mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Shin wanin mu zai iya ce Allah ya gafarta min shiga wuta? - kamar a dare lailatul Qadr?

Assalamu alaikum
1. Kubuta daga shiga wuta
Fadin da ke cewa ku yi wa mutane magana bisa kimar hankalin su, ina neman bayanin ku kan wadanna tamaayoyi da nake dasu
-. Shin akwai wani ma’auni da mutum zai gane shi ba dan wuta bane?
-. Shin wanin mu zai iya ce Allah ya gafarta min shiga wuta? - kamar a dare lailatul Qadr?
-. kuma cewa mutum na da tabbacin ya kubuta daga wuta zai iya sako sako da ibadun shi na sauran abin da yarage na rayuwar sa?
-. ina neman a taimakamin da wasu rubuce rubuce kan wannan maudu’I na kubuta daga wuta da kuma hadisai na ahlul baiti da suke bayani akan hakan.
2. mun san cewa sakamako bawa bayan ya mutu shine ko Allah ya bashi ladane ko kuma ya azabtar dashi ko kuma Allah ya yafe ma sa sabida shi Allah gafurur Rahim ne, amma hakan bazai sa muyi dogaro da aiyukan mu na duniya ba
Amma tamabaya ta ta shafi wanda aka kasheshi bisa zalunci kamar a harin bom, wanda zaa iya kiranshi shahidi, muna tsammanin rahamar Allah da kuma karamcin sa zai shafe wannan bawansan kuma zai gafarta masa dukkanin zunubarsa da suka gabata.
To yadace muke ce dukkanin zunubansa Allah ya yafe masa, ko kuma muke ce da badin Allah ya yarda da shi ba da hakan bata faru da shi ba?

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Amsa na farko: me zunubi fursunan zunuban sa ne sannan kuma batinin duk wani zunubi wuta ne, wato me zunubi fursunan wuta ne don haka ya kamata mu lizimci kan mu da aiki na gari da zai ke kara mana Imani

Amsa na gaba: Eh taqawa taqawa taqawa

Amsan gaba: alama na tuba shine mutum bayan ya tuba kar ya sake komawa ruwa wato kar ya sake komawa zunuban da yakeyi kafin tubar sa idan kuwa ya kasance haka, ba shakka adduar’sa za ta karbu a daren lailatul qadr kuma zai sami kubuta daga shiga wuta.  

Amsa na gaba: hakane

Amsa na biyu: idan har ya kasance yana da wulayan ahlul baiti, ba shakka an masa alkawari da shiga aljannah kuma za’a gafarta masa dukkanin zunuban sa

Allah shine yasan abin da ya fi dacewa da duk wani bawan sa sannan shi yasan lokacin da yafi dacewa ya dauki ransa.

Tarihi: [2016/9/9]     Ziyara: [1095]

Tura tambaya