mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Shin shi’ar Fatima za su ga haskenta a ranar kiyama ko suma suna daga cikin wadanda za su kau da idonawansu lokacin ketara siradinta.

A cikin littafin kasa’is alfatimiya juz 1 sh 325 mawalaffin littafin ya kawo cewa sayyada Fatima (as) za ta yi tajalli da haskenta mai farantawa zukata sai ya zamanto ya kewaye dukkanin wadanda aka tasa a ranar taso wato kiyama sai ta razana idanun na farko da na karshe, zukata su jebance shi, Ambato ko tunani ko himma basu wanzuwa face sun kebantu ya zuwa kallon kyakkyawan hasken Fatima (as). Haka zai ai yekuwa da kira cikin wanda aka tashe su ace musu ku rufe idanuwanku ku kau da ganinku ku sunnkuyar da kawukanku, babu wani mutum guda da ke da karfin ganin kyalkyalin hasken Fatima (as) a dukkanin cikin duniyar malakutiyya da filin kiyama, ku rufe idanunku …. Ya zuwa karshen julmar.

Tambaya: ta yaya za ta mamaye haskenta kan dukkanin wanda aka taso a kiyama idanu su firgita da mamaki waye ya ganta da har ya yi yekuwa da umarnin a rufe idanu shin wannan yekuwa da kira ya na zuwa bayan yayewa da tajalln haskenta a ranar kiyama, idan ya kasance hakan shin shi’arta za su ga haskenta ko kuma suma bai daya suke da sauran mutane da suke rufe idanuwansu sannan ta yaya za ta tseratar da su daga wuta,
Allah ya saka muku da alheri muna jiran amsarku.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Lallai ranar tasowa daga kabari na kusa-kusa garemu idan mutum ya mutu to kiyamrsa ta tsaya, a wannan lokaci ne abubuwa za su yaye gabansa

 (فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَاءَكَ فَبَصَرُكَ الْيَوْمَ حَدِيدٌ)

Sai muka yaye maka rufinka daga barinka yau ganinka na da kaifi.

ma’ana basirarsa da ganinsa na da karfi, sai ya mu dinga hakikanin abubuwa a duniyar barzahu kamar yadda suke mu kuma dinga tsinkayar tsarkakkun ilimai, sannan mu samu kewayar haske cikin duniyar imkani (duniyar yiwuwa) lallai ita na daga kewayar haske cikin duniyar wajibul wujud (wanda samuwarsa ta zama tilas ga zatinsa), lallai Allah shi ne mai kewaya kan komai kewayarsa tana tajalli cikin duniyar imkani cikin muhammadu da iyalansa amincin Allah ya tabbata garesu, haskensu na kewayar kan dukkanin halittu cikin duniya da lahira bawai lahira kadai ba, sannan babu wani mutum da zai iya kallon wannan haske mai girma daga ma’adanin girma face dai wanda Allah ya yi masa izini saboda haka ku rufe idanunku duk da cewa kuwa kun kasance kuna ganinta da basirar idaniyar zuciyarku ya yinda zuciya ta zamanto

لِمَن كَانَ لَهُ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى السَّمْعَ وَهُوَ شَهِيدٌ ،

ga wanda ke da ita ko kuma ya jefa ji alhalin yana mai shaidawa.

Allah ne masanin hakikanin lamurra.   

 

Tarihi: [2017/7/24]     Ziyara: [797]

Tura tambaya