lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Siyasar muslunci

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Siyasar muslunci zama 

Idan ka zama shugaba ko ka zama shugaban wani ofis ko wata ma'aikata ta gwamnati ko mai zaman kanta ko makaranta kai ko malami ka zama koma me ye, farkon abinda zamu tambayeka shine ina tsarinka idan baka da tsari to baka cancanci zama kan wannan matsayi ba kawai ka ja gefe ka koma gefe, bai kamata ba wanda bai da hankali ace shine ya zama shugaban mutane, ina gaya muku duk wata al'umma da suke a duniya ko su waye addini abind asuke da'awa ko kiran addini ko ba addini suke kira ba, da zara ka je wajensu tambaye su ina tsarinku, idan suka ce maka basu da wani tsari rubutacce da suka rubuta ce musu mahaukata ko su waye, da tsari ne mutum yake iya sanin ma'auninsa da  iya hadafin da aka cimma na wannan tsarin, an cimma hadafi ko ba a cimmasa ba, don haka idan kana neman shugaban kasa ko gwamna koma mene ne a atakin farko dole ne tsarinka ya kasance yana hannunka kuma ka auna ayyukanka da ayyukan mabiyanka kan wanna tsarin ka cimma hadafi ko baka cimmasa ba, bana mantawa akwai wani wawa da aka taba tambaya shin mene ne tsarinbka me ye kundin tsarinku sai yace kur'ani saboda tsananin jahilci, na'am kur'ani littafi ne mai tsarki littafi ne da aka saukar domin hidayar duniya baki daya dole da bukatar kasancewa ace al'ummarka tana wasu alakoki sannan kur'anin ne yace ku kasance kunada tsari, riwayoyin da manzon Allah (s.a.w) da hadisansa sune sukai umarni da cewa ka kasance kanada tsari hatta manzon Allah da ka saukarwa da kur'ani yanada kuma wani kundin tsarinsa a gefe na dokoki tsakaninsu d asauran mutane wanda suka tsara su wanda wadannan dokoki na hankali basa sabawa shari'a, amma shi wawan naka kawai sai yace kur'ani shikenan ba matsala yanzu nuna mana a kur'ani matsayinka nuna mana matsayin mabiyanka nuna matsayin shugabanni kungiyarka da bangarorinsu nuna mana ayyukansu a cikin kur'ani nuna mana haddodin da akai iyaka na ayyukansu da idan wani ya saba me za ai masa nuna mana alakokinku da sauran kasahse ko sauran kungiyoyi a cikin wannan nuna mana nuna mana?!

Saboda haka wannan sakarci da shashanci da yawa yake, manzon Allah (s.a.w) duk da cewa yana da kur'ani amma kuma yanada mu'hadat da mukarrarat da ya dawwana ya rubuta tsakaninsa da sauran dauloli da kuma mutane.

Tura tambaya