lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Gudummawar da addu’a take bayarwa a rayuwa

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ﴾

Ban halicci aljanu da mutane sai don su bauta mini.

Akwai wata ta tambaya da take fadowa kwakwalwar mutum shine cewa hakika Allah ta’ala ya sanya bauta masa matsayin hadafin samar da mutum, shin wannan hadafi yana dacewa da zatin mutum, shin yana amsa bukatunsa na asasi ko kuma baya amsa su? Abinda hikima ke hukuntawa cikin dukkanin ma’abocin hankali shine hadafinsa ya kasance ya dace tare da zatinsa, ya kuma dace da bukatunsa da ikon sa, da hadafi zai kasance bako daga bukatun mutum da kudurarsa, da wannan hadafin ya gaza tasiri cikin kufansa, alal misali mu kaddara akwai wani mutum da yake da karkata da kwadayi zuwa ga ilimin likitanci kuma yana kudura kan kustawa cikin ilimin, wannan mutumi nda zai karkatar da hadafinsa ga ilimin lissafi ko ilimin injiniyanci, to da wannan hadafi zai kasance ya gaza tabbatar ta kufansa, da kuma hadafin bai kasance mai tabbatuwa ba sakamakon ginuwar zatin sa, sakamakon hadafin bai dacewa da dabi’arsa da karkatarsa, baya kuma dacewa da kudurarsa, bay a kuma iya amsa bukatun sa, mutum ma’abocin hankali ya zamanto ya ajiye kansa cikin hadafin da bai haduwa tare da kansa hakan ya sabawa hikima, kuma rushe manufa ne, sabida ya sanya kansa cikin hadafin da baya dacewa da zatinsa.

Allah ta’ala mai hikima ne, hikimar sa tana hukunta ya sanya hadafin samuwar mutum hadafi da yake dacewa da zatin mutum, kuma mai amsa bukatunsa, Allah ta’ala ya sanya ibada hadafin samuwar mutum, idan ibada bata kasance bukata ta zati cikin mutum ba, idan ibada bata kasance tana dacewa tareda zatin mutum ba, da kuma cewa mutum yana bukatuwa zuwa gareta a dabi’ance da halittarsa,  sanya wannan hadafi ga mutum sanyawa ce ga lamarin da bai dacewa ga ma’abocin hadafi, hakan ruguje hadafi ne daga samuwar mutum, kuma shi ruguje manufa abu ne mai muni, kuma shi abu mai muni baya gangarowa daga ma’abocin hikima mudlaki, saboda haka natija zata kasance: ita ibada hadafi ce da mutum yake kwadayinta cikin zatinsa, kuma yake bukatuwa zuwa gareta cikin zatinsa, ko da kuwa Allah bai ya sanya masa hadafi ba lallai shi yana bukatuwa bukatuwa ta zati ga wannan hadafi, shin ya inganta cewa ibada tana raya bukatarmu ta zati? Shin muna bukatuwa zuwa ga ibada bukatuwa ta zati ko kuma A’a? addu’a bargon ibada, addu’a itace mafi bayyanar masadik da surorin ibada, shin mutun yana bukatar addu’a, ko kuma alakar sa da addu’a tsuran dangantakar sauke wazifar da ta wuyansa ne, bawai cewa addu’a tana amsa bukatar sa da kuma gamar da badinin sa? Ita addu’a haka take tana amsa bukatunb zahiri dana badini, ina kira ne ba badini kira ne na halitta da badinin mutum, ko da kuwa Allah bai sanya ta hadafi ga mutum ba.

 

  

Bukata ta farko: bukatar mutum zuwa ga numfashi da fitar da abinda ke zuciyar sa

Kowanne mutum yana bukatar bayanin zatinsa, kowanne mutum yanayin tsanani kan samun sa, bakin ciki da takaici kan samun sa, tsanance-tsanance da damuwa kan kewaye shi, idan wadannan abubuwa suka mamaye suka tsananta ya rasa mafita kan kaiwa ga su shake shi ya fadi ya mutu idan har bai tofar da abinda yake masa kaikayi a kirji ba Kenan, cikin kawar da tasirin wadannan kunci da kuntatar da ke cikin zuciya mutum yana bukatuwa da ya tofar ya Magana domin karkade su daga cikin zuciyar sa, yana bukatar ace ya zauna tareda wani mutumin da yake kaunar sa yake kuma sauraren sa yake maraba da jin ra’ayinsa domin ya bashi labarin radadin da yake fama da shi, ya zamanto ya samu damar bashi labarin bakin ciki da damuwar da yake ciki domin karkade damuwar daga cikin zuciyar sa. Mutumin da ya gaza bayanin damuwar sa da bakin cikin sa ba to bakin cikin zai kashe shi rayuwa ta kar shi, ya jarrabtu da kulli cikin zuciya, zai wayi gari rikitaccen mutum da bazai iya rayuwa cikin nishadi da annashuwa ba, saboda haka mutum yana bukatuwa bukatuwa ta zati zuwa ga karkade damuwa da bakin ciki daga cikin zuciyar sa, karkade bakin shine ake kira da addu’a, lokacin da mutum yake tsayuwa a gaban ubangijinsa ya kai masa kukan damuwar da yake cikin da tsananin da yake cikin a rayuwa, da zunuban da ya aikata, lallai ahaka yana magance kulli da kuntatar da yake fama da ita cikin zuciyar sa, sannan hakan zai samar masa da sauki da sassautar kullin da yake tareda shi lokacin da yake addu’a da munajati tareda masoyin sa, ba kowa bane wannan masoyi sai Allah, sa’ilin munajati da wanda baya tona asirin sa, wanda bayyana aibobin sa, wanda yake karbar kukansa, yayin da tabaraka wa ta’ala yace:   

.

﴿ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ﴾، ﴿وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِ إِذَا دَعَانِ فَلْيَسْتَجِيبُوا لِي وَلْيُؤْمِنُوا بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ﴾

Ku kiraye ni zam amsa muku. Idan bayina suka tambayeka game da ni lallai ni ina kusa-kusa ina amsa addu’ar mai kira idan ya kirani ko su nemi amsawa ta su yi Imani da ni tsammanin su sa shiriya.

 

Bukatuwa ta biyu: bukatuwar mutum zuwa ga fata:

Kowanne mutum idan zunubai suka tattara sukai masa yawa sai yaga ya fara debe tsammani, sai ka same shi yana cewa: kai ni ga bazai taba yiwuwa in canja ba, ni mutum ne mabarnaci na aikata zunubai da yawa, ni tsiyatacce ne, an halicce ni don tsiyata, ba da ban na kasance matsiyaci ba a zatina, ba da ban an halicce ni don na tsiya ba, da ban kafe kan aikata zunubai da sabo ba, da ban yi shekaru ashirin ko talatin ioa cikin sabo da zunubai ba, mutum idna ya barna da sabo da yawa sai debe tsammani ya same shi da cewa shi zatinsa tsiyatacce ne ba zai karabi kowanne irin canji ba, idna debe tsammani ya same shi sai ya zama mutum mai son daukar fansa, ya koma mutum da yake rayuwa cikin tunanin fansa da gaba kan jama’a, sakamakon yana ganin kansa kasa da waninsa, wanin sa yana iya canjua rayuwar sa, amma shi ya zama ba zai iya canjawa ba.

Hanya day arak ta magance wannan kuntata ta zuciya itace addu’a, addu’a ita take iya canja mutum, Allah ta’ala yana cewa ya bawana ka tunkaro rahamata (rahama ta ta yalwaci komai da komai) (yaku bayina da suuka aikata barna a kawukansu kada ku debe tsammani daga rahamar Allah lallai Allah ya na gafarta zunubai baki dayansu lallai shi mai gafara ne da jin kai) ya zo cikin hadisi cewa: rahamar Allah tana yaduwa ranar kiyama har ta kai ga Iblis ya saran samunta alhalin shine ya batar da halittu baki dayansu, saboda haka ita addu’a tana sabunta fata tana shuka shi cikin zuciyar mutum, addu’a tana tunbuke rashin jin fata cikin mutum, tana sabunta nishadi cikin mutum, tana sanya mutum ya zama mai kazar-kazar mai fata cikin rayuwa da gina kansa da samarwa.

 

Bukata ta uku: bukatuwar mutum zuwa ga yiwa kansa hisabi:

Ba zai yiwu mutum ya samu cigaba ba matukar ba ya yi wa kansa hisabi, hanyar kamalar zati shine nakadin shi zatin, nakadin zati itace hanya ga samun kamalar zatin, Allah tabaraka wa ta’ala yana cewa:

 

﴿إِنَّ اللهَ لَا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّى يُغَيِّرُوا مَا بِأَنْفُسِهِمْ﴾،

Hakika Allah baya canja abinda yake tareda mutane matukar su  basu canja da kansu ba.

Rayuwa tana canjawa kan canjawar zati, canjawar zati bayani ne kan yiwa kai hisabi, sabida haka yiwa kai hisabi shi mafara ce da mutum yake bukatuwa zuwa gareta domin ya samu damar canja matafiyar s, addu’a itace hanya guda daya rak cikin yiwa kai hisabi, lokacin da mutum yake kebancewa da kansa ya bijiro da munanan ayyukansa ya tunato da bakaken kwanakin sada dararen sa, ta hallaro da file din ayyukansa ya lissafa duk wani zunubi da sabo da kuskuren sa, wannan lissafi da hisabi shine hanyar kamala, iatace hanyar habbaka canja zatinsa, sabida haka ne cikin hadisi ya zo cewa:

”حاسبوا أنفسكم قبل أن تحاسبوا“،

Ku yi wa kawukan ku hisabi gabanin yi muku hisabi.

Bugu da kari ya zo daga Imam Kazim (as) fadinsa:

 

”ليس منا من لم يحاسب نفسه كل يوم“،

Baya daga cikin mu duk wanda baya yi wa kansa hisabi kowacce rana.

Sabida me? saboda ya samu damar canja rayuwar sa, sabida cigabantar da ita, idan ya aikata aiki mai kyawu sai ya nemi Karin Allah daga gareshi, idan kuma ya aikata mummuna sai ya nemi gafarar Allah ya tuna zuwa gareshi daga barin aikata su, yiwa kai hisabi hanya ce ta cigabantar da kai, kamar yanda kake yi wa kanka hisabi cikin kasuwanci shin ka samu riba ne ko kuma asara kayi, ka yi wa kanka hisabi kan zunubai da sabo, domin ka samu damar kubuta daga wadannan bakaken files (fayaloli) ka wayi gari fayal dinka na sheki da haske babu duhu cikin sa, sabida haka yiwa kai hisabi wata bukata ce da mutum yake bukatuwa zuwa gareta a asasi, hanya ciyar da ita da amsa mata itace addu’a, kan wannan Diraru cikin siffanta Sarkin muminai Ali (as) yake cewa:

 

”كان والله غزير الدمعة، طويل الفكرة، يحاسب نفسه إذا خلا، ويقلّب كفيه على ما مضى

Ya kasance mai yawan zubar da hawaye da kuka, mai yawan zurfafa tunani, yana yiwa kansa hisabi idan ya kebantu, yana jujjuya tafukan sa kan abinda ya gabata.

 

Bukata ta hudu: bukatuwar mutum kan sanin kansa:

Ta yaya mutum zai iya sanin kansa? Ya zama wajibi kowanne mutum ya san ko shi waye ya san kansa, zatin mutum na da muhallan karfi dana rauni.

Tura tambaya