b Shin asasin ilimummukan shi’a an samo su ne daga Ahlus-sunna
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Shin asasin ilimummukan shi’a an samo su ne daga Ahlus-sunna

 


Akwai shubuha da take kai kawo da cewa wai asalin asasin dukkanin ilimummukan shi’a sun debo su ne wurin Ahlus-sunna wannan shine abinda tarihi da nassoshi suke shaida kansa daga dukkanin bangarorin biyu, idna hakan ya tabbata zai zama nakasa da tawaya da suka kan shi’a wadanda suke da’awar cewa sune mafi sanin ilimummukan muslunci daga tsakankanin musulmai.

 

Amsa:

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ka sani ilimummukan da suke yawo tsakanin Ahlus-sunna hakika an rubuta su ne tun farko-farkon muslunci bayan bayan karni na farko cikin hallarar Annabi (s.a.w) da halifofi hudu, amma ilimmukan shi’a an rubuta su cikin karni na biyu da na uku cikin karshen gaiba Sugra, cikin abind ayafi shahara bayan karni na farko zamanin gaiba kubra, a dabi’ance yake kuma a bayyane yake cewa malamai shi’a a wannan zamani sun rubuta litattafan su na manhaji da uslubin litattafan na nan na yawo kuma a hannun musulmai a wancan zamani, sai dai cewa hakan sam bai nuna nakasa ga shi’a idan muka kalli yanayin rayuwa a wancan zamani da duba kan dalilin da ya hana su rubuta litattafan Rijal da na hadisi dana fikhu da usul da abinda ya yayi kama da haka, basu fara rubuta sai bayan shekara 250 da hijira, hakan bai kasantu sai don sakamakon muhimman abubuwa guda biyu da ya zama dole mu waiwaye su:

Na farko: bisa zahirin mahangar Ahlus-sunna bayan zamanin Annabi (s.a.w) da bayan zamanin halifofi hudu shari’a da sanya hukunce-hukunce sun yanke kai hatta bayanin ayoyi da tafsiri, hakan ya tilasta su ya zuwa komawa ga wadancan hadisai a karni na farko, bayan komawa garesu sun suka larurantu ya zuwa ga dawwana ilimummuka daban-daban misalin ilimin Rijal da Hadisi da Diraya abinda yayi kama da haka sakamakon saukakar wannan komawa da ingancinta, amma shi’a fiye da shekaru biyu basu laruranta da ya zuwa misalsalan wadannan ilimummuka ba sakamakon suna Imani da Imami da imamanci da wajabcin komawa gareshi a zamanin sa ko kuma zuwa ga marawaicin hadisin sa  a zamanin, saboda haka ya zamanto basu dawwana litattafai ba cikin ilimummuka     da muka ambata sai bayan gaiba sugra da kubr, da dabi’ance yake a wannan zamani wajibi ga malamai shi’a su fara dawwana litattafai da kuma yi musu babuka babi-babi, bisa abinda ya zama al’ada da kuma yaduwa ga Ahlin wannan zamani shine tsari da uslubin litattafan Ahlus-sunna da suka a hannun mutane fiye da shekaru 200.

Na biyu: shi’a basu samu dama ba, hatta idan suka yi niyyar rubuta littafi daya a wannan zamani bai yiwu sakamakon tsananta musu da hukuma take, wannan ya sanya zaka ga  yawancin ilimin shi’a a wannan zamani ya yana cikin haddar a kwakwale da kuma `yan takardu wurin kebantattun shi’a, basu yadu ba tsakankanin amawan shi’a ballantana yakai ga yaduwa tsakankanin garuruwa da kasashen musulmi sakamakon tsananin tsoron azzaluman halifofin Umayyawa da Abbasiyawa, sai dai cewa a karshen gaiba sugra da farawar gaiba kubura, kofa ta bude ga shi’a sakamakon samuwar Alu Buwaihi wadanda suka kasance daga shi’a, sakamakon karfin da suke da shi kan Abbasiyawa, daga nan litattafan shi’a daban-daban suka fara bayyana da fantsama cikin baki dayan ilimummuka da fannoni, ta yanda a wannan zamani suke kece da shallake litattafan Ahlus-sunna wadanda yawanci suka ginu kan gurbatacciyar shimfida da mukaddima, kamar yanda yake ambace cikin litattafan tarihi, manya-mayan malaman Ahlus-sunna sun yi dalibta a hannun malaman shi’a, kamar misalin Shaik Kulaini da Shaik Saduk  da Shaik Dusi da Mufid. Hatta cikin wannan zamani zaka samu wannan fifiko yana nan cikin ilimummukan hankali dana nakali cikin godiyar Allah ta’ala.

Tura tambaya