lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)


An karbo daga Imam Rida (a.s)

عن الإمام الرضا(ع): من زارها عارفاً بحقّها فله الجنّة

Duk wanda ya ziyarce ta yana mai sanin hakkinta yanada aljanna

Sannan fadinsa (yana mai sanin hakkinta) abinda ake nufi da hakki shine tabbataccen abu, saboda haka hakkinta anan ana nufin abind aya tabbata gareta daga Allah matsarkaki daga manzonsa da iyalansa tsarkaka, ya zo cikin riwayoyi cikin ziyarar A’imma tsarkaka ya zo daga gare su cewa: dukkanin wanda ya ziyarci Imami yana mai sanin hakkinsa sannan daga cikin mafi girman hakkinsa shine imanida kasantuwar jagora da biyayyarsa take farilla daga Allah, amma batun hakkin Sayyada Ma’asuma to suna da tarin yawa sai dai kawai mu dan kawo abinda ya saukaka:

 

Kadai takai wannan madaukakin matsayi cikin gidaje da Allah yayi izini a daukaka- da wurin Allah da manzonsa da iyalansa tsarkaka sakamakon iliminta da saninta da tsarkakakkiyar bada kariya ga alfarmar wilaya, da kuma fana’i cikin Allah cikin mukamin imamanci da mafi girman halifanci  da misaltu a zamaninta cikin Imam Rida (a.s) lallai tana kamanceceniya da gwaggonta Sayyada Zainab (a.s) cikin ba dakariyarta kan motsin `dan’uwanta shugaban shahidai Husaini ibn Ali (a.s) kamar yanda take kamanceceniya da Fatima mahaifiyarta (a.s) cikin girmanta da tsarkakarta da kyawunta da kamalarta, me yafi kyawunta daga abinda Imam Komaini ( r) yake fadi cikin baitocin wakensa da harshen farinsanci cikin falalolinta da darajojinta, bara mu dan kawo tarjamarsa a takaice, yana cewa: hasken ubangiji yayi tajalli-Allah hasken sammai da kassai- cikin manzon mafi karamci-sannan daga gareshi yayi tajalli cikin sarkin muminai Haidar Karrar (a.s) sannan ya bayyana cikin Fatima Zahara, yanzu kuma yayi tajalli cikin diyar Musa bn Jafar Alkazim (a.s) kadia duniya ta kasantu ne albarkacin wannan haske, ba da ban shi ba da komai ya kasance wargi, wani zamani bait aba zuwa da kwatankwacin wannan mataye guda biyu ba-Fatima Zahara da Fatima ma’asuma (a.s) wadanda suka fito daga tsakankanin tarsashin kudurar Allah, Zahara ta kasance mabda’ain kumfar ilimi, sannan ita kuma diyar Musa (a.s) ta kasance masdarin da tushen hakuri da juriy, wancan ta kasance kambun sarauta kan kawunan annabawa-sai ita kuma wannan ta kasance kwalkwalin waliyyai sulkensu, wancan ta kasance ka’abar duniyar girmama, ita kuma wannan ta zamanto mash’arin mulkin sarkin girmama, ba da ban anyiwa bakina takunkumi ba da fadin Allah (bai Haifa ba) da nace…… iata Zahara’u sarauniya ce kan mulki azal, ita ko Ma’asuma sarauniya ce a kan karagar girmama, Zahara ta kayatar da kasar madina munawwara, ita ko Ma’asuma ta haskaka kasar Qum mai tsarki, ma’asuma ta sanya kasar Qum cikin daukakar aljann, ita ko Zahara ta sanya ruwan birnin Madina Kausara, sai kasar Qum taii gibdi kuma daga gareta aka sanya kofar aljanna.

 

Kadai ana sanin girman Sayyada Ma’asuma da daukakar matsayinta karkashin nassoshi da suka zo kan hakkinta daga Ma’asumai (a.s) kamar misalin fadin kakanta Sadik (a.s)      

 

الصادق(ع): «بضعة منّي من زارها وجبت له الجنّة»،

Tsokata dukkanin wanda ya ziyarceta aljanna ta wajaba kansa.

Da fadin babanta (as) raina fansarta, hakama fadin dan’uwanta Rida (as)

الرضا(ع): «من زارها كمن زارني»،

Duk wanda ya ziyarceta kamar misalin wanda ya ziyarceni.

 وقول ابن أخيها الجواد(ع): «من زار عمّتي وجبت له الجنّة».

Da fadin `dan `dan’uwanta Jawad (as) duk wanda ya ziyarci gwaggona aljanna ta wajaba kansa.

 

Dukkanin wadannan jumloli da misalsalansu sun zo ne suna bayanin kan Sayyada Ma’asuma

Tura tambaya