mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wasu daga cikin tambayoyi

Tambayoyin da akafi karantawa

Ka kara hadisan manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi da hadisan ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata gare su kan abubuwan da ka sani na riwaya a baya


Kamar yadda ka sani cikin kowanne ilimi da fanni da sana’a wanda ya kasance yafi kwarewada ilimi cikin fanni da ilimi da sana’a daga waninsa yana bayyana da zuhuri kan fagen cikin dukkanin kwararru da da masu kaifin basira, aka basu kyautukan girmamawa kamar yadda al’amarin yake cikin wasannin motsa jiki, duk wanda ya samu nasara ya zo a sahun farko zai rabauta da sarkar yabawa ta zinariya, na biyu kuma a bashi sarkar azurfa na uku kuma a bashi sarkar tagulla kamar yadda suka kebantu da kebantaccen matsayi cikin al’umma kan ragowar mutane gama gari.
Ya kake ganin karfafa kwararru jarumai sadaukai a wajen Allah da wajen annabwan Allah da wasiyyai da waliyyanm Allah matsarkaki?

 

Karanta tare da ni wannan hadisi mai daukaka daga manzon Allah tsira da aminci su kara tabbata gare shi da iyalansa har ka san su wane ne jarumai na gaskiya, ka kara karantawa tare da lur ada fadakuwa da sanya hankali cikin kowanne karo z aka karu da sabon ilimi.

قال صلی الله علیه واله وسلم: قال الله سبحانه: إذا علمت ـ أي إذ كان عبدي هكذا ـ أنّ الغالب على عبدي الاشتغال بين نقلت شهوته في مسألتي ومناجاتي، فإذا كان عبدي كذلك، فأراد أن يسهو حِلتُ بينه وبين أن يسهو، أُولئك أوليائي حقاً، أولئك الأبطال حقاً.

Manzon Allah tsira da aminci su kara tabbata gare shi da iyalansa ya ce: idan ka sani- ai lokacin da bawana ya kasance cikin wannan hali na sani-lallai galibi kan bawana shi ne shagaltuwa tsakankanin kai kawon sha’awarsa cikin rokona da munajatina, idan ya kasance haka, sai ya nemi rafkanuwa zan shiga tsakaninsa da rafkanuwa, wadancananka sune waliyyaina na hakika, wadancananka sune jarumai.

Ya zo a wani hadisin daga manzon rahama tsira da aminci su kara tabbata gare shi da iyalansa ya ce:

: يقول الله عز وجل: إذا كان الغالب على العبد الاشتغال بي، جعلت بغيته ولذّته في ذكري، فإذا جعلتُ بغيته ولذّته في ذكري، عشقني وعشقته، فإذا عشقني وعشقته، رفعت الحجاب فيما بيني وبينه، وصيّرت ذلك تغالباً عليه، لا يسهو إذا سها النّاس، أولئك كلامهم كلام الأنبياء، أولئك الأبطال حقاً.

Mai girma da daukaka yana cewa: idan ya zama galibi ga bawana shi ne shagaltuwa tare da ni, zan sanya kololuwar abin da yake nema da jin dadinsa ya zama cikin ambatona, idan kololuwar bukatarsa da jin dadinsa suka zama cikin ambatona, sai ya zama ya kaunace ni nima na kaunace shi, idan ya kaunace ni na kaunace shi, zan yaye hijabi tsakani na da shi, in mayar she da hakan mafi galaba kansa, ba zai dinga mantuwa idan mutane suka manta. Wadancananka zancensu zancen annabawa ne, wadancananka su ne cikakkun jarumai.

Abin da ke cikin wadannan hadisai guda biyu ba boyayye bane daga shiryarwa madaukakiya da gwalagwalai suke fitowa daga cikinsu da zinariya ta alfahari daga ilimai da ma’arifofi, farinciki daga wanda ya kasance daga cikin cikakkun jarumai, ko kuma ya kasance kan hanyarsu zuwa ga jarumtaka ta gaskiya cikin tafiyarsa da sulukinsa da irfaninsa na muslunci lafiyayye .

Bawan Allah Adil-Alawi. 13 ga watan shawwal tsakankanin huda biyu
Tarihi: [2017/12/3]     Ziyara: [286]

Tura tambaya