'ilin da aka ce akwai hakkoki to ubangiji na sanya wasu hukunce hukunce ciki, wannan makala tana da danganta ka da tambayar da ta gabata kan hakkokin maza da su ka hau kan mata, daga mafi girman hakkokin maza na shari'a da na dokoki da suke kan mata.
1 dole mace ta rungumi shugabancin miji: idan cikin rayuwar auratayya wata matsala ta bijiro, to warware wannan matsalar na wajen miji sai da cewa wannan shugabanci na miji bai kamata ya fita daga kyawunta zamantakewa ba, ka da kasantuwarsa na hakkokin shari'a da dokoki ya zamanto dalili da zai sanya miji munantawa iyali.
2 tilas mace ta mallakawa mijinta kanta: wajibi mata ta kasance cikin shirin amsa kiran mijinta don biya masa bukatarsa ta sha'awa sai dai idan ta na da wani uzuri na shari'a ko na doka da zai hana ta amsa kiransa kamar jinin haila da ke bijiro mata wata wata ko kuma wata rashin lafiya.
3 biyayyar miji a mahallinsu da gidan da suke zaune, sai dai idan mijin ya sallamawa matarsa wannan hakki nasa, ko kuma a al'adarsu mace ke da wannan hakki ku kuma wata larura mace ke da ita wadda za ta iya cutar da rai ko

DA SUNANSA MATSARKAKI

gameda hakkokin shari'a da ya ratayu kan miji da mata da Allah ai mana karin bayani Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?

 

TAKATACCIYAR AMSA: dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna, addini muslunci domin iyali su samu tsayuwa  da dawwama ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana wasu wajibai kansu, duk sa'ilin  da aka ce akwai hakkoki to ubangiji na sanya wasu hukunce hukunce ciki, wannan makala tana da danganta ka da tambayar da ta gabata kan hakkokin maza da su ka hau kan mata, daga mafi girman hakkokin maza na shari'a da na  dokoki da  suke kan mata.

1 dole mace ta rungumi shugabancin miji: idan cikin rayuwar auratayya wata matsala ta bijiro, to warware wannan matsalar na wajen miji sai da cewa wannan shugabanci na miji bai kamata ya fita daga kyawunta zamantakewa ba, ka da kasantuwarsa na hakkokin shari'a da dokoki ya zamanto dalili da zai sanya miji munantawa iyali.

2 tilas mace ta mallakawa mijinta kanta: wajibi mata ta kasance cikin shirin amsa kiran mijinta don biya masa bukatarsa ta sha'awa sai dai idan ta na da wani uzuri na shari'a ko na doka  da zai hana ta amsa kiransa kamar  jinin haila da ke bijiro mata wata wata ko kuma wata rashin lafiya.

3 biyayyar miji a mahallinsu da gidan da suke zaune, sai dai idan mijin ya sallamawa matarsa  wannan hakki nasa, ko kuma a al'adarsu mace ke da wannan hakki ku kuma wata larura mace ke da ita wadda za ta iya cutar da rai ko

 

lafiyarta.4 biyayyar miji a wajen gida da shigar da baki cikin gida, a al'adance sai dai a lokacin sauke hakkin addini na wajibi kamar fita zuwa aikin hajji ko kuma fita don yin magani ko kuma ya zamanto zaman gida zai cutar da rai ko jiki da mutuncinta.

5 biyayyar miji da neman izininsa kan yin aiki a wajen gida da nau'in  aiki, a yanayin da ya sabawa al'adar zamanin da matsayin jinsin maza da mata ya kasance.

 

AMSA FILLA FILLA: Allah madaukaki ya halicci mace da namiji da yanayin da kowanne dayansu na bukatuwa da daya bukatuwar  gangar jiki da ta ruhi, samuwa da wanzuwar kowanne ba ta yiwuwa ba tare da dayan ba, kammaluwar ruhi da gangar jiki ba ta yiwuwa sai suna tare da juna, masana hikima na cewa kowacce halitta yanki ne daga wata halitta kamamalalliya, dukkaninsu tawayayyu ne matukar basu kasance tare da juna ba saboda kowanne dayansu na kammala daya.

Bisa lura da banbanci tsarin  halittar jikin mace da namiji da banbancin ruhi sai ubangiji ya sanyawa kowanne dayansu hukunce hukunce da hakkoki da sukayi tarayya cikin wasunsu, a wasunsu kuma kowanne ya kebantu da nasa don samun lamincin bukatun duniya da na lahira  ga kowanne dayansu.

Wadannan hakkoki da hukunce hukunce  malamai  sun kallesu daga mahanga uku: 1 mahangar fikihu 2 mahangar kyautata dabi'a{akhlak} 3 mahangar hakkoki.

Sakamakon a wannan wajen muna yunkurin amsa tambaya da akayi kan hakkokin mace da ke kan miji, sakamakon wajibai na akhlak da ruhi suke kammala da cika wajiban hakki da dokoki da kuma kasantuwar wajibai na fikihu ba su da banbanci mai yawa da wajibai na hakkoki da dokoki to zamu takaita bayani kansu.

wajibai da ayyuka na akhlak:

ayyuka da wajibai na akhlak da ke kan mace sun kasu kashi biyu kamar yadda ya zo a harshen riwayoyi sune kima da muhimmancin  zama da miji da tattala shi.

 Manzon Allah{s.a.w} ya ce: da ace sujjada na halasta ga wanin Allah da na umarci mace ta yiwa mijintaا  

Hakkin miji kan matarsa yafi kowanne hakki yawa da daraja

Jahadin mace shine jurewa cutarwar da mijinta ke mata.

 

Bai kamata mace ta fusa ta mijinta ba koda kuwa mijin ya cuta mata.

 

Ba a karbar aikin dukkanin matar da mijinta ke fushi da ita.

 

Dukkanin matar da ba ta godiya ga mijinta dukkanin aikin da ta yi ba za ta samu lada ba.

 

2 ayukan akhlak na zama da miji:

Bai kamata ace mace ta na da karkata da sha'awar kallon wani wanda ba mijita ba idan ta kasa kiyaye hakan to matsayin  mazinaciya ta ke wajen ubangiji.

 

Tilas ne mace ta kasance ta na amsa bukatun sha'awa na mijita a kowanne lokaci da kowanne yanayi ko da kuwa ta na kan gadon bayan rakumi dole ne idan ya nemeta ta amsa bukatarsa, idan kuma ta ki aikata hakan to  mala'iku za su la'ance ta.

 

Bai halasta mace ta yi azumin mustahabbi ba tare da izinin mijinta ba, da dukkanin aikin mustahabbi.

 

Bai kamata mace ta tsawaita sallah ba ta yanda yin hakan zai hana amsa bukatar mijinta.

 

Bai kamata mace ta yi sadaka ba tare da neman izinin mijinta ba.

 

Bai halasta mace ta fita wajen gida ba tare da izinin mijinta ba, idan ta aikata hakan mala'ikun sama da kasa zasu yi ta tsine mata har lokacin da za ta dawo gida.

 

Ya kamata mace ta cancadawa mijinta ado ta sanya turare, bai halasta ta sanyawa wanda ba mijinta ba turare idan ta ki kiyaye hakan sallolinta ba za su karbu ba.

 

Wajibai na hakkoki da doka:  za mu yi bayanin hakkoki da mace da miji su kayi tarraya da wanda ba suyi tarayya ba ciki.

Wajibai da mata da miji su kayi tarayya ciki:1 Kyautata zamantakewa da juna: wajibi ne mata da miji su kyawunta zamantakewar su ta rayuwar aure dole ya zamnato akwai tausasa harshe da sakin fuska da murmushi tsakanin junansu  kamar yadda yake wajibi su kauracewa munanawa juna da miyagun kalamai sai idan yin hakan na da wani uzuri na shari'a ko na al'ada.

 

2  taimakon juna: dole ne mata da miji ya kasance suna aiki kafada da kafada don karfafar  rayuwar su ta iyali da cigabanta, ma'aunin wannan  taimakekeniyar juna ya doru bisa al'adun inda suke rayuwa, kamar misali ace  idan a al'adun wajen da suke rayuwa  ya zamanto shayarwa da lura da gida  na wuyan mace sannan ayyukan wajen gida na kan wuyan miji to a irin wannan lokacin ya kamata matar da mijin su hadu su taimakawa junansu don sauke wadannan ayyuka.

 

3 tarbiyantar yaro: mata da miji ababen tambaya tambaya ne kan tarbiyyar dansu gwargwadon ikonsu bisa  la'akari da wajen da suke rayuwa da zamani da al'ada, dole ne su zage dantse su yi iya kokarinsu wajen yi masa tarbiyyar ta gari.

 

4 cika alkawari: bai halasta mata da miji su kulla wata alaka wadda ta sabawa shari'a da wani mutum daban.

 

Wajibai da suka kebantu da mace :

1 rungumar shugabancin miji: idan ya kasance wata matsala ta bijiro musu cikin rayuwarsu ta aure to warware wannan matsala na hannun miji sai dai cewa bai kamata miji ya fita daga da'irar kyautata zamantakewa ba yayin da yake yunkurin warware wannann matsala ka da kasantuwar shari'a da doka ta bashi dama ya zamanto dalilinsa na yin amfani da wannan damar ta hanyar da ba ta dace ba.

 

2 salllama kanta ga mijinta: ya kamata mace ta kasance cikin shiri amsa kiran bukatuwar mijinta ta sha'awa gwargwadon iyawar jiki da ruhi bisa al'ada sai idan ta na wani uzuri na shari'a ko al'ada kamar misalin jinin haila ko rashin lafiya wanda zai hana ta hakan.

 

3 biyayya ga miji a cikin gida, sai dai idan shi mijin ya sallama wannan hakki na sa ga matar tasa, ko kuma ya kasance sabanin al'adar  zamantakewa da aka saba da shi ya zamo ace biyayyar na hannun mace ko kuma  ya kasance akwai larura da za ta iya cutar da rai ko lafiyar  ita macen.

 

4 biyayyar miji a wajen gida cikin fitar ta unguwa da shigowar baki cikin gidan, sai cikin sauke hakkin shar'a na wajibi ko neman magani a irin wannan wuraren wannan wajibi na saraya, ko kuma idan zamanta cikin gida na iya cutar da lafiyar ta da mtuncinta.

 

5 biyayya da neman izinin miji cikin yin aikin kwadago da irin nau'in aikin cikin yanayi da ya sabawa al'adar zamani da wajen da suke rayuwa da jinsin mace da na miji.

Ya zuwa yanzu munyi bayanin hakkokin miji kan matarsa atakaice, yanzu za muyi kokari yain bayanin hakkoki mace kan miji atakaice.

Kasha na uku hakkokin mace da ke kan miji: hakkokin mace da ke kan miji sun kasu kasha biyu 1 hakkokin kyautata dabi'a{akhlak} 2 hakkokinta na shari'a

.

Hakkokin kyawunta dabi'a a mahangar riwayoyi

1 kyawunta halayya tare da mace: ya zo cikin hadisi cewa son mata na daga dabi'un  annabawa{as}.

2 nuna soyaya da kauna ga mata annabawa ba sa gafala da shi cikin kowanne hali.

3 kau da kai da yafiya ga mata yayin da suka nuna wata halayya mara kyawu.

4 murmushi da sakin fuska da kyautata musu mu'amala.

6 mafi kasantuwa abin so cikin maza shi ne wanda ya fi kowa kyautatawa ga matarsa.

7 jin tsoron ubangiji da kauracewa take hakkin matarsa.

 

Wajiabi na akhlak:1

 dole ne ya dinga kallon matarsa kamar matsayin wata furen fulawa mai dadin kamshi ba wai ya dinga yi mata kallon baiwarsa ba.

2 dole ne ya tanadar mata kayyakin ado na zamani da kayan sawa  da kayayyakin marmari musammam lokutan bikin  sallah

3 ya kamata ya dinga shawara da matarsa cikin muhimman lamuran rayuwa.

4 kiyaye hakkokin da akhlak na kusantar mata don biyan bukata.

 

Hakoki da suka kebantu da miji.

1 bada kudade ga matarsa  don sauke hakkin ciyarwa.

    2 samar mata da abin da za ta ci gwargwadon yadda bai sabawa al'ada ba da inda suke rayuwa ba.

3 samar mata da tufafin da za ta sanya gwargwadon al'adar garin da suke rayuwa.

4 samar mata da gidan da zata zauna bisa yadda al'adar inda suke rayuwa.

5 samar mata kayayyakin ado daidai gawragwado.

6 samar mata da mai mata aikace aikacen gida idan haka al'adunsu suka tafi kai ko kuma saboda larura ta rashin lafiya.

7 samar mata da magani yayin rashin lafiya.

 

Hakkokin kusantar juna don biyan bukatuwar sha'awa:

Dokoki sun kame baki a wannan fage sun wadatu da kyautata zamantakewa, sai dai cewa malaman fikihu sun kasa abin zuwa kashi biyu.

1 hakkin mace da ke kan mijinta  shi ne cewa idan miji ya auri budurwa to dole ya shiga dakinta har zuwa tsawon kwanaki bakwai idan kuma bazawara ce to kwanaki uku, idan kuma matarsa daya to dole cikin kwanaki hudu ya bata dare daya ragowar ukun kuma ya na da yanci yin yadda ya ga dama da su, idan kuma ya na da mata da yawa to cikin hudu kowacce na da daya.

2 kusantar jinsi ta biyan bukatar sha'awa: wajibi ne  miji ya kusanci matarsa sau daya cikin watanni hudu kasantuwar hakan na daga hakkinta na wajibi da ke kansa.

 

Tarihi: [2017/5/23]     Ziyara: [2964]

Tura tambaya