mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

MENENE RA’AYINKU DANGANE DA MAUDU’IN ZIYARAR ASHURA DA DU’A’U TAWASSUL


Salamu Alaikum wa Rahmatullahi ta’ala wa barakatuhu
Mene ne ra’ayinku Akaramakallahu dangane da maudu’in ziyarar Ashura wacce ta mashhura da wacce ba mashhura ba da Du’a’u Tawwsul? Sakamakon kasantuwar a wannan zamanin shakku kan ingancin maudu’in tsinuwar da take ciki… Allah ya saka muku da alheri.

 

Salamu Alaikum wa Rahmatullahi ta’ala wa barakatuhu

Mene ne ra’ayinku Akaramakallahu dangane da maudu’in ziyarar Ashura wacce ta mashhura da wacce ba mashhura ba da Du’a’u Tawwsul? Sakamakon kasantuwar a wannan zamanin shakku kan ingancin maudu’in tsinuwar da take ciki… Allah ya saka muku da alheri.

 

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Wannan shakku da shubuhohi tun zamani da akwai su kuma ba su gushe bat un lokacin saukar Adamu da Shaidan lallai Shaidan yana wahayi ya zuwa mutanensa da wadannan shubuhohi bawai sababbi bane da kuma cewa sun samu yaduwa a wannan zamani ba, amma batun ziyarar Ashura zaka iya duba littafin da na rubuta wanda yake sharhi ne da ta’aliki ya kasance mujalladi hudu (Adwa’u fi Sharhi Ziyaratul Ashura) amma Du’a’u Tawwasul da wasunta to ya isar cikin riko da ita kasancewarta manyan malamai da masana hadisai sun nakalto ta kamar misalin Shaik Abbas Qummi (k.s) cikin littafinsa Mafatihul Jinan da sauran malamai masu tarin yawa, ka da ka ga za kunnuwa ka damu da shakku da wahaman kiyayya da jahilci da wauta da mulkin mallaka wanda yake nufin rarraba tsakaninmu domin samun damar mulkarmu saika ga suna wurgo misalin wadannan shubuhohi tsakankanin muminai domin raba kawukansu da shagaltar da su don samun mulkarsu cikin gidajensu, wajibi a farka farkawar muslunci mai girma da kare addini da Kura’ni da Sunnar Annabi tsarkakka da hanyar A’imma tsarkakakku amincin Allah ya kara tabbata a garesu.

Wurin Allah muke neman taimako.  

Tarihi: [2019/10/19]     Ziyara: [433]

Tura tambaya