sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- Fikhu » Karijul Fikhu bahasi cikin kira'a da bayyanar da haruffa.
- » sakafa da sakafantacce a mahangar muslunci
- » Sirri daga sirrikan imam sadik (as)
- » Sirri daga sirrikan Sayyada Fatima Ma’asuma (a.s)
- tafsir » Kada ka cutar da wanda kake baiwa Sadaka
- Fikhu » Bahasul Karij-mas'ala ta 14 baya halasta fara zikirin ruku'u gabanin kaiwa ga haddin ruku'u
- Fikhu » Bahasul Karij 24 Muaharram shekara 1442 cigaba kan bahasin hukunce-hukuncen ruku’u
- » Abuta ko qawance
- » YARO MATASHI TARE DA TSOHO
- » Muhimman wasiyoyi uku daga Imam Sadik (as)
- » Sai nayi na so abu kaza, sai muka so abu kaza niyya, sai ubangiji ya nufi abu kaza
- » Mace da tawayarta
- » Bada'u tsakanin hakika da kagen makiya
- » Mene ne ma’anar fadin jumlar (iliminsa yafi hankalinsa yawa) shin wannan jumla za ai la’akari da ita suka zuwa ga Sayyid Kamalul Haidari?
- Akida » ADALCIN ALLAH MATSARKAKIN SARKI
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
Hakika Ahlil-baiti daga A’imma tsarkaka (a.s) su sun kasance kamar salsala da yankunansu yake kamanceceniya da juna wadanda sashen su ke danganewa da sashe, su tsatson annabi ne (s.a.w) a halicce da dabi’ance sune mafi daukakar mutane karfafaffiyar igiya wacce manzon Allah (s.a.w) dangane da ita yake cewa
(( اني تارم فيكم الثقلين كتاب الله عترتي اهل بيتي ، ما ان تمسكتم بهما لن تضلوا بعدي ابدا )
Lallai ni mai bar muku nauyaya biyu ne littafin Allah da tsatsona Ahlin gidana, matukar kuka yi riko da su ba za ku taba bata a bayana ba har abada.
Rayuwarsu makaranta ce mai girma da ta ke kwararar da failoli ta kuma ke yada haskayen ilimi da fasaha da ladubba da tsantseni, su ambaton sunayensu waraka ne daga dukkanin cuta, mutumtakarsu abar koyi ce haka ma mu’ujizozin su ababen kwaikwayo ne da annabta cikin baki dayan fagage, kai hatta sai da takai ga manzon Allah (s.a.w) ya ce:
(( نحن اهل البيت لا يقاس بنا احد )) .
mu Ahlil-baiti ba kwatanta mu da kowa.
karantar rayuwar kowanne Imami da cikakken shakali mai cin gashin kansa zamu samu cewa akwai wata siffa ko wani hali da ya mamaye rayuwarsa da fadadden shakali da mafi kyawun sura, misali Imam Bakir (a.s) ya fifitu da ilimi da koyar da malamai, amma Imam Sajjad zamu samu cewa rayuwarsa ta haskaka da da yawan ibada da addu’o’i…..
sai dai cewa hakan bai nufin ragowar Imamai cikinsu akwai gajiyawa da takaitawa cikin wadancan fagage sai dai cewa kadai babban dalili a cikin hakan shine yanayin da suka samu kansu na siyasa da zamantakewa da ya bubbugar da wancan siffa da shakali mafi kyawu cikin wadancan iyakoki da dabaibayi wadanda zalunci da sasarinsa ya shata su da karfe da wuta
imam Rida (a.s) sha’aninsa bai da banbanci da sauran Imamai (a.s) tun lokacin da ya zo duniya har zuwa shahadar sa ya kasance babban tafki da ilimi da hakuri ke nitsewa cikinsa sani ke koshi daga gare shi dukkanin girman mas’ala tana kankancewa gabansa, yana amsa iyakokin halal da haram na addini cikin kiftawar ido tare da hakikanin daidai.
Imama ya rayu karkashin zalunci da danniyar Abbasawa cikin rayuwa da take cike da bukatuwa da radadi da wahalhalu ya shallake jarrabawowin zamani daban-daban, sai dai cewa shi jurewa hakan.
Mahaifin Imam Rida (a.s) Imam Musa bn Jafar ya kasance a daure cikin fursun din Abbasiyawa mai ban tsoro, sai dai cewa adadai wannan lokacin idan dawagitai na kansa suna bibiye da dukkanin motsin Imam Rida amincin Allah ya kara tabbata a gare shi da tsananin bibiya da dandakewa sakamakon siyasarsu mai tsanani da take lamzinta kisa da halakarwa bayan sun gane cewa shi Imami ne ma’asumi, sun kasance suna jin tsoran sa kai hatta kalma guda daga gare shi tana basu tsoro kai hatta sunbatar kananan yara!! Tana sabbaba takurawa ga masarautar Abbasiyawa ta yadda ya wayi gari yana barazana da wanzuwar mulkinsu da samuwarsu cikin mulki sakamakon sun sabbaba tsanani da wahalhalu cikin halittu ga kawukansu gabanin sabbaba cutuwa bga wanin su!
Halifan Abbasiyawa Mamun ya aika da gayyata zuwa ga Imam Rida (a.s) a madina yana gayyatarsa bisa tilashi da ya taso daga birnin Madina zuwa garin Kurasan, wannan gayyata ta daidai da lokacin faruwa yunkurin juyin-juya hali da ya faru cikin a cikin Madina a zamaninsa, ba wani ynukuri bane face yunkurin Muhammad bn Jafar Sadik dan baffan Imam Rida amincin Allah ya kara tabbata a gare shi.
Mamun yayi yunkurin sauya fuskar siyasar Abbasiyawa cikin mu’amala tareda mutane a bayyane bayan ya ga cewa babu wani amfani cikin bakararriyar siyasa, ya kasance yana boye kiyayyarsa ga Imam yana nuna cewa shi yana daga cikin masoyansa.
A daidai wannan lokaci Mamun ya kasance yana bakin kokarinsa wajen ganin ya sanya Imam da magoya bayansa a gaban tarkonsa a garin Kurasan domin ya sanya idanunsa kansu da dukkanin motsinsum ya kuma yi musu ukuba da wannan sharri, dalili kan abin da muke fadi shine cewa hakika Mamun ya iyakance mostin Alawiyyawa daga Madina zuwa Kurasan, ya kuma sanya sojoji kan dukkanin kai kawonsu suna bibikye da su suna raka su.
Imam Rida (a.s) ya taso daga Madina zuwa Kurasan zukatan mutane na tafiya tareda shi suna raka shi suna damfaruwa da shi duk inda yaje duk inda ya sauka.
Imam Rida (as) ya tashi tsaye da ayyukan tabligi da ilimi na addini fadadadde mai kayatarwa cikin hanyarsa zuwa Kurasan ya amsa tambayar dukkanin wanda ya tambaye shi daga dukkanin kowanne addini cikin kowanne kofa daga kofofi, sai ya zama ma’abota hankula dama jahilai sun gigita daga iliminsa bai day aba tareda banbbancewa ba!
Hakika ya kasance hasken rana da bazu cikin duffan kasa dukkanin wanda ya haskaka da shi yana rayuwa!
Lokacin da Imam ya isa garin Kurasan sai Mamun ya nada shi a matsayin mai jiran gado bisa tilas ba tare da son ransa ba yana tsammani cewa da hakan ne zai kubuta daga rigingimun siyasa da suka kewaye shi da kuma amfanin da wannan dabarar ne zai samu hutu daga daukar fansa da juyin-juya hali kuma mulkinsa ya samu wanzuwa da dawwama har abada.
Imam Rida (as) bai kasance yana da wani kwadayi ba cikin wani matsayi ko mukami da zukata ke dagawa zuwa gare shi, saboda ya san zurfin shaidanci Mamun da dabararsa ta siyasarsa mai girman sai dai cewa Imam (as) ya karbi wannan nadi saboda wasu dalilai daga cikinsu akwai rage kaifin tsananin da barazanar da shi’arsa suke fuskanta da kuma kankin kansa da kuma taka burki kan hakan ta hanya samun shiga a cikin fada.
Mutanen masu tarin yawa daga fada sun nuna rashin amincewarsu da nadi Imam rida (as) a wannan muhalli mai hatsari daga cikinsu Fadalu bn Sahalu wanda ya bayyana hakan karara gaban Mamun lokuta da daman gaske.
Nada Imam ya kasance lamari bako mai ban mamaki da ya haifar da shakku da tunani tsakankanin mutane, har takai ga wasu sun kasa gasgata abin da suka ji, musammam ma kasantuwar A’imma tsawon tarihi sun kasance sun dauki matsayar gaba ga karkatattun hukumomi tun daga wafatin manzon Allah (s.a.w) har giftawa ga zamanin mulkin Umayyawa sannan Abbasiyawa, idan muka dubi Haruna Rashid zamu ga shine ya kashe mahaifin Imam Rida (as) ta hanyar shayar da shi guba lokacin da yake tsare da shi a fursun mai tsananin duhu!!
To kaka za a ce kuma kwatasam wannan ya faru?!!
Lamarin yakai ga wasu mutane daga dangin Abbasiyawa sun kasa daurewa wannan nadin sun fara tunanin shirin hambarar da Mamun daga karagar mulki, sai wadannan masu matsala da matakin da Mamun ya dauka na nada Imam suka taru bayan rufaffun kofofi suka ce ma junansu: (dole ne mu cire mamu mu nada wani matukar dai bai janye daga wannan mataki da ya dauka ba)!!
Sannan a gefe guda kuma zamu tarin suka da martani da tambayoyi da suke sabawa hankali daga bangaren magoya bayan Imam Rida (as) da masoyansa.
Imam Rida (as) ya kasance yana amsa musu da cikakkiyar hujja mai gamsarwa, wannan mataki nasa ya kasance domin kare hakkokin raunana da haramtattu daga hakkokinsu.
Mamun ya nemi Imam Rida (as) ya yi wata huduba gaban taron mutane hudubar da ta tarihin muslunci bai shaida irinta ba Mamun ya ne mai tunani cewa zai samu yabawa daga gare shi, hudubar Imam ta kasance takaitacciya amma mai cike da ma’ana da isar da sako ta kuma tattaro dabi’un Imam da bayyana hakikaninsa kan rashin amintarsa da laminta kan daga wannan nadi na Mamun, ya zo cikinta:
(( بعد حمد الله والثناء عليه ان لنا عليكم حقا برسول الله ( صلى الله عليه واله وسلم ) ولكم علينا حق به فاذا اديتم الينا ذلك وجب عليكم الحق لكم ))!!
Bayan godiya da yabo ga Allah hakika muna da wani hakki kanku da manzon Allah (s.a.w) kuma kuna da hakki kanmu da shi idan kuka sauke hakkinmu garemu to hakkinku ya wajaba kanku!!
Mamun ya kasance yana burin cewa Imam yayi masa kammalalliya biyayya, sai dai cewa shi babu abin da ya girba face faduwa kasa warwas, sannan wannan huduba ta Imam Rida (as) dalili ce yankakke hujja mai huda kan cewa bai dace shi ya zama bawan mukaman siyasa ba sannan ta juya ta zama musiba babba da ta fda kan Mamun mummunan naushi da ya tona asirin Abbasiyawa.
Mamun ya nufi cutar Imam Rida (as) ya kuma rage matsayin da kaskantar da iliminsa gaban mutane da aljannu, sai ya nemi wasu ba’arin malaman fada da malaman addini da su shirya tambayar Imam Rida (as) kan falalar Imamancinsa da ma’asumancinsa gameda tunaninnkan Abbasiyawa sai ya zama sun fadi babu nauyi babu nasara, sannan sukai nadama kan abin da suka aikata domin sun hakawa Imam rijiya amma sai ya zamanto sune suka fada wannan rijiya, suka kuma gane cewa shi ilimin Imam ilimi ne daga Allah matsarkaki kuma shi babban tafki ne daga ilimin da wutar masharranta ba ta iya kone shi domin daga shi ne dukkanin magudana da koramu suke sha daga ahalin ilimi!
Mamun ya nemi Imam Rida (as) da yayi ayyuka a bude kai tsaye gabansa bayan ya samu labarin daukakar matsayin Imam gaban jahilai.
Sai ya nemi Imam da ya jagoranci sallar Idi, Imam yayi watsi da bukatar Mamun, sai dai cewa Mamun yaki yarda ya kafe lallai sai Imam ya jagoranci wannan sallar Idi.
Dalilin da ya sanya Imam watsi da jagorantar sallar ya bubbugo ne daga kasantuwar Imam bai gamsu da wannan nadi ba da shakalin san a zahiri, ta kaka kuma zai karbi al’amurran da ya zama wajibi a dabbaka hukuncin Allah cikinsu a bayyane misalin tsayar da sallar Idi ba tareda bayyana zaluncin azzalumai ba da abubuwan da suke faruwa, sabanin abin da shi Mamun yake so!!
Daga karshe dai Imam bisa tilashi ya karbi jagorantar sallar ya fito daga gida da yanayin kushu’I ya na mai tattaro siffofin salihai, da A’imma (as) da annabawa (as) yana mai nesantar dukkanin alamomin girman da da jiji da kai da ruduwa na boge wadanda Mamun ya kasance yana siffantuwa da su.
Wannan taro na taron mutane ya yi kwarji matuka da yayi kamamceceniya da zubar ruwan sama ya zama yanayin ya fara dawo da kwakwalensu zuwa ga zamanin manzon Allah (s.a.w) sukai mu’amala da Imam Rida (as) da dukkanin dumamar zukatansu da kwakwalensu domin begen Imam Rida (as) yayi hukunci ya kuma dabbaka muslunci lamarin da ya haifar da raurawar matsayin Abbasiyawa da tsorata su da gigita lamarin ya juya ya zama azaba kansu!
Sai Sahalu bn Fadalu ya sanar da daya daga mashawartansa ya sanar da Mamun abin da yake faruwa sai Mamun ya bda umarni fasa yin wannan sallah, Imam ya dawo gida ba tareda jagorantar sallar ba sai dai cewa mutane basu janye soyayyarsu ga Imam ba lamarin da ya sanya Mamun fara tunanin yadda zai kubuta daga Imam da kowacce hanya ce, saboda girma da daukakar mukamin Imam (as) ya wayi gari babban hatsari kan Mamun daga karshe dole sai sanya guba yayi cikin abinci Imam ya kubuta daga barazanar da take fuskantarsa, tsammaninsa cewa guba zata iya dusashe hasken ranar Imam ta gama da daukakar matsayinsa da ambatonsa!
Hakika Imam Rida (as) yayiwa Harsamatu bn A’ayuni wanda ya kasance hadimin Mamun ne amma kuma masoyin Imam Rida (as) da cewa ka da a bari Mamun yayi masa wankan gawa ya bashi labarurrukan da zasu faru daga baya kansa sannan tabbas wadannan abubuwa sai da suka faru!
Imam Rida (as) ya bashi labarin yadda za a sanya masa guba da kasha shi, hakika wasiyyar Imam Rida (as0 ba ta bar wani gurbin shakka ba da cewa lallai shi Imam rida (as) ya mutu ne shahidi sakamakon gubar da aka shayar da shi ita, bawai yanda ba’arin wasu jahilai da makiya suke da’awar cewa wai Mamun bai shayar da Imam guba ba, bari wannan da da’awa ta sabawa akidarmu ta imamiyya saboda Imam Sadik (as) yana cewa
(( مامنا الا شهيدا او مسموما )) .
babu wani mutum daga garemu face shahidi ko wanda aka shayar da shi guba.
Bayan shayar da Imam guba sai Imam ya fara maimaita kalmarsa ta karshe cikin rayuwarsa:
(( قل لو كنتم في بيوتكم لبرز الذين كتب عليهم القتل الى مضاجعهم )) .
Kace ko da kun kasance cikin dakunanku da wadanda da aka rubuta musu kisa sun fita zuwa ga wuraren kwanciyarsu.
Mamun ya boye labarin shahadar Imam (as) tsawon kwana daya sakamakon tsoron da yake kan abin da ka iya faruwa kan hakan daga karshe gaskiya ta bayyana, daga karshe sai ya aika da gayyata ga dukkanin dangin Abu dalib domin halartar jana’izar Imam ya bayyana musu cewa Imam Allah ya karbi ransa amma ba a samu wata shaida a jikinsa da zata iya bayyana dalilin mutuwarsa ba!!
Sai dai cewa wannan da’awa ta karya daga Mamun ta kasance kamar misalin kawalweniya da take nesanta na kusa da kusanto da na nesa ta wayi gari dalilin tsananta fusatar mutane da kiyayyarsu kan Mamun da kuma neman yin kisasi kan Mamun, lamarin da ya tsorata Mamun ya kuma rasa rashin yarda hatta daga masoyansa lamarin ya tilasta Mamun nuna damuwa da bayyana bakin ciki kan mutuwar Imam yana tsammanin zai iya yaudarar mutane da kuma biye ta’addancin da ya aikata da dawo da lamari karkashin kontiron dinsa.
Daga karshe dai an raka jana’izar Imam cikin jana’izarsa masoya da makiya sun yi tarayya daga mazauna sama da kasa, sai dai cewa Mamun ya bayyana kafewa da dagewarsa kan cewa shi ne zai wanke gawar Imam a binne shi da hannunsa yana mai fadin:
(( اليس زعمتم ان الامام لا يغسله الا امام مثله )) !
Ashe baku ke raya cewa babu mai wanke Imami face Imami misalinsa ba)!
Waye zai masa wanka alhalin dansa Muhammad Jawad yana zaune a cikin Madina a wannan lokaci.
Lamarin bai dauki lokaci mai tsayi kwatsam sai ga bayyanar haske mai huda wata mai haskaka Imam Muhammad Jawad (as) ya zo domin ya shirya mahaifinsa Rida (as) haske biyu da suka bayyana daga dukkanin ayyuka nagari da ayoyi mahaskaka, ta yiwu mafi alherin wanda ya yabe shi da yan baitocinsa shine mawaki Ali bn Abdullah cikin `yan baitocinsa da ya raira wadanda cikinsu yake cewa:
يا ارض طوس سقاك الله رحمته
ما ذحويت من الخيرات يا طوس
Ya kasar Dusi Allah ya shayar da ke rahamarsa.
Wai menene ki ka tattaro daga alherai ya Dusi.
Daga cikin tambayoyin wanna sashin ()
- ALLAH YANA GANI NA A KOWANNE WAJE
- mafhumin addini
- MENE NE YA SANYA AKA HAIFI ALI (AS) A CIKIN DAKIN KA’ABA
- Tuba da tubabbu kan hasken kur’ani da sunna
- ?mai yasa mukeso musan Ahalulbait
- KARIJUL FIKHU 16 MUHARRAM 1441 H- YA HALASTA YIN UDULI DAGA SURA ZUWA WATA CIKIN ZABI MATUKAR BA AKAI GA KARANTA RABI INBANDA FATIHA DA IKLAS
- Wasiyyai da tsarkakakken tsatso
- Daga kowanne malami akwai hikima
- TUFA barbeloli masu yawan gaske sun sauka kan wata qatuwar bishiya, sannan iskar ta kasance iskar kak
- Wahabiyanci tsakanin guduma da uwar makera