lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mai lamintar da Barewa

 

Inama na kasance xan Barewa

In yi ta tsalle ina gudu dare da rana kan dandarya qasan dutse  da kan dutse da kan sahara da dandaryar qasa dare da rana

In yi ta gudu yau she ne zan ganka inama wata rana zaka zauna kusa da ni ka sanya hannunka ka shafa kaina.

Inama ka kasance abokina da murmushinka.

Da ni da `yar'uwata.

Saboda mahaifiyata ta gaya mini cewa haqiqa kai a wani zamani a wata rana ka kasance masoyin wata qaramar `yar Barewa.

Farin ciki da halin wannan `yar Barewa da kai kasance mai lamininta.

Saboda haka ka zo ni zan zama `yar qaramar `yar Barewa, `yar Barewar da ita kaxai da wanzu.

`yar Barewar da ta wanzu baquwa tsakanin dandaryar qasan dutse da sahara.

Tura tambaya