b SHAHARARRUN MALAMAN DUNIYAR MUSLUNCI
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

SHAHARARRUN MALAMAN DUNIYAR MUSLUNCI

Wayewa da cigaban muslunci, hakika wayewar muslunc cike take da haifar da nasarori cikin tsahon zamani, itace wayewar da ta kasance wayewa ta mutum ta habbaka da cika da cigaba daidai lokacin da duniyar turawa ke cikin duhun kai da jahilci, duhu da jahilci da talauci sune mafi bayyanar alama a cikin kasashen turawa, har yanzu galibin cigaba kirkire da nasarorin ilimi sun bubbugo daga malaman muslunci, ana karantar da nazariyoyinsu cikin jami’o’in kasashen turawa da na larabawa, ana la’akari da su matsayin masdarori da tushen ilimi mai muhimmancin gaske,  wayewar muslunci ta bada gudummawa cikin tarihin habbakar tunani da ilimi, tsahon tarihi wasu adadi daga malamai daga muslunci sun bayyana wadanda suka bada gudummawa cikin wayewar muslunci, sai ya zamanto iliminsu ya fantsama ya yadu cikin sassa daban-daban na duniya lamarin da ya kai ga yaduwar sunayensu da daukakarsu.

 

Mafi shahara daga cikinsu akwai:

 

Abubakar Razi: shine Muhammad bn Zakariya daya daga cikin malamai masana ilimin falsafa da suka shahara, ta yanda ya kaddamar gudummawa da nasarori muhimmai cikin ilimummuka musammam ma cikin fagen ilimi likitanci, ya rayu a zamani a lokaci mai tsayi a shekara 865 miladiya ya zuwa 923 miladiya, an haifeshi a garin Rayyu cikin kasar Iran, amma wafatinsa ya k, Razi ya koyar da ilimin likitanci a garin Bagadaza, ya himmatu da talifi kan ilimin likitanci wajen tsofaffin masana, ya kwadaitu kan fahimta da riskar abinda ya kunsa, bai takaitu iya haka ba, ya himmatu kan fuskantar matsalolin da suke kunshe ciki da warwaresu, kamar yanda ya kasance yana himmatuwa cikin sharhin ra’ayoyi masana likitanci cikin darasussukansa, sai kuma daga baya yayi tahlilinsu ya warware yayi sharhi.

 

Muhammad bn Musa Kawarzimi

Shine Muhammad bn Musa babban malami musulmi, ya shahara da iliminsa da saninsa da sanin sa kan ilimummuka daga nau’ukan ilimi, misalin ilimin falaki da Jabaru da ilimin lissafi, da injiniyanci, ana kirga Kawarzimi daga malaman da suka bada gudummawa cikin ilimin lissafi ta yanda ya nakalci ilimin sanin lambobi zuwa kasashen turai, sannan ana kirga shi malami na farko da ya bada gudummawa cikin ilimin Aljebra cikin kaziyoyi da wasiyyoyi da gado.

 

Farabi:

Shine Abu Nasar bn Muhammad, an haifeshi cikin kasar Kazakastan cikin garin Farab a shekara ta 872 miladiya ya shahara da lakabin mu’allimul sani cikin duniyar larabawa bayan babban masanin falsafa Arasto, Farabi ya nufi birnin Bagadaza domin koyon harshen larabci, ya wallafa wasu adadin talifai a zamansa a Bagadaza, daga nan ne kuma ya taso ya kewaya adadin wasu wurare misalin Harran da ke kasar Siriya, da kuma yaje kasar Masar da birnin Damaskus, ya bar babbar taska daga binciken sa a fannin falsafa, ana kirga shi babban uba ga Afladinawan muslunci na wannan zamani, kamar yanda ya wallafa littafi da sunan Almadinatul Fadilatu, ana kiyasta shi da littafin Jamhuriyatul Afladon Alfadilatu.

 

Ibn Sina:

Abu Ali Husain ibn Sina ya kasance daga fitattun malaman muslunci da suka samu shahara, ya shahara sakamakon fifitarsa cikin ilimin falsafa da likitanci, nasabarta taba tukewa zuw aga kasar Uzbekistan, an haife shi a tsohon garin Bukara a shekara ta 980 ya bar duniya 1037 miladi, ana yi masa lakabi da Shaikul Ra’is, turawan yamma na kiransa da baban likitanci sarkin ga likitoci, Ibn Sina ya bada gudummawa cikin talifi litattafai kusan 200 cikin maudu’ai daban-daban musammam fagen likitanci da falsafa, mafi shaharar littafinsa shine littafin (Alkanun fi Dibbi)

 

Alkandi

Shine Abu Yusuf Yakubu Kahdani, nasabarsa tana komawa zuw aga dagatan KIndatu, babu dandakakkken bayani kan tarihin haihuwarsa da wafatinsa, na haife shi an garin Kufa yayi wafati a birnin Bagadaza, ana tsammanin ya rayu a tsakankanin shekara 801 zuwa 837, ana kirsga shi daga malamai musulmai da suka shahara, ya himmatu cikin ilimummuka daban-daban misalin ilimin Jogirafi (geography) da mandik (logic) da Ilimin kimiyya da likitanci da falsafa, ana kirga shi matsayin farkon wand aya fara samar da tsarin bahasin ilimi ta hanyar amfani da istidlali da mukaddima da dogara kan ra’ayinsa da cewa ilimi yana matsayin abu guda, daga haka yana iya haifar da ilimummuka daban-daban sashensu tareda sashe.

 

Ibn Nafis

Shine Abu Hassan bn Abu Hazam wanda aka fi sani da Ibn Nafis, babban malami, an haife shi a shekara 121o ya bar duniya a1288 miladi, ana kiransa da bakuraishe sakamakon danganewar nasabarsa ga kuraishawa da suke zaune kusa da garin Damaskus, Ibn Nafis yana daga cikin muhimman likitoci da masana, ta yanda ya kaddamar wani adadin talifai cikin ilimin likitanci da falsafa da luggan haka zalika ya lamintar da muhimmai malamai wadanda suka karanta ilimin fiziyolaji.

 

Ibn Rushdi

Shine Muhammad bn Ahmad bn Rushdi ana yi masa kinaya da Abu Walid shi babban malami ne, ya rayu a shekara 1126 miladiya ya zuwa 1198, nasabarsa ta na karkarewa ua zuwa garin Kurdabatu, ya himmatu da karatun falsafa da likitanci da lissafi da Usul da fikihu, sannan ya kasance Alkali sahon shekaru a birnin Ishbiliya, daga nan ne kuma Allah ya karbi ransa a garin Kurdabatu, ya shahara da kasantuwarsa mafi ilimin likitanci a zamaninsa, ya fifitu da kudurarsa kan tasnifi da kaifin basira da sanin ma’ani sauran abubuwa.

Tura tambaya