sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- » Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Ummul Masa’ib Haura’u Zainab diyar sarkin muminai Ali bn Abu dalib (as)
- » Shawarwarin Ayatollah samahatus sayyid Adil-alawi kan ilimin sanin halayyar dan adam
- » falsafar humanism (mutumtaka) ka'ida ce ta mazhabar Almaniyanci
- » Imam Aliyul Hadi (as) a cikin tsakiyar Zakuna
- » Wasikar Najashi
- » JIFAN JAMARAT
- » SAUTIN KIRAN HANKALI-TARE DA AYATULLAH ASSAYID ALI-ALAWI
- Tarihi » Al'ummar Jahiliya gabanin aiko da Annabtar cikamaki
- » GISHIRI CIKIN TAFIN HANNU
- » Darussan hauza> bahasul karijul fikihu 22 ga rabi'u Awwal shekara ta 1439 hijri- zartar da istis'habi da hujjiyarsa cikin shakka sa'ilin shafe shari'ar data gabata da mai riskuwa (38) Birnin Qum mai tsarki- tare da samahatu AyatollahAssayid Adil-Alawi
- » Taskar Adduoi 2
- Fikhu » KARIJUL FIKHU 5 RABIU SANI 1441 CIKIN TA’ARIFIN IJTIHADI A ISDILAHI DA NAKADI A KAN TA’ARIFOFIN DA AKA AMBATA
- » dayanta Allah a cikin ibada
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » taklidi shine riko da ra’ayin wani domin aiki da shi a far’aiyyat ko kuma lazimtarsa cikin akidu
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
Wahabiyawa a wannan zamani a garuruwan Hijaz cikin Harami biyu masu daraja a garin Makka da Madina sun kasance kamar Umayyawa da Abbasiyawa cikin barnar dukiya da almubazzaranci a daidai lokacin da sauran musulmi da suke kewaye da kasarsu ke cikin matsananciyar yunwa da rashin cikakkun kayan sawa a jiki, lallai Wahabiyawa sun hada kai tare da `yan jari hujjar yammacin duniya cikin tsotse alherai da mabubbugar arziki, sun mamaye fetur da kuma danne raunanan mutane da amfani da karfinsu cikin bukatunsu da danne musu `yanci da shake Dimokradiyya da ruhin mutuntaka da adalci da zamantakewa, da kuma kashe musulmi da kai musu farmaki.
Hakika dukkanin wanda ya samu tsinkaye kan ingantattun litattafai a wurin dukkanin Bawahabiye ba zai yi shakku da kokwanto ba da cewa kololuwar hadafinsu shi ne hallakar baki dayan musulmi-ko kuma mu ce ganin bayan wadanda suka samu dama a kansu ba tare da banbance `dan shi'a da sunna ba, lallai babu abin da yake kosar da `kishinsu sai wannan siyasar ta su ta rashin imani da tausayi, babu abin da ya hana su zartar da wannan siyasa da kuduri face karfin musulmi daga gabas da yamma, da kuma motsawar gwagwarmaya don yakar zalunci da nuna fin karfi anan da can, da kuma imanin mutane kan `yancin addini da bayyana ra'ayi da dukkanin uslubin da ma'abocin addini yake son yi.[1]
Akidar Wahabiyawa (ko dai ayi wahabiyanci ko kuma a fuskanci kaifin Takobi) lallai ka'idarsu ta farko wacce basa karkace mata shi ne dukkanin Makiyinsu Mushriki ne ko da kuwa ya furta kalmar tauhidi ya yi azumi ya yi sallah, Mushriki a wajensu kashi biyu ne: Mushriki wanda baya furta Kalmar tauhidi baya azumi baya sallah, sai kuma Mushriki wanda yake furta Kalmar tauhidi (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Muhammad Manzonsa ne) yana sallah yana azumi sai dai cewa kuma tare da haka yana sunbatar kabari wannan mutumi Mushriki ne a wajensu wajibi a kashe shi a yake shi, tana ma iya yiwuwa a wurin ba'arin wasunsu ya zama mafi hatsari daga tsantsar Mushrikai da basu furta Kalmar tauhidi ba.
Hakika dukkanin musulmi sun kyamaci wahabiyanci tun farkon samuwarsa, Shaik Abu Zahara [2] ya na cewa: akasarin musulmi suna kyamatar wahabiyanci da mafi tsananin kyama.
Amma hukunta su da cewa daga Kawarijawa suka fito a wannan zamani namu zan wadatu da Ambato maganganu biyu ta farko magana ce daga daya daga Malaman sunna ta biyun kuma daga shahararren malamin shi'a.
Babban malami Allama Shaik Muhammad
Amin bn Umar wanda akafi sani da bn Abidin[3] cikin
ma'anar Kawarijawa yana cewa:(( suna kafirta Sahabban Annabinmu) na san cewa
wannan ba sharadi bane cikin abin da ake kira da Kawarijawa, bari dai shi Kawarijanci
bayani ne ga wanda ya yi tawaye ga Sayyidina Ali Allah ya kara masa yarda, bada
ban hakan ba da ya wadatar cikinsu imaninsu kan kafircin dukkanin wanda suka
yiwa tawaye, kamar yanda ya faru a zamani da muke ciki cikin mabiyan Muhammad bn
Abdul-Wahab wadanda suka yi tawaye suka fito na fito da shugabanninsu na
lokacin a garin Najadu suka yi galaba a Harami biyu masu daraja suka kwace su,
hakika sun kasance daga mabiya mazhabar Ahmad bn Hanbal, sai dai cewa imaninsu
kan cewa su kadai ne musulmai kuma duk wanda ya sabawa akidarsu Mushriki ne,
kuma sun halasta kashe dukkanin Ahlus-sunna da wannan imani na su da ma kashe
malamansu sunna da suka saba musu, har zuwa lokacin da Allah zai karya karfinsu
ya rusa garuruwansu ya baiwa musulmi nasara a kansu da sojoji a shekara ta
3230, maganarsa ta zo karshe.
wannan shaida ce daga Malamin wannan zamani kan
fitinar wahabiyanci wacce ta bayyana karara tana bayyanar da hakikaninsu da
cewa sun fice daga addini sun fita daga lafiyayyar da'ira, suna ganin cewa su
kadai ne musulmi sauran dukkanin musulmai Mushrikai ne kamar dai yanda
Kawarijawa suke imani a farkon muslunci.
Allama Shaik Muhammad Jawad Mugniya ya ce: Kawarijawa sun fi kowa cikin musulmi yawan ibada da kiyaye sallah har sai suka shahara da sunan ma'abota bakaken goshi sabida yawan sallah da sujjada goshinsu sai da ya yi tambari da bakir kirin, amma kuma tare da haka sun kasance basa taka tsantsan cikin zubar da jinane da kwace dukiya da lalalata tsaro da zaman lafiya…. Wata rana Sahabin Manzon Allah Ibadatu bn Karzu ya ji sautin kiran sallah sai ya nufe shi domin yin sallah sai kwatsam ya tsinci kansa cikin Kawarijawa, sai suka ce masa: menene ya kawo ka nan ya kai Makiyin Allah? Sai ya ce: ku `yan'uwana ne, sau suka ce: a'a kai `dan'uwan Shaidan ne, lallai zamu kasheka, sai ya ce: yanzu ba zaku yarda daga gareni da abin da Manzon Allah ya yarda da shi daga gareni ba? Sai suka ce: wanne abu ne Manzon Allah ya yarda da shi daga gareka? Sai ya ce: naje wajensa lokacin ina Kafiri sai na karanta Kalmar shahada (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Muhammad Manzonsa ne) sai ya kyaleni, amma tare da haka basu kyaleshi ba sai suka kama shi suka kashe shi.
Kawarijawa sun taba datsewa sannan Malamin muslunci Wasil bn Ada'u hanya a lokacin yana tare da abokan tafiyarsa, yayin da suka yi yunkuri kashe su ba don komai sai don suna musulmi sai Wasil ya ce musu: mu Mushrikai ne wadanda cikinsu Allah ya ce (idan wani daga Mushrikai ya nemi makwabtaka dakai ka bashi makwabtaka) sai suka samu tsira daga hannunsu, sai dai cewa hakan ta faru ne bayan sun yi ikirari cewa su Mushrikai ne, da ace sun cewa Kawarijawa mu Musulmi ne `yan'uwanku da tabbas tuni sun kashe su kamar yanda suka kashe Sahabi Katada.
Wahabiyawa basu da banbanci da Kawarijawa a wannan fagen cikin wannan tunani na ukuba da rashin imani, hakane, hakika Wahabiyawa basa kafirta ba'arin Sahabbbai da halasta jinanensu kamar yanda Kawarijawa suka kasance, koma dai yaya ta kasance, lallai muslunci kuntatacce ne a fahimtar Wahabiyawa, musammam ma cikin abin da ya ta'allaka da tauhidi, lallai suna fassara tauhidi da kuntataccen tafsiri, baya dabbakuwa kan kowa sai iya kansu, ta yanda suke alakanta shi da ruguje Kaburbura da gine-ginen da suke kansu daga Masallatai kai hatta Kabarin Annabi, da haramta sallah da addu'a a wuraren, suna haramta ziyartar Kabarin Annabi da daukar hoto da makamancin haka, amma sanya suttura da labulaye kan Rauda Kabarinsa mai tsarki da fadin Musulmi ya sayyidina Muhammad da ya Muhammad duka wannan a wajensu bidi'a ce da halaka da bata
Wannan shi ne muslunci a fahimtarsu, amma raya kasa da gyara raunana cikinta da kokari cikin samar da saukin rayuwa da kayan more rayuwa domin kubuta daga rauni da kufaifayinsa da taimakekeniya cikin samun da tsanukan rayuwa da wadata ga dukkanin mutane, da kuma nesanta daga sabubban kiyayyya da gaba dukkanin wadannan suna daga abubuwa na mataki na biyu wani abu mai bijira a wurinsu.
Babu shakka cewa muslunci da ya takaitu cikin fahimta da tunanin Wahabiyawa da babu inda zai je k otaku daya ba zai yi zuwa gaba ba, Sakamakon Musulmai suna da wannan shahararren tarihi mai hatsarin gaske da ya turbude hancin Makiya barai na nesa ya tilasta su ikirari da cewa sakon Muhammad bn Abdullah (S.AW) shi ne tushen wayewa da cigaba, hakika ya farkar da baki dayan duniya kan madaukakan misalai sababbi, ya yaki miyagun al'adu, yayi imani da cewa bai halasta mutum ya kasance kayan aiki da tsanin samun farin cikin wani mutum daban da zai yi amfani da shi don cimma hakan, sai cikin Saudiyya zaka ga masu mulkinta a rayuwa cikin manyan fadoji da gine-gine da aka assasu ka rashin mutunci da jahilci da tabara.[4]
Wannan shi ne hakikar wahabiyanci!!
Allah ya tsaremu daga sharrinsu da fitinarsu.Daga cikin tambayoyin wanna sashin ()
- Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- Bahasul karijul fikhu 25 ga sha’aban zaman a 108
- Taskar Adduoi 1
- DAGA CIKIN SIRRIKAN TARON MINA
- Siyasar muslunci zama na Arba’in
- SIRRIKAN ARAFAT
- ME YASA YAN SHIA SUKE KIRAN SUNAN YAYAN SU DA ABDU ALI KO ABDU ZAHRA……..?
- KARIJUL FIKHU 15 GA SAFAR SHEKARA 1441 CIGABAN BAHASIN BAYYANA KARATU DA BOYE SHI
- Kowacce rana ashura ce kowacce kasa ma karbala ce