lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Taskar Adduoi 2


Da sunan Allah me rahama me jin kai

Ina farin cikin sake kawo muku kashi na biyu daga cikin adduoi dan biyan bukatu da wasu sauran matsaloli,Kaman yadda na kawo a kashi na farko da ya gabata waddanan adduoi na jaraba su kuma naga tasirin su a cikin rayuwa na,ya zo a cikin hadisai cewa duk wanda yayi niyar addua toh yayi imani da shi kuma ya kore dukkanin wani shakka daga zuciyar sa dan shakka yana hana amsa addua.

Ga wasu addua domin kara karfin kwakwalwa da kuma maganin mantuwa mussaman ga tsofi da wadanda suke da matsala na mantuwa.

1-Duk wanda ya karanta dukkan sunan Allah da ke dauke da harafin (MIMUN) kaman Arrahma da Arrahim sau 90 zai sammu karin farfin kwakwalwa ,idan ya ci gaba da yin haka kuwa na tsahon shekaru to haka karfin kwakwalwar sa zai ci gaba da karuwa.

2-mutum zai yi alola sai ya rubuta aytul kursiyu da ma’u wardi da zafaran a tafin hanun san na dama sannan sai ya lashe da harshen sa,zai yi haka har sau 7. Yin hakan yana kara karfin kwakwalwa.

3-duk wanda ya rubuta wannan adua da ma’u wardi ya wanke ya sha kafin ya karya kumallo zai iya haddace duk wani abun da yake so da izinin Allah.ga adduan Kaman haka

)بسم الله نوّر بكتابك قلبي وإشرح به صدري وأطلق به لساني بحولك وقوتك لا حول ولا قوة إلّا بالله العلي العظيم) 

4-karanta wannan addua kafin a fara karatu yana temakawa wurin kara karfin hadda

)اللّهم أُرزقني فهم النبيين وحفظ المرسلين وإلهام الملائكة المقربين آمين يا رب العالمين(

5-yazo a cikin mafatihul jinan a bangaren adduoin da ake yi bayan ko wani sallah shima yana tasiri wurin karfin kwakwal da karfin hadda

)_سبحان من لا يعتدي على أهل مملكته، سبحان من لا يأخذ أهل الأرض بألوان العذاب، سبحان الرؤوف الرّحيم، اللّهم إجعل لي في قلبي نوراً وبَصَراً وفَهمَاً وعلماً إنّك على كل شيء قدير(

Muna baran addua wurin yan uwa

 

Tura tambaya