sababun makaloli
- Tarihi » masu tarbiyya ga al'umma
- Fikhu » Mas’ala ta bakwai: kallon gefan hanci a halin sujjada,
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi shekara 1442 cikin mas’alar shimfida hannun yatsu hade da juna hatta babban yatsa zuwa kusa da kunne
- Akida » Addu’a sirrin ibada
- Akida » Wasiyoyi uku daga Imam Sadik (A.S)
- Akida » Kibiya ta shida
- Akida » Kibiya ta biyar
- Akida » Kibiya ta hudu
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta uku
- Akida » Kibiya ta biyu-raddi kan Wahabiyawa daga litaffan bangarori biyu-shi’a da sunna
- Akida » Kibiya ta farko-Wahabiya daga Kawarijawa suka fito
- Akida » Kibban Raddi kan wuyan Wahabiyya
- Fikhu » Bahasul Karijul Fikhi- Usul 8 ga watan Jimada Awwal shekara 1442h
- Fikhu » bahasul Karijul fikhi 7 Jimada Awwal shekara 1442 h wada'au shi ne kebantar da lafazi kan wata ma'ana
makaloli
- » Sirri daga sirrikan imam sadik (as)
- Tarihi » nasiha da nusantar al'umma
- » Kowacce rana ashura ce kowacce kasa ma karbala ce
- Fikhu » BAHASUL KARIJUL FIKHU 19 RABIUS SANI 1441 H, JERANTAWA TSAKANIN FATIHA DA SURA DA TSAKANKANIN KALMOMINSU DA HARUFFANSU 47
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » darussan yakini cikin sanin asalan addini
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- Akida » Kibiya ta uku
- » dangantakar addini da siyasa
- » mafhumin addini
- » KARIJUL FIKHU 15 GA SAFAR SHEKARA 1441 CIGABAN BAHASIN BAYYANA KARATU DA BOYE SHI
- Akida » Gamammiya Annabta da kebantacciya daga cikin hadisai masu daraja
- » Wasikar Najashi
- » Ta wacce hanya mutum zai zama Arifi
- Tarihi » Me ya sanya Imam Sajjad (a.s) bai yunkura ba don kafa hukuma?
Mukalolin da akaranta dayawa.
- » Addu’o’I da zikiri kan Karin Soyayya a tsakanin ma'aurata
- » Addu’a makamin mumini-tattaunawa tare da Ayatullah samahatus-sayyid husaini shahrudi
- » SIRRIN SALATI
- » Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar
- » Bahasul karij: Magana mafi karfi itace hade suratu Filu da suratu li’ilafi
- » Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.
- » Me yasa Imam Ali yayi mubayaa wa Abubakar da Umar
- » KAN HANYAR SHUGABAN SHAHIDAI IMAM HUSAINI (AS)
- » Hankali a mahangar makarantar imam kazim (as)
- Akida » Tambaya a takaice: shin Mala'ikan da yake zuwa da surar mutum shima yana da sha'awa
- » HAJJAJU IBN YUSUF!
- » SHIN kana karanta qur'ani
- » Taskar Adduoi 4
- » Taskar Adduoi 2
- » Falalar ilimi da malamai
Annabta
﴿عالِمُ الْغَيْبِ فَلا يُظْهِرُ عَلي غَيْبِهِ أَحَداً * إِلاّ مَنِ ارْتَضي مِنْ رَسُولٍ فَإِنَّهُ يَسْلُكُ مِنْ بَيْنِ يَدَيْهِ وَ مِنْ خَلْفِهِ رَصَداً * لِيَعْلَمَ أَنْ قَدْ أَبْلَغُوا رِسالاتِ رَبِّهِمْ﴾ ؛
Masani boye da bayyane baya bayyana gaibunsa ga wani mutum sai wanda ya zava daga manzo hakika shi ya na shiga daga gabansa da bayansa* domi ya samu tabbas kanb cewa sun isar da sakon ubangijinsu.
Cikin wannan aya ubangiji yana tsinkayar da annabinsa gaibu, tambaya anan shi ne su waye wadanda suke da tsinkayi kan gaibun Allah mdaukaki su wanene madaukan wahayinsa? Cikin fasalin da ya gabata mun tsinkaya da abubuwan da wahaya ya kevantu da su da sababin bukatuwa zuwa gareshi, bayan mun tabbatar da bukatuwar ga wahayi tambaya ta farko da take fadowa cikin kwakwalwarmu shi ne: ta wacce hanya zamu kai ga zuwa ga wahayi? domin amsa wannan tambaya ya zama dole muyi ikirari da cewa daukacin mutane basu da cancantuwa da tanadi yin Allah kai tsaye da Allah madaukaki, kai hatta ma da Mala'ikan wahayi domin su kai ga wahayi su samu ittisali da shi, ta wannan babi ne babu wata hanya da makawa face aiko da manzanni daga jinsin dan Adam domin su zama tsani da tsakaito tsakanin Allah da bayinsa, su sanar da su umarnin Allah da haninsa, ana kiran wadannan jakadu da sunan Annabawa.
Da sannu cikin wannan fasali zamu kutsa cikin bahasin kan hanyoyi sanin annabawa da ismarsu.
Hanyar sanin annabawa
Hakika annabawa sune hanya daya rak don kaiwa ga wahayi, a kowanne lokaci zaka samu cewa akwai wasu mutane `yan cin galla da suke da'awar annabta bisa zalunci da karya, domin sua shuka shakku da kokwanto da vata cikin zukatan mutane, kan wannan asasi, tambaya mai muhimmanci shi ne ta wancan hanya zamu gane annabawan Allah na gaskiya da manzanninsa? Domin amsa wannan tambaya sai mu ce hakika daukar sakon daga Allah musammam cikin mas'alar da ta ta'allaka da makomar dukkanin mutane da farincikinsu, mas'ala ce mai matukar muhimmanci, saboda haka wajibi kan dukkanin mai da'awar annabta ya gabatar da hujja da karfafaffen dalili da yake tabbatar da cewa shi an aiko daga vangaren Allah, sakamakon cewa a hankalce da larurance idan wani mutum yayi da'awar cewa shi yana dauke da sako mai muhimmanci daga wani mutum ko kuma shi shugaba ne to take za a nemi ya gabatar da dalili da zai tabbatar da hakan, wannan na kasantuwa lokacin da ya zamanto ba aminta da shi ba kan da'awarsa.
Daga wannan mahanga ce ake ganin samuwar ayoyi ga annabawa ya zama al'amari na larura domin idan babu su hujja ba ta cika kan mutane, saboda haka ya zama dole ga ubangiji mai hikima ya turo annabawa da ayoyi da mu'ujizozi domin kada tawaya ta afku ga manufar aiko manzanni, domin baiwa makarya damar yin mu'ujiza zai tauye manufar Allah, sakamakon abinda yae tattare da hakan dag avatar da mutane, tabbas Allah madaukaki bai aikata wani aiki da yake tattare da tauye manufa da hadafi, saboda haka bai baiwa makaryata damar mu'ujizozi.\
Daga abinda muka ambata zamu gane cewa lallai mafi muhimmancin hanyar gane annabawan gaskiya shi ne mu tabbatar gangarar mu'ujizozi daga hannunsu kai tsaye ido da ido ko kuma mu ji hadisai ingantattu mutawatirai.
Mu'ujiza a luggance tana nufin wani aiki da yake da sauran mutane suka gaza yinsa, malaman ilimin kalam sun gindaya sharudda ga mu'ujiza, daga cikinsu akwai cewa: dole ta kasance ta ketare abinda aka saba da shi yau da gobe, dole ta cudanya da da'awar annabta, dole ta dace da tanadin abinda ake da'awa, dole kasance tareda kalubalanta da mubaraza da kuma gazawar sauran mutane kan yinta wadannan sharudda hankali na riskarsu, da yawan masu zurfin tunani cikin addinin kiristanci sunyi imani da cewa mu'ujiza trana daga muhimman ayoyi da za a iya tsallakawa zuwa wata duniyar, kamar yanda wasu ba'arinsu suke ganin ketare dokokin dabi'a na daga cikin muhimman abubuwan da mu'ujiza ta kevanta su da kuma kasantuwarta bayyananniyar aya kan lamarin ubangiji na kai tsaye, sannan kari kan haka hakika busharar annabawan da suka gabata- na tabbatatar da annabtar annabawa masu zuwa bayansu, na iya zama karin hujja kan samuwar wahayi, tabbas, a wasu lokuta ba'arin wasu lamurran kamar misalin (dorewar ta tarihi ga addini tareda dukkanin makirci da tukkun makiya) na iya kasancewa dalili kan gasgatuwar addini, sai a haikance wannan ba zai tava zama dalilin da zai gasgata addini ba, domin sau da yawan lokuta zaka samu tunanunnuka na vata da karkata sun dore tsawon tarihi kamar yanda shima tabbatuwar yaduwarsa bai zama hujja, tareda dukkanin haka tattarao dalilai daga ire-iren wadannan zai iya karfafar addini.
Ismar annabawa
Isma tana daya daga cikin muhimman abubuwan da annabwa suka kevantu da su, abin nufi anan shi ne su annabawa katangaggu daga aikata karamin savo da babban savo.
Sannan ita isma shi ne ya kasance ma'asumi bai aikata wani aiki da ake kirga shi matsayin haramun a fikihance, haka kuma kada ya bar aikata wani aiki da ake kirga shi matsayin wajibi, hakika da'irar ismar annabawa ta tattaro isar da wahayi da bayaninsa hakama da zantukan annabawa da dukkanin ayyukansu, ba da ban kasantuwar isma cikin wadannan hali ba kai hatta cikin kaddara cewa annabawa suna barin wajibai kuma suna aikata haramun, to da hakan ya rushe hadafin shiryar da mutane, lallai hakan bai dacewa da hikimar Allah.
Ko kuma muce, kari kan hukuncin hankali wajibi annabawa su kasance ma'asumai daga dukkanin kuskure da zamewar kafa lokacin da suke karvo wahayi daga ubangiji haka lokacin isar da shi zuwa ga bayin Allah da bayaninsa, wannan fa kari kan wajabcin ismarsu hatta cikin magana da aiki, da Allah zai bada izini ga annabawa su bar wajibi su aikata haramun to lallai hakan zai ci karo da hikimarsa zai kuma rusa hadafin halittar bil Adama, ma'ana hakika ya aiko annabawa domin shiriyar da mutane, idan ya zamanto cewa ya halasta ma annabawa aikata haramun to zai zama toshe haynar shiriya, sai dai kuma ba zai tava yiwuwa a lokaci guda abubuwa guda biyu masu cin karo da juna su gangaro daga mai hikima ba.
Tsokaci dangane da isma
An bijiro da tambayoyi masu yawan gaske kan mas'alar isma, a cikin wannan zamani namu an tada shubuhohi masu yawa cikin sabuwar riga da zamu yi dan ishara kan ba'arinsu, daga cikinsu akwai:
1- isma tareda zavin dan Adam
Mafi muhimmancin tambayar da aka bijiro shi ne cewa: shin isma ta kasance daga zavin mutum ko kuma tilashi ce, domin ayyukan mutum da shi kansa suna kimantuwa karkashin yantaccen iradarsa da zavinsa, idan muka kudurce cewa ita isma tilashi ce, to imami zai zama kamar remote control da ake sarrafa shi ba tareda zavinsa ba saboda bai cancanci ayi koyo da shi ko kuma bai cancanci a bashi lada kan ayyuka da yayi ba.
Amsa kan wannan sassaukan ishkali; ita iradar mutum tana da rukuni biyu na asasi sune ilimi da irada, idan mu ka aikata savo, sababin hakan na komawa ga rashin cikakken sani da tsinkaye kan munin abinda muka aikata, ko kuma dai mun rasa karfafaffiyar irada cikin kauracewa aikata hakan, duk sanda wadannan abubuwa biyu suka karfafa da'irar savon mutum zata hasarantu ta dinga karuwa.
Haka zalika su annabawa katangaggu ne ta fuskanin ma'arifa, domin cewa su suna ganin munin ayyuka da kyawuntarsu da idanuwan basirarsu, amma ta fuskanin irada lallai suna da iko da kudura ta yanda guguwar sha'awe-sha'awe bata iya gisgizasu.
Tambaya ta gaba shi ne me ya sanya aka sanya ilimi da irada cikin da''irar `yan tsiraru, gaskiyane cewa abinda aka bjirar zai magance matsalar zavin ma'asumai sai dai cewa kuma tareda haka sababin fifitarsu da daukakarsu kan sauran muatne yana nan wazne ba tareda amsa ba, shi ma'asumi yana kallon savo a matsayin guba mai kisa shi ya sanya ma kwakwata baya yin tunanin kusantarsa, saboda haka mu da a ce mun mallaki irin wannan ilimi da irada da mun samu cikakkiyar isma da Katanga.
Akwai amsoshi kan wannan tambaya da take kallon isma a matsayin wata kyauta daga Allah, daya daga cikin wadannan amsoshi da riwayoyi suke karfafasu, tana ganin warwara na iya samuwa cikin ilimin Allah da ya gabata, ma'ana Allah bmadaukaki gabanin halittar mutane ya sani da iliminsa azali cewa wasu yanki daga mutane zaus yi aiki da zavinsu iya aiki fiye da sauran vangarorin mutane, ta yanda ko da ba basu wata baiwa kevantatta ba lallai da aikinsu na zavi zasu iya fifita vkan sauran dukkain mutane, wannan matsayi shi ne wanda wadannan yanki zasu kai gareshi karkashiun zavinsu shi ne kuma dalilin da ya sanya Allah yi musu kyauta da wannan kyauta, sai suka rabauta da ilimi nda irada ta yanda karkashin hakan suka samu damar amfana da wannan cikakken shinge da Katanga, albarkacinssu su wayi gari shiryayyu masu shiryar da dukkanin mutane, ko kuma muce sababin rabauta da wannan kyauta kari kan ladansu shi ne cewa samar da dukkain hanyoyin shiriya ga dukkanin mutane, tabbas ya zama dole garemu mu waiwaya zuwa ga cewa lallai shi taiumakon ubangiji yana jingina zuwa ga wasu ka'idodjida dokoki, shi Allah madaukaki yana taimakon dukkanin muminai dukkanin wanda ya taka hanyar alheri zai karfafe shi da taimako da tallafi, saio dai cewa taimakon yan a dacewa da fafutika da zage dantse taereda ka'idoji da dokokin da ya sanya su.
2-sakamkon imani da isma.
Masu inkarin isma suna bijiro dawasu adadin sakamako marasa kyawu da suka dogara da wannan imani, saboda haka ne ma suka durfafi yakarsa, hakika wasu kungiya sunyi imani cewa wai ma'asumi bazai iya kasancewa abin koyi ga sauran mutane ba, wai kadai dai abinda zai iya daukaka matsayin annabi shi ne gamagarin rayuwarsa wacce take ba katangaggiya ba daga savo da kuskure wacce ta tabbatar da cewa shi ya samu nasara cikin mafi girman jihadi da yakar nafsul ammara, da kuma cewa shi cikin mafi yawan lokuta ya san hanyarsa da ingantaccen hadafinsa ya tafi kan wannan hanya.
Akwai kuma masu ganin cewa isma wani abu ne kawai da akai da'awa domin havvaka munafunci da kayata zahiri, saboda hakane zaka same su suna ta kokarin kwantar da hankalin masu aikata savo karkashin kafa musu hujja da cewa: shi fa savo wani abune da aka sanya shi cikin halittar dan Adam.
Mu dauki mafhumi mudlaki kan isma, sannan sai mu kalli yanda cikin gida yake sanya takura cikin rai …da yake lazimtawa masu imani da shi yin aiki da abinda ya dace tareda wannan mafhumi mudlaki, sannan kuma ta wata fuska zaka ga sun samu tsaruwa da daidaituwa a waje karkashin waccan mahanga mudlaka ga isma.. tabbas masu imani da isma idan muka kalli dukkanin dabaibayinsu da dangantuwarsu ta mutum ba zasu iya jujjuyawa ba a aikace da badinance tareda wannan yankakkiyar bukatar addini a cikin da waje, saboda haka wanne abu ne ya kamata su aikata tareda wannan tufaka da warwara mai cutar da ruhi mai yakar zuciya mai rusa hankali? Kai kace babu abinda ya rage sai riya da daukar dala babu gammo da havvaka kasuwar munafunci da almundahana da tsarkake kai na karya bda kayata zahiri da nuna zuhudu.
Ya kamata mu lura da cewa wannan bayani yana yakar katsalandan din hukuma cikin lamurran addini ga mutane, yana kudurce cewa lallai shi bai halasta ga hukuma ta yi katsalandan cikin fagen addinin mutane, da kutsawa cikin addininsu da imaninsu da dabi'unsu ba, wadannan muatne suna yada wani nau'I na addinin almaniyanci (raba addinin da hukuma) ko muce (secular system), kamar yanda suke imani da cewa shi savo voye yake cikin gundarin mutum, da kuma cewa kaddara wani mutum da baya aikata savo da yada hakan cikin jama'a wani abu ne da ya savawa daidai, domin mutum ya ksance cikakken mutum bawai remote control ba da bai iya juya kansa to dole ne a bashi damra aikata savo bisa dacewa da halittarsa da iradarsa, sai dai cewa kuma Sarkin muminai Ali (as) yana ganin mafi mhummancin hadafin hukumar muslunci shi ne gyara lamurran addinin mutane, daga cikin dalilansa na karvar halifanci sun kasance don kawo gyara da zartar da adalci. Daga wannan ne idan shugaba kan zartar da hukunce-hukuncen Allah ya ksance ma'asumi to a hankalce zai kasance ne mafi kammala da tasiri. raddi kan ba'arin masu inkarin isma zamu kawo ba'arin wasu nukdodi
A- ismar annabawa tana da wasu natijoji masu kyawu na makoma basu tabbatatuwa face ta wannan hanya, isma cikin karvo wahayi da isar da shi a matakin ilimi, kum tana sanya ma'arifa da tabbatacen farin ciki, hakika isma daga aikata savo-kari kan fa'idoji tana kama hannun mutum a matakin aiki ta sanya mutum samfuri kammalalle ga mutane da suka `yantu daga karshe daga tarkunan shaidan suka koma ga Allah. Hadafin kur'ani mai girma daga hakaito kissoshi misalin kissar Annabi Yusuf (as) shi ne wannan darasi ma'ana bayyanar da wannan hakika shi ne cewa hatta cikin karsashin samartaka da saukakuwar dukkanin damar aikata savo zai iya yiwuwa mutum yayui galaba kan nafsul ammara hakan na kasantuwa cikin taimakon Allah.
B- bai halasta mu din ga tunani da kaddara ma'asumai kamar matsayin wani inji da ake sarrafa shi ba, da suke tafiyar kan madaidaicin tafarki ba tareda wasiwasin Iblis ya bijiro musu ba, kuma suna tafiya zuwa ga hadafi domin mu fitar da natijar cewa sun banbanta da gamagarin mutane, bari dai gaskiyar magana shi ne cewa suma suna dauki ba dadi da sawwale-sawwalen shaidan sai dai cewa su suna fita daga wannan dauki ba dadi suna masu nasara daga wannan babban jihadi, bisa wasu riwayoyi hakika Annabi (s.a.w) yayi magana dangane da musluntar Shaidaninsa:
«لكنّ اللّه أَعانني عليه فأَسلَم».
Sai dai cewa Allah ya taimakeni kansa sai ya muslunta.
Wannan na nufin cewa baiwai kadai yayi galaba kan shaidan ba a'a kadai dai ya samu nasara kansa ya ja ragamarsa ta yanda shi da kansa yake yanke hukunci da kada ya afka cikin tarkon shaidan.
C- duk da kasantuwar shugabannin addini suna kwadaitar da mutane kan biyyya ga ma'asumai suna umrani da a riki annabawa matsayin ababen koyi garesu, sai dai cewa tareda haka suna karfafa wannan gava cewa lallai su basu kusanci annabawa ba cikin matsayi da mukami ba har abada, saboda haka lallai shi imani da fikrar isma baya haifar da takura a rai kan muminai daga cikin gida ko a waje, kuma bazai tava azabtar da ruhinsu ba , su ma'asumai sun gabaci sauran mutane cikin dukkanin kamala da falala mutumtaka, makusancinsu shbine wanda ya tafi kan hanyar da suke kai, sai dai cewa bai kamata gareshi yayi tunanin kusantarsu ba har abada, Imam sarkin muminai Ali (as) yana cewa:
: «ألا و إنّ إمامكم قد اكتفى من دنياه بطمريه٬ و من طعمه بقرصيه٬ ألا و إنّكم لا تقدرون على ذلك و لكن أعينوني بورعٍ و اجتهاد٬ و عفّة و سداد »
Ku saurara hakika imaminku daga duniyarsa ya wadatu da tsummokaran guda biyu daga abincin kuma ya wadatu da gutsiren gurasa biyu, lallai shi ya san cewa bazaku iya haka ba saboda haka ku taimakeni da yin tsantseni da zage dantse, da kame kai da daidaituwa.
Ma'ana dais hi bai nemi muminai da su kasance ma'asumai ba kadai dai abinda ya nema daga garesu shi ne su bi hanyarsu ta fuskanin kasantuwarsa waliyyan Allah, wannan aikai bawai kadai bai haifar da takura a rai ban cikin gida kan muminai bariu dais hi wata fitila ce da take haskaka hanyar gaskiya garesu.
4- kur'ani da ismar annabawa
Daga cikin batutuwa na daban da ake tattaunawa kansu shi ne samuwar wasu ayoyi da zahirinsu ke nuni kan ismar annabawa da kuma zarginsu kan ba'arin ayyukansu, wannan yananyin ya zo da sura mayalwaciya cikin litattafan riwaya da tasirida kalam an tattaunasu da fadin gaskiya, daga nan ne domin mu kai ga fahimtar zurfafar wannan mas'alar zamu wadatu mulahaza da tsokaci game gari.
A- lafuzza misalsalin (isyan) savo da (istigfar) neman gafar, nbai dace ace tayi tunbe da tasiri cikin kwakwalwa ba da kai tsaye zamu fassara su da sanannun ma'anonin da aka saba da su yau da gobe ba, wadannan lafuzza suna da wasu ma'anoni masu yalwa baus takaitu cikin haramu din shari'a ba, alal misali, hakika rashin aikata umarni ibadojin mustahabbi da na nusantarwa shima nau'I ne na savo; duk da cewa ba a daukarsa aiki na haramun ga wand abai bi wannan umarni ba, haka zalika lamarin yake dangane da lafazin istigfari da tuba wadanda kae fassara su da ma'noni masu kishiyintar juna, bisa kusancin mutum da matsayinsa ta yanda bawai akdai haramun ne a shari'ance ba kadai dai cikin ayyukan mustahabbi ma wadanda suke barinsu abain zargi ga makusanta to zamu iya kawo maganar istigfari da tuba da neman gafara, kamar yanda zunubi yak an zo da ma'anar aikin da karshensa yake da muni, akan wannan asasi ne, yakin da annabi (s.a.w) yayi kan bautar gumaka ake kirga shi zunubi ta fuskanin tunanin mushrikai, haika Allah a kare annabinsa mai girman daraja (s.a.w) daga mummunan sakamako bayan fatahu Makka kamar yand aya zo cikin kur'ani mai girma:
﴿إِنّا فَتَحْنا لَكَ فَتْحاً مُبِيناً * لِيَغْفِرَ لَكَ اللّهُ ما تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَ ما تَأَخَّرَ﴾
Hakika mun maka budi budi mabayyani*domin Allah ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da wand aya jinkirta.
B-bisa abin d aya zo daga riwayoyi, lallai daya daga cikin nukdodin maudu'in shi ne himatuwa cikin lafuyzzan kur'ani mai girma da cewa ba'arin wasu ayoyi sun sauka kan uslubin
«اياكِ اَعني واسمعي يا جارة» .
ke nake nufi kiji ya makwabciya.
Bisa gini kan wannan, tarteda kasantuwar manzo mafi karamci (s.a.w) shakka da kwakowanto basu bijirowa gareshi sakamakon kasantuywar wahayi daga samaniy, sai dai cewa kuma shi kur'ani mai girma yana magana da shi da kalmomi irin misalin
﴿فَإِنْ كُنْتَ فِي شَكٍّ مِمَّا أَنْزَلْنَا إِلَيْكَ فَاسْأَلِ الَّذِينَ يَقْرَأُونَ الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكَ لَقَدْ جَاءَكَ الْحَقُّ مِنْ رَبِّكَ فَلاَ تَكُونَنَّ مِنَ الْمُمْتَرِينَ﴾ .
Idan ka kasance cikion shakku daga abinda muka zaukar ka tambayi wadanda suke karanta littafi gabaninka hakika gaskiya ta zo maka daga ubangijinka kada ka sake ka kasance daga masu jayayya.
Sannan abu ne cewa wannan aya bata ishara zuwa ga cewa shakku na ribatar annabi mafi girmama (s.a.w) kadai dai kur'ani mai girma na budewa babin bahasi da tahkiki da bincike ga wanda yake magantuwa da su karkashin wannan uslubi, yakna kuma neman su da su kawar da shakkunsu daga tambayar malaman yahudawa da fada-faddan kiristoci wadanda suke da cikakken sani na yakini kan siffofin annabi cikamaki, cikin wata ayar zaka samu Allah yana zargin manzonsa mafi karamci (s.a.w) sakamakon amsa bukatar masu raunin imani da yafe musu tarayya cikin jahadi
﴿عَفَا اللّهُ عَنْكَ لِمَ أَذِنْتَ لَهُمْ حَتّي يَتَبَيَّنَ لَكَ الَّذِينَ صَدَقُوا وَ تَعْلَمَ الْكاذِبِينَ﴾ .
Allah ya yafe maka daga abinda ka basu izini har sai wadanda suka gasgata sun bayyanar maka ka kuma san makaryata.
Sabaoda haka cikin kankanuwar lura da fadakuwa da sannu zai bayyanara mana cewa zargin da ya zo cikin ayar mai girma ya karkata ne ga wadanda suke janye jiki daga jihadi da raunanan uzurori, suna amfani dasu matsayin shinge don su gjhewa yaki su zauna a gidajensu, da keta alfarmar da'a ga umarnin manzon Allah (s.a.w) kari kan haka lallai ko da ma wadannan masu raunin imani sun zo sun halaraci fagagen daga babu abinda halartarsu zayta kara face raunana karfin gwiwar sauran mayaka, kamar yanda ya zo cikin aya mai zuwa cikin wannan suara dai-sannan da sun tunkuda al'amura zuw aga tavarvarewa da hasara, abinda ya zo cikin wanann aya tabbatar da akasin abinda wasu ke kudurcewa-bawai kawai bata nuni zuw aga zargin manzon Allah (s.a.w) ba bari dai ma yabonsa take yi cikin zirin zargida tona asirin lamarin masu savo, hakika amsa bukatarsu bai katangesu daga tonuwa da bayyanar munafuncinsu bada riyarsu.
C- abinda muka ambata zuwa yanzu bai kore yiwuwa abinda ake kira (tarkul aula) barain ya kamata daga garesu ba, lallai misalin kananan lamurraan bayyyanar da su cikin kur'ani mai girma da fuskanin da ya tunkuda masu saukakkan tunani zuw aga shakku da bjiro da ire-iren wadannan tambayoyi: idan ya kasance annabawa ma'asumai ne menene ma'anar danganta ire-iren wadannan lamurra zuwa garesu? Imam sarkin muminai (as) yana bada amsara wannan tambaya cikin bijiro da wannan nukda shi ne cewa ambaton wadannan aibobi ya kasance ne don gudun kada hujjojin annabawa su girmama cikin kirazan al'ummunsu ya kai ga sun ajiye su a mahallin Allah kamar yanda nasarawa suka aikata da Isa dan Maryamu, sai kur'ani ya kawo don nuni kan kamalar da Allah kadai ya dayantu da ita. A hakika irin wannan nau'I da kur'ani ya cika da shi zai taimakawa musulmi wurin kauracewa guluwi da wuce gona da iri kamar yanda nasarawa suka aikata ta yanda suka Allantar da annabinsu,lallai wannan ya tuke cikin kafirci mai girma.
D- ta yiwu mu samu ba'rin wasu ayoyin kur'ani mai girma sunyi amfani da Kalmar (zanbu) da misalsalansu kan ba'arin wasu annabawa, sai dai cewa ya zama dole mu fadaka da lura da cewa abinda ake nufi da wadannan kalmomi bai kasance savo ba da kura-kurai da muka saba da su yau da gobe, ma'ana ketare shari'a, a'a wani abu ne daban shi annabi bai tabbata yana aikata hatta makarauhi ba ballantana haramun, haka y askance ne karkashin ka'idar (kyawawan ayyukan rabautattu munana ne gurin kusantattu) tareda karin bayani zamu ga cewa shi zunubi yana da fuskoki uku: {zanbul kanuni} savawa shari'ar Allah, {zanbul Akhlaki) mummunan gurbi da yake wanzuwa kan ruhin mutum, koda kuwa wanan aiki bai askance daga haramun ba shari'ance, {zunubi cikin mukamin masoyi kan masoyinsa}wanda shi bai daga savawa shari'a baui kum a lazimta fadawa cikin munanan halaye, sai dai cewa shi laifi da bai dace da matsayin soyayya ba, da yawa-yawan abubuwan da kur'ani ya danganata su ga ma'asumai da mutane gamagari suke musu kallon laifi sun ksance daga fuska ta uku, ma'ana su waliyyan Allah ma'asumai sakamakon kasantuwarsu kan mukamin madaukaki cikin soyayyar Alla, allai abinda wannan mukami yake hukuntawa shi ne cewa su sadaukar da dukkainin himmarsu zuwa ga abin bautarsu, kadai su karjkatar da dukkanin himmatuwarsu zuwa ga wanin Allah, kana wannan asasi ne ya zama lallai takaitawa cikin wannan mukami ake kirga shi garesu matsayin savo, tabbas bawai savo bane a hakikarsa da ya cancanci azaba da ukuba ko kuma haramtuwa daga shiga aljanna, kadai dai yana yin tasiri da cutarwa cikin mukamin kariyarsu masoyinsu garesu da kulawarsa ta musammam garesu, sai ya zamanto sun nesantu daga gareshi gwargwadon abinda suka aikata.
Ta wata nahiyar kuma lalai ita rayuwar duniya tana da nata hukunce-hukuncen, suna iya kasancewa wajibi a shari'ance da dokance a wasu lokuta, misalain auare, abinci, tarayya cikin jihadi da yaki, wadannan lamurra wazifofi ne na wajibi a muhallinsu wajibi a sauke s, sai dai cewa da gwargwadon muhimmancinsu suna rage cikakkiyar karkatar mutum zuw aga ubangijinsa, wannan wani lamari da yake sanya mutum ya dinga jin ya aikata zunubi ga kusantattu, saboda haka hatta mafin girmamar annabawa da mafi kusancin bayi zuwa ga Allah ba zai tava yiwuwa su kuvuta daga zunubi ba, duk da cewa wadannan zunubai sun sha banban da ma'anar savon Allah a shari'ance da dokance cikin kyawawan halay, lllai shin savoy a kevantu cikin zawiyyar dokokin shari'a., sai wannan zawiyya ta fadadu ne zata tattaro dokokoin Akhlak, tabbas ma'asiya ba zata tava tattaro zunubinn da yake tsakanin masoyi da masoyi ba.
Saboda wannan dalilibazai yiwu ace kur'ani mai girma ya danganta aikata savo ga annabawa ba, lallai hakan yana cin karo da ismarsu, abinda zai jawo watsi da akidar ismar kwatakwata, saboda haka lam,arin yana bukatar dogon tunani da lura da fadaka cikin kur'ani da yin tawilin wadannan ayoyi.
5- Isma da istigfari
Tsawon tarihi kuka da neman gafarar da A'imma ma'asumai (as) ya ksance wani lamari mai muhimmancin gaske da yake baiwa mabiyansu mamaki gaske, ana kidaita wannan lamurra daga cikin falalolinsu madaukaka, lamarin da hatta ya kaiga daya daga cikin malaman yahudawa Yahaya bn Zakariya ya samu yabawa da wannan wannan kevantacciyar falala wato (yana kuka ba tareda aikata zunubi ba), sarkin muminai (as) cikin amsa kan haka yana cewa: hakika hakan ya kasance ga manzon Allah muhammad (s.a.w) an kuma bashi abinda ya fi hakan falala, lallai Yahaya bn Zakariya ya kasance a zamanin da babu bauatar gumaka babu jahiliya.
Muhammad (s.a.w) an bahsi hikimada fahimta tun yana karamin yaro tsakankanin masu bautar gumaka da rundunar shaidan, bai tava kwadaitar musu da bautar gumaka b, bai tava tarayya cikin bukukuwansu ba, ba a tava samunsa da yain karya ba, ya ksance amintacce mai gaskiya mai hakur, ya ksance yana lazimtar azumin sati-sati, sai aka tambayeshi kan hakan sai yace: nib a daidai nake da dayanku ba, lallai ni ina yini wurin ubangijina sai yake ciayar dani ya shayar dani, ya kasance yana kuka har dardumarsa ta jike da hawaye sabaoda tsoran Allah azza wa jalla ba tareda kuma ya aikata kowanne irin zunubi ba.
Hakika wannan kuka da istigfarin da imaman shi'a suke yi ya sanya wasu yin tunanin inkarin ismarsu, alal misali daya daga cikin marubuta a wannan zamani yayi rubutu kan inkarin isma yana mai cewa: dole ne aka zurfafa fahimta da sanya hankali cikin batun isma da kuma karvar nazari da tunani kan cewa babu wani mutum da baya aikata savo ma'ana babu wani mutum ma'asumi, kowa da kowa yana dauki ba dadi da wasiwasin shaidan, kowanne mutum yana da iyakarsa kuma tawaya na bijira kansa, lallai lazimtarsa cikin iyakantuwa ya sanya shi kowanne lokaci yana fadi tashi da neman daukaka a zatinsa, hakika annabwan Allah sun rayu da yanayin mai dorewa cikin kalubalen dabi'u da ma'anawiyy, sun ksance cikin jihadi da dako da dauki ba dadi, annabinmu Muhammad (s.a.w) ya kasance yana fadin cewa a kowacce rana yana istigfari da tuba sau dari daya
[«إنّه ليران علي قلبي و إني لاستغفر اللّه كل يوم مائة مرة»،
Lallai yana tsatsantuwa a kan zuciyata lalai ni ina neamn gafara sau dari a kowacce rana.
Bisa yadda bayanin ya zo kara daga ayayar kur'ani muanzon Allah (s.a.w) ya ksance yana da wasu zunubai da suke bukatar neman gafararsui da tuba, manzon Allah (s.aw) da Imam Ali (as) da iam Husaini (as) sun kasance suna magiya da neman gafara wajen ubangijinsu suna munajati da dukkanin kunan zuciya da radadi, sun kasance suna ikirari da zunubans, dukkanin hakan bai kasance bijirarren aiki ba gaban wasu, sun kasance a hakikance suna jin cewa sun aikata zunubi, suna tsarkake zuciyarsu, saboda haka sanannen lamari ne ace mutum ya aikata zunubi, shi zunubi wani abu da yake da asali cikin mutum bazai tava yiwuwa bay a wofita daga gareshi, saboda haka babu bukatar kaddara wannan tsarkaka ta karya da nuna zuhudanci, bisa ra'ayin mawaki ba'iraniye Hafiz Shirazi: idan ya kasance mun sumantu da walkiyar savo* to ina mu iana da'awar ma'asumanci.
Jumlolin da aka kawo a sama kalmomi ne na gaskiya da aka nufi vata da su, natija shi ne baus da sakamako mai kyawu, na'ama mu ma mun sallama cewa lallai kowa da kowa yana dauki babu dadi da wasiwasin shaidan, sai dai cewa munyi imani da cewa su ma'asumai suna fitar daga wannan dauki babu dadi cikin nasara a kowanne lokaci ba tareda shaidan yayi galaba kansu ba, hakika ma'asumai sun kasance cikin gwagwarmayar tsaftace dabi'u da badini sai dai cewa cikin taimakon ubangiji kafarsu bata tava zamewa ba.
Eh muma mun yarda da wannan nukdar cewa (kunan rai da magiya cikin munajati da Allah bawai suna yi don nunawa mutane yadda ake ganawa da Allah ba bari dai sun ksance hakika suna jin cew asuna aikata zunubi) babban malamin Addini Allah ya jikan rai Arbili wanda yayi wafatai 692 hijri yana daya daga cikin wadanda suka karfafa wannan hakika, hakika albarkacin Imam Musa Alkazim (as) na lura da wannan hakika na kai ga gano cewa zunubin da ma'asumai suke ikirarinsa don gyarawa baya daga aikata abubuwan da Allah ya haramata aikata su, sakamakon cewa wanda isa ga kusanntar fada da hallarar ubangiji yana daukar ma kansa ma'auni mafi dandaka cikin auna kurakuransa, sai ka same shi yana daukar abinda yak e gama gari na wurin sauran mutane a matsayin zunibi a wurinsa, alal misali me yafi yawa daga mutane da basa jin komai basa jin kunan zuciya da radadi yayinda sallar wajibi ta shude suka yi kara'inta, mutum nawa ne suke jin kunan rai da radadi yayinda basu yi sallolin nafila ba, da dai suaransu, duk sanda masoyin Allah ya karu cikin sanin ubangiji da kaunarsa sai ya dinga ganin nauyaya abinda ke wuyansa, zak asmeshi yana ta fadaka da ikirari da takaitawa cikin sauke wajiban da suke wuyansa kan bautar ubangijinsa yanda ya dace da sha'anins- zamu kawo karshen zancenmu da maganar Arbiliwanda yayi bincike da lura gameda abinda ma'asumi yake daga zunubi daga wata zawiya ta daban.
Abinda ya rubuta shi ne cewa lallai sun annabawa da A'imma (as) sun sadaukar da dukkanin lokutansu cikin ibadar Allah zukatansu cike suke da tunawa da shi, a koada yaushe suna cikin taka tsantsan kamar yanda sarkin muminai (as) ya fada:
«اعْبُدِ اللَّهِ كَأَنَّكَ تَرَاهُ فَإِنْ لَمْ تَرَهُ فَإِنَّهُ يَرَاكَ
Ka bautawa Allah kamar kana ganinsa idan kai baka ganinsa hakika shi yana ganinka.
Su koda yaushe suna fsukanta zuw agareshi ne sun nufe da dukkanin smauwarsu, duk sanda suka yi sako-sako daga wacan marataba da madaukakin matsayi zuwa karkata bda kayan ci da sha da mika wuya zuwa kusantar mata daga ayyukan halaliya sai su kirga hakan daga zunubi ko kuskure sai ka samesu suna neman gafara daga aikata hakan, ashe baka ba'arin bayin mutane ba da zasu zauna suci su sha su kusanci mata alhalin sun san cewa suna gaban idon ubangidansu to lallai hakan zai kasance abin zargi wurin mutane za a kirga hakan takaitawa cikin sauke wajibin ubangidansu, to me kake tsammani daga ubangidan dukkanin uwayen gida mamallakin mamallaka, zuw aga wannan nukda ne amincin Allah ya kara tabbata gareshi yayi ishara
«إِنَّهُ لَيُرَانُ عَلَى قَلْبِي وَ إِنِّي لَأَسْتَغْفِرُ بِالنَّهَارِ سَبْعِينَ مَرَّةً»،
Lallai zuciya ta tana tsatsa lallai ina neman gafara sau dari a kowanne yini.
Lafazin saba'in yana komawa ga adadin istigfarin da yake ba wai ga tsatsar ba, da fadinsa:
«حَسَنَاتُ الْأَبْرَارِ سَيِّئَاتُ الْمُقَرَّبِينَ
Kyawawan ayyukan rabautattu muna ne a wurin makusanta.
Takaice wannan fasali
1-mafi muhimmancin hanyar sanin annabawa shi ne gangarowar mu'ujizozi daga garesu da busharar annabawan da suka gabace su, dalili ne da ake kafa hujja da shi bisa bukatuwa zuw aga wahayi da kansa shi nykae karfafa larurar kuvutarsu daga aikata kuskure, annabwa ma'asumai ne cikin karvo wahayi da isar da shi da bayaninsa, ismarsu cikin ludufin Allah tana faraway tun suna kananan yara.
2-Har abada shi ma'asumai baya tunanin aikata zunubi albarkacin ilimin da yake da shi da karfaffar iradar da Allah ya ni'imta shi da ita wacce take da asalai cikin tanadinsu na irada, ismar annabawa ta tattaro fa'idoji savanin abinda wasu ba'arim ke fadi-hakika bata azabtar da ruhin mumini da lamirinsa.
3-akwai amsoshin hankali ga dukkanin abinda ake dangantawa ga ma'asumai daga savo na zahiri da istigfari, himmatuwa da ma'anar asalin kalma da samuwar hadafin tarbiya da taka birki kan Allantar annabawa, da barin abinda yafi kamata da aikata zunubai na barin kyawawan dabi'u ko kuma zunubi a mukamin soyayya na daga jumlar dalilai da suka sanya danganata zunuban zahiri zuw aga annabawa cikin kur'ani mai girma, shi istigfarin ma'asumai yana daga babin (kyawawan ayyukan rabautattu munana ne ga makusanta).
Karin Masdarorin mudala'a
1- Tanzihul Anbiya'u wal A'immati-Shariful Radi
2- Almizan fi Tafsirul Kur'an-karkashin bayanin ayoyin da suka ta'allaka da ismar annabawa-Muhammad Husaini Taba'taba'i. bugun Kum Mu'assasatu Isma'iliyan 1392 hijiri.
3-Majma'ul bayan fi Tafsirul kur'an-karkashin bayani kan ayar isma annabawa, bugun Darul Ihya'aul turasul Arabi, 1379 hijri.
4- Nubuwat dar kur'an- Muhammad Jawadi Amuli, bugun kum Isra', 2002 miladi.
5- Ma'arifatul dalil- Misbah Yazdi bugun Tehran 1996 miladi
6- Tanzihul Anbiya az Adam ta katam- Muhammad, kum nabug 1374 shamsi.
Daga cikin tambayoyin wanna sashin ()
- WANENE YA FI HATSARI TSAKANIN NAFSUL AMMARA DA SHAIDAN?
- IMAM HASSAN ASKARI DA TALAKAWA
- SIRRIKAN ARAFAT
- Bahasul karij: Fikihu zama na (103) kashi (1)
- Hakuri kan mutuwa `da daga cikin Kur'ani mai girma
- TUFA barbeloli masu yawan gaske sun sauka kan wata qatuwar bishiya, sannan iskar ta kasance iskar kak
- Yanzu ba zaku yi duba zuwa ga Rakumi ba yaya aka halicce shi_ ina fuskar kamanceceniya
- KARIJUL FIKHU 7 GA RABIU AWWAL SHEKARA 1441, KAN MUSTAHABBANCIN BAYYANARWA CIKIN AZUHUR DA LA’ASAR
- DAGA ZANTUKAN IMAM MUHAMMAM BAKIR A.S
- Abuta ko qawance