lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

KARIJUL FIKHU 17 MUHARRAM 1441 H CIGABAN BAHASIN UDULI DAGA SURA ZUWA WATA SURAR

Wuri: birnin Qum mai tsarki cibiyar Muntada Jabalul Amil Islami tareda_ Samahatus Assayid Adil-Alawi (H)

Lokaci: karfe 8 na safe, Fikhu 4.

Bahasinmu zai dora kan inda muka tsaya cikin mas’alar cuduli daga sura zuwa wata surar maganarmu ta kasance cikin mukamai a yanzu muna mukami na hudu cigaban kan mukami na uku da ya gabata wanda natijarsa ta kasance kamar haka: ba ya halasta ayi uduli mudlakan daga suratul Iklas da Fatiha zuwa wasu surorin, face dai abinda aka togace daga ciki da dalili, wannan shine bayaninsa cikin mukami na hudu  cikin maganar Almuhakkikul Hilli (K) : (na’am ya halasta ayi uduli daga garesu zuwa suratul Juma’atu da Munafikun iaya cikin Juma’a sakamakon kasancewa mustahabbi ko kuma cikin Azuhur din ranar Juma’a koi ta kanta Juma’ar a rakar farko ya karanta suratul Juma’a ta biyu ya karanta Munafikun, idan ya mance ya karanta wata surar daban ko da kuwa Fatiha da Iklas to a wannan fuska ya halasta ya yi uduli zuwa garesu matuakar dai bai kai ga rabin surar ba.

Ina cewa Mashhur da Almuhakkikul Hilli sun tafi kan halascin yin uduli daga Fatiha da Iklas zuwa suratul Juma’a da Munafikun a iya sallar Juma’a a jumlace saboda banbanci tsakanin karanta suratu Iklas cikin mantuwa ko ganganci, kuma muma wannan shine ra’ayin da muka zaba, abinda mashhur sukayi ittifakin kansa cikin kasancewa da zai karanta cikin rafkanwa a iya Iklas sannan jumlar nassoshi suna shiryarwa zuwa gareshi daga cikinsu akwai:

 

صحيحة محمد بن مسلم عن أحدهما عليهما السلام: في الرّجل يريد أن يقرء سورة الجمعة في الجمعة، فيقرء قل هو الله أحد؟ قال عليه السلام: يرجع إلى سورة الجمعة

Ingantacciyar riwayar Muhammad Ibn Muslim daga daya daga cikinsu (a.s) dangane da mutumin da yake son karanta suratul Juma’a sai ya manta ya karanta suratul Iklas? Sai Imam (a.s) yace: ya janye ya koma karatun Juma’a.

وصحيحة الحلبي عن أبي عبد الله عليه السلام: إذا إفتتحت صلاتك بقل هو الله أحد وأنت تريد أن تقرء بغيرها فامض فيما ولا ترجع إلّا أن تكون في يوم الجمعة، فإنّك ترجع إلى الجمعة والمنافقين منها[2].

Ingantacciyar riwayar Alhalabi daga Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gareshi: idna ka fara sallarka da karatun suratul Iklas alhali kayi niyyar wata surar ba ita ba to ka cigaba kanta ka da ka janye sai dai idna ya kasance cikin sallar Juma’a, lallai zaka janye daga gareta ka koma zuwa ga karanta suratul Juma’atu da Munafikun.

Makamancin wadannan riwayoyi akwai riwayar Ubaidu Ibn Zurara kamar yanda ya gabata da waninsu.

Abinda Assayidul Murtada Alamul Huda ya tafi kansa cikin littafin Al’intisar da Ibn Idris (K) cikin Assara’ir kan hana yin uduli mudlakan bisa riko da idlakokin umum raunannar Magana ce.

Sai dai cewa abu guda ya rage hakika muhallin nassoshin kadai ya kasance cikin halin mantuwa cikin karatun suratul Iklas ba tareda ishara zuwa ga suratul Hamdu ba, riskar da ita zai kasance cikin fuska biyu: ta farko: rashin faifaicewa, lallai zai lai zai lazimta keta ijma’i gud abiyu da kuma sabawa maganar Imam (a.s)  cikin kaddara kasancewa tareda dayarsu, babu banbanci tsakaninsu cikin halasci da hani idna ya kasance yana hanawa cikin Iklas to haka zai kasance cikin Fatiha sakamakon ijma’i da nassoshi idna kuma ya halasta ayi uduli cikin Iklas cikin wuraren da aka ambata  to haka zalika ya halasta cikin Fatiha, idan kuma nassi bai gangaro ciki sakamakon rashin zabar cikin faifaicewa, wannan shine ra’ayin da Assayidul Hakim ya zaba cikin Mustamsak dinsa juz 6 sh 190 sai dai kuma Assayidul Ku’I (K) cikin sharhin Urwatul Wuska juz 14 sh 355 yana ganin yankewa da shi cikin shakalin farko shine kafa hujja da fuska ta biyu riko da riwayar Aliyu Ibn Jafar.

Fuska ta biyu: da idlakin da ya zo cikin Sahihatu Aliyu Ibn Jafar daga dan’uwansa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi

 قال: سألته عن القراءة في الجمعة بما يقرأ؟ قال: سورة الجمعة، وإذا جاءك المنافقون، وان أخذت في غيرها وإن كان قل هو الله أحد فاقطعها من أوّلها وارجع إليها[3].

Yace: na tambaye shi dangane da karatun sallar juma’a? sai yace: ka karanta suratul juma’a da suratul munafikun, idan kuma ka karanta wasu surorin idan sun kasance daga suratul Iklasi to ka yanke daga farkonta ko koma kan suratul juma’a ko munafikun.

Fuskar kafa hujja: cikin isnadi babu riwayar bata da matsala sakamakon Aliyu Ibn Jafar ne ya rawaice ta cikin littafinsa, duk da cewa Allama Hurrul Amli ya rawaito riwayar da ta hannun Kurbul Isnad cikin raunannen isnadi sakamakon samun Abdullahi Ibn Hassan cikin isnadinta sai dai kuma a riwayar Allama Yusuful Baharani daga littafin Aliyu Ibn Jafar isnadin lafiyayye ne.

Amma daga fuskar abinda take shiryarwa to da farko: akwai cin karo da juna tsakanin idlaki kna hana yin uduli daga surorin biyu zuwa wasunsu bisa dogaro da idlakin riwayar Aliyu Ibn Jafar (a.s) lallai zai yanke abinda yake karantawa koma bayan suratul juma’a da munafikun mudlakan ko da kuwa suratul Iklasi ce ko fatiha ko kuma wasunsu, da kuma tsakanin idlaki biyu cikin mukamin cin karo da juna da yake kasance daga nisba umumu wal kusus min wajhin, kadai dai karon ya kasance cikin muhallin haduwar suratul Iklasi da fatiha idlakin farko yana cewa bai halasta ba ayi uduli hatta cikin suratul juma’a da munafikun sai dai cewa shi ya kebantu ne da iya ranar juma’a, sannan idlaki na biyu yana cewa ya halasta ayi uduli a kowacce sur ace hatta cikin Iklasi da fatiha, idan sukai karo da juna cikin karatu fatiha da suratul juma’a sai su fadi su biyun, sai ya koma ko dai zuwa ga asali ko kuma istis’hab takyir sai ya zama kana da zabi cikin yankewa ko cigaba cikin karanta fatiha a ranar juma’a m ko kuma komawa zuwa ga umumi da ya gabata a sama shine halascin uduli matukar dai bai kai ga karanta rabin fatiha ba kamar sauran surorin  ko kuma dai ya komo zuwa ga asali da ka’idar farko da take hukunci da halasci.

Na biyu: zamu iy kafa hujja da kiyasul Aulawi: bayani daga fuskar idlakin hadisin Aliyu Ibn Jafar (a.s) da bayyanar da gamewa dukkanin surori wanda daga cikinsu akwai fatiha, hakan ya tabbatu ne ta fuskar taksis kebantar da ambaton suratul Iklasi cikin fadinsa amincin Allha ya tabbata a gareshi (idan suratul Iklas ce to kana iya yankewa daga gareta) da ma’anar ko da kuwa sura da kake karantawa ta kasance kulhuwallahu ce ka yanketa daga babin idrajul fardul kafiyyi fil hukmi wanda shine yankewa da kasance itace karshen fardi da za a karkare zuwa gareshi cikin yankewa, wannan na bayyanar da cewa suratul tauhid itace mafi girmama daga waninta cikin hukuncin uduli, sabida ita tafi cancanta ace an kammala karatunta daga waninta, idan har ya halasta ayi uduli daga gareta zuwa suratul juma’a da munafikun a ranar juma’a to tabbas yafi cancantuwa ya halasta cikin sauran surorin da ba it aba, ka lura, lallai cikin wannan bayani akiwa kamshin kiyasi gurbatacce.

Wani bayanin:

Yayin cin karo da juna da riko da mafi rinjaye bisa la’akari da Akbarul Ilajiya  da umumul murajjihat babu banbanci cikin kasantuwarsa ambatonsa cikin hadisai ko akasi, lallai idlakin hadisin Aliyu Ibn Jafar (a.s) yafi karfafa daga idlakin da yake kore halascin uduli, hakan ya tabbatu sakamakon shaida da karina cikin fadinsa (a.s) : (idan surar ta kasance kulhuwallahu) zahirin shine kasantuwar suratul tauhid mafi cancantuwa da kammala karatunta daga waninta, idan ya halasta ayi uduli daga gareta to ya zai zama yafi halasta ayi cikin sauran surorin, ka lura.

Mukami na biyar: kadai uduli ya halasta daga suratul tauhid zuwa suratul juma’atu da minafukun a ranar juma’a kamar yanda hakan ya kasance daga abinda aka hakaito daga Alfakihu da Annihayatu  da Almabsud da Assara’ir lallai haka ya bayyanu ne cikin Azuhur din ranar juma’a, tambaya anan shine shin ya kebantu da sallar juma’a kamar yanda Allama Yusuful Baharani ya zaba cikin Alhada’ik juz 8 sh ko kuma ya fadada daga juma’a da Azuhur kamar yanda ra’ayin mash’hur ya tafi a kai da ma’anar Azuhur da juma’a, sannan daga Attazkiratu  da Jami’ul Makasid da zahirin abinda ya zo daga mujaz da Arrauda cewa bayanin ya kasance ne kan Azuhur da La’asar, wannan shine abinda idlakin da ya zo cikin Sahihatu Alhalabi yake hukuntawa daga fadinsa (a.s) : (cikin ranar juma’a).

Amma batun cewa ta hado da sallar Asubahi lallai ba fagen riko da wannan fuska sakamakon rashin shigar da suratul juma’a da munafikun cikinta, kadai surorin juma’atu da munafikun suna zama mustahabbi ne a iya Azuhur da la’asar da juma’a.

Wannan mas’ala mas’ala ce da ra’ayoyin suka sassaba cikinta

Zamu cigaba da yardar Allah ta’ala.


[1] الوسائل: باب 19 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الأوّل.

[2] الوسائل: باب 19 من أبواب القراءة في الصلاة الحديث الثاني.

 

Tura tambaya