lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi

 

 

Mas’ala ta 9: Magana mafi karfi hade suratu Filu da Li’ilafi sannan a hade suratu Adduha da Alam Nashraha, bai isar a karanta daya daga cikin su face sai a hade su tare da karanta basmala tsakanin su.


ina cewa: Akaramakallahu da farko ya tafi kan Magana mafi karfi kuma ita koma bayan fatawa ne, sannan karo na biyu: kamar yanda yake nunawa ita mas’alar akwai sabanin malamai cikin ta a jumlace, mash’huri ko kum tama iya kasancewa mafi shahara sun tafi kan hade suratu Filu da Li’ilafi haka hade Adduha da Alam Nashraha, wajabcin hada su a cikin sallah da ma’anar cewa wanda ya nufi karanta daya daga cikin su cikin sallar sa babu banbanci cikin raka’ar farko ko ta biyu ayyananniya da ya kalle ta tare da yar’uwar ta, kada ya wadatu ya isu da daya daga cikin su bayan ya gama karanta Fatiha face dai ya hada su biyun tare da juna kamar matsayin sura guda daya, haka kuma dole ne hadewa ya zama a jerance yadda akai bayani, da farko ya karanta suratu Fili sannan ya karanta Li’ilafi ta yanda basamalar Li’ilafi zata kasance tsakiyar su.

 

Anan akwai da’awa uku, ta farko: hade surori biyu da wajabcin karanta su tare da juna matsayin sura guda daya ba matsayin surori biyu masu banbanci da juna ba, na biyu: zai jeranta tsakanin su kamar yand aya zo a matani, na uku: tare da karanta basmala tsakanin su.

 Fuskar dalili a ta farko: shi ne ijma’i mudda’I da ijma’i madaraki kamar yanda yake a zahiri, hakika Assayid Murtada Alamul huda (ks) cikin littafin sa Al’intisar ya danganta hakan ya zuwa ga iyalan gidan Muhammad (as)[1]

 An karbo daga Saduk: (sh:740) ya danganta ikirari da hakan da cewa addinin Imamiyya n, daga littafin Assara’u da Attahrir da Nihayatul Ahkam da Tazkira da Almuhazzabul bari’u da wasun su da cewa hakan maganar da malaman mu suka tafi akai ne.

na biyu: bisa riko da wani yanki daga riwayoyi duk da dai mursalai ne sai dai kuma cewa an gyara raunin da suke da shi ta hanyar aikin da malamai sukai a riwayoyin kamar yanda wannan shi ne ra’ayi na, daga cikin su akwai riwaya mursala data zo daga littafin Shara’i (malaman mu sun rawaito cewa suratu Adduha da Alam Nashraha sura ce guda daya, haka Filu da Li’ilafi sur ace guda daya)[2]

daga cikin riwaya mursala da aka hakaito to daga Alhidaya(sh:7) da Afikhul Ridawi, da Almustadrakul Wasa’il babi 7 daga babikan kira’atul hadisul salils da Majma’ul Bayan (Wasa’il babi 1 daga babukan karatu cikin sallah hadisi 4, da Almustadrak: babi 7 daga babukan karatun sallah hadisi 1, daga Abu Abbas Assayabiri: Adduha da Alam Nashraha sura ce guda daya.

Da Almusnad daga Shajaratu Afiyu Bashar Nabbal daga Albaraki: Alam tara kaifa da Li’ilafi sur ace guda daya.

Daga ciki akwai ingnatacciyar riwayar Zaidu Shahham: Abu Abdullah (as) ya jagorance mu sallar Asubahi sai ya karanta Adduha da Alam Nasharaha cikin raka’a daya[3]

Fuskar dalili: shirywar wa kan wajabcin karanta su a hade a bayyane yake babu fagen jidali, lallai aikin Imam (as) da jumlacewa yana daga abinda yake jawo faduwa kafa dalili a jumlace saoi dai cewa yana kasance ya samu karfafa daga abinda ya zo cikin Marasil din riwayoyi kamar yanda Malamin mu Assayid Hakim (ks) yayi ishara zuwa ga hakan.

Daga ciki akwai riwayar Mufaddak bn Salihu daga Abu Abdullah (as) ya ce: naji shi yana cewa: kada ka hade surori guda biyu cikin raka’a daya in banda Adduha da Alam Nasharaha da Alam tara Kaifa da li’ilafi[4]

Cikin Almadarik: 3 sh 377 daga sharhin Urwatul wuska: j 9 sh 328: lallai ni ban tsinkayi wani ingantacce dalili d ayake shiryarwa kan wajabcin karanta su hade ba iya abinda na iya cimma sune riwayoyi guda biyu kuma dukkanin akwai bukatar a tattauna kansu cikin isnadin su da abinda suke shiryarwa kai, daya daga cikin su itace ingantacciyar riwayar Zaidu Shahham _ kamar yanda ta gabata sai dai cewa bata shiryarwa kan wajabcin hade surori biyu da har zai nuni kan cewa sura ce guda daya sakamakon jumlacewar aiki.

Na biyu riwayar Mufaddal bn Salihu wacce ta gabata_ ishkali na hawa kan kafa daili da ita: da farko ta fuskani isnadi lallai rarrauna ne sakamakon zuwan Mufaddal bn Salihu, kamar yanda yake a hanyar Ayyashi zuwa gareshi mursalan.

Na biyu ta fuskanin abinda take shiryarwa lallai ta gaza, lallai togacewa ne daga hani kan hade tsakanin surori biyu da yake na haramci ko karhanci bisa sabanin maganganu guda biyu tsakanin manyan malamai, kololuwar abinda yake cikin sa a wannan lokaci shi ne kore haramci ko karhanci cikin kebantar wadannan surori guda biyu, da cewa bai haramta ba ko ba makaruhi bane hade su da cudanya su, saboda haka riwayar bata shirywarwa kan wajabcin hade tsakanin surori biyu, bari dai an tafi kan yawaituwar surori, da wani fadin daga abinda ya girmama tsakanin malamai shi ne kasantuwar su sura guda daya, kamar yanda aka hakaito kansa sai dai cewa kuma riwaya ce mursala amma dai an gyara ta da aikin malamai kamar yanda hakan shi ne ra’ayi na.

Sai dai cewa malamai da suka zo daga baya sun tafi kan cewa surori ne biyu da suka ratayu da juna duk da cewa ana hade su cikin sallar.

Babban malamin hadisi Yusuful Bahrani cikin Alhada’ik: j 8 sh 202 ya ce: mutum na farko da ya fara sabawa haka shi ne Almuhakkikul Hulli (ks).

Duk wanda ya tafi kan hadewar su hakika ya kafa dalili da ijma’i da riwayoyi kamar yanda ya gabata sai dai cewa wasu ba’arin malamai na wannan zamani bisa abinda yake garesu daga maginar su sun tafi kan cewa wannan rauni ya fadar da riwaya kuma isnadi bai gyaru ba da aikin malamai, sannan abinda ya zo daga riwayoyi cikin babin lallai yana da raunin isnadi sakamakon samun irsali, wannan Kenan da farko: kari na biyu: shi ne abinda aka hakaito daga ijma’i daga madaraki da kuma jingina kan wadancan riwayoyi hakika mun rigaya mun fita daga ijma’i sakamakon rashin samun karbuwar madogarar su bisa raunanar su cikin isnadi, kan wannan ne ya zama abinda ke hukunta hadewa ya gaza, bamu da wani dalili abinda la’akari kan haka, shi kuma rashin dalili dalili kan rashi, sai a lura sosai, lallai sabanin zai kasance na magina.  

Amma wadanda suka tafi kan cewa surori ne masu banbanci da juna kamar yanda wurin wadanda suka zo daga baya hakan ya kasance sakamakon rko da wasu fuskoki: na daya: kamar yanda yake da Almadarik: daga tabbatar da raba tsakanin su da karanta basmala da ya zo cikin kur’ani kamar sauran surori daga cikin abinda yake shiryarwa kan cewa surori masu macu cin gashin kansu.

An amsa wannan ishkali: wannan kaifiyya tsakanin surori kadai ya kasance daga tattarawar da akaiwa mushafi da tsara surori lokacin Halifofin musulmai musammam ma Halifa na uku bayan tabbatar da wannan tsari da kaifiya ya kuma kona abinda sauran kur’anan da aka rubuta kan fatu da takardu.

Sannan anyi ishkali kan wannan amsa: hakika makomar hakan na tukewa zuwa ga da’awa kan samun jirkita cikin kur’ani mai girma daga fuskar kari ma’anar Karin basmala tsakanin surorin Adduha da Alam Nasharaha alal misali, tafiyar kan jirkita da kari a yanke gurbace yake da ittifakin musulmai, kamar yanda Halifa na biyu ya nufi kara harafin wawun cikin wata aya sai ya zama ya fuskanci bore an zazzare takubba kamar yanda ya zo a tarihi sai ka koma ka duba, idan ya sabani ya kasance tsakanin musulmai kan jirkita kadai to cikin tawayar ayoyi ne bawai kari ba cikin su, hakika ya tabbata a muhallin sa sananne wurin ahalin sacewa babu jirkita cikin kur’ani mudlakan babu cikin kari ko tawaya, idan an samu wata jirkita to cikin ma’ana ne da dabbaka shi sai suke jirkita Magana daga muhallin ta bawai kari ko tauyewa lafuzzan sa ba.  

Abinda ya fi dacewa da daidaita cikin amsa kamar yanda yake wurin ba’arin wasu manya malamai shi ne da farko: hakika tsuran tattaruwar sura kan basmala baya hukunta banbantuwar ta daga wanin ta bai kuma yayewa kan kasantuwar ta sura mai cin gashin kanta, duk da cewa mafi galibi shi ne kasantuwar hakan bai fa’idantar da komai face zato kamar yanda bata shirywarwa zuwa dawwama, saboda haka bamu da wani dalili kan cin gashin kai kuma shi rashin dalili dalili ne klan rashi.

Na biyu: shi jirkita da kari kadai yana gasgatuwa da ace ya kasance da nufin cewa shi wani yanki ne daga kur’ani, sai dia kuma cewa mukamin ba haka ya nun aba, bari dai an kara basmala ne domin ta kasance mararraba tsakanin surori alama kan cin gashin kan su kamar sauran alamomi ko bayanai da aka ambata cikin farko-farkon sura, sannan bata nuna lamba ko alamar aya in banda suratu Fatiha hamdu kamar yanda ya gabata, sai a lura     

 Shi kur’ani saukarwa ne da sauka, na farko ya kasance karo guda kamar yanda ya kasance cikin lailatul kadri na biyu kuma sannu-sannu a hankali a hankali cikin shekaru 23 daga aiko annabi har zuwa wafatin sa, cikin na farko basmaloli sun kasance.




[1] Babban malamin Assayid Hakim (ks) cikin mumtamsakihi j 6 sh 176 ya fadi haka, cikin Al’intisar sai dai cewa Assayid Kuyi cikin sharhin san a Urwatul wuska j 14csh 327 ya ce mu bamu samu haka cikin Al’intisar ta yiwu yana nufin Al’ibtisar

[2] Alwas’il: babi na goma da babukan kira’atu fi salati hadisi 9

[3] Alwasa’il: babi na 10 daga babukan kira’a fi salati hadisi 1

[4] Alwasa’il: babi 10 daga babukan kira’a fi salati hadisi 5

Tura tambaya