mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Ina son shiga Hauza Ilimiyya bana son shiga Jami’a

Maudu’in shine na gayawa mahaifiyata cewa ina son karatu a Hauza ilimiyya bana son shiga Jami’a sai dai cewa ta ki amincewa ta ce mini idan kayi karatu a Hauza ka gama a ina zaka samu aikin yi?

Maudu’in shine na gayawa mahaifiyata cewa ina son karatu a Hauza ilimiyya bana son shiga Jami’a sai dai cewa ta ki amincewa ta ce mini idan kayi karatu a Hauza ka gama a ina zaka samu aikin yi?

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai

Da farko: ni abinda nayi Imani da shi shine cewa lallai farin cikin duniya da lahira na cikin Hauza Ilimiyya da saharadin tsoran Allah da kiyaye dokokinsa da tsarkake niyya cikin neman ilimi tareda yin aiki da shi.

Na biyu: kayi bakin kokarinka wajen fahimtar da mahaifiyarka girman ilimin lahira da fifikonsa kan ilimin duniya, lallai ita Jami’a cikinta akwai ilimin duniya amma ita Hauza itace take dauke da ilimin makomar kowa lahira.

Shi ilimin rayuwar duniya yana daga kasa shi ko na lahira yana daga sama, ina Surayyatu da Sara wato kasa, ina mulki da zahir daga duniyar Malakut da Gaibu, ai ina kwata-kwata babu hadi babu kiyasi tsakaninsu, shi ilimin duniya yana gushewa da mutuwa da gushewar ita duniyar, shi kuma ilimin lahira da makoma yana wanzuwa da wanzuwar Allah da sarmadiyyarsa matsarkaki ta’ala.

Na uku: yayin da mutum ya shiga Jami’a ya kammala zai fito ya samu aiki ya zama hadimin daula, amma lokacin da ya shiga Hauza zai kasance Hadimin Imam Zaman ya kuma kasance daga Sojojinsa.

Ina zaka hada Hadimin Daula da Hadimin Sahibuz Zaman (A.F) musammam idna daular ta kasance Azzaluma Fajira Kafira.

Na hudu: kamar yanda ya zo cikin ingantattun Hadisai kuma ni a kankin kaina na Jarraba shi lokuta da daman gaske lallai Allah yana dauke nauyin arzikin Dalibin ilimi da yake Hauza ilimiyya ko da farko zaka samu yana rayuwa cikin talauci da bakunta daga karshe zaka samu Allah ya buda masa kofofin arziki ko da kuwa ya kasnace yana gudun duniya yana wadatuwa da dan abinda yake wajibi.

Ya zo cikin hadisi mai daraja cewa: hakika mutane suna gudu bayan arzikinsu shi kuma Dalibi arzikin yake binsa a guje.

Na biyar: na rantse da ubangijin Ka’aba ina da sani da yakini cewa neman ilimi addini tareda sharadinsa wallahi wani dadina da ya shallake dukkanin dadin duniya da dukkanin kudi da dukiyar rayuwa da ayyukan hukuma wannan wani abune da na gwadashi da kaina a rayuwata cikin shekaruna, cikin ba’arin wasu lokuta akwai wasu maganganu kamar yanda Almuhakkikul Kurasani ya fada a lokacin farkon dare zuwa alfijir yana karatu ya rubuta yana jim wani irin dadi da farin ciki  ta yanda ta kai yana kanyi kururuwa ya daga murya yana mai cewa: ina Sarakuna da `ya`yan gidan Sarauta ina suke ina dadin da yake cikin ilimi cikin ma’anawiyya da ruhiyyarsa da Malakutiyya da lahira da zan gaya maka fa’idojin shiga Hauza da sai ta kaini da wallafa littafi, sai dai cewa zan wadatu dan wannan takaitaccen bayani, Allah ne mai bada kariya da cewa da taimako babu inda muke neman taufiki sai wurin Allah madaukaki mai girma      

 

Tarihi: [2021/1/24]     Ziyara: [305]

Tura tambaya