lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Ma'anonin hankali

Sannan shi ilimi da ma'arifa kamar yanda ya gabata suna daga abubuwa guda daya da suke da dab banbantuwa a kankin kansu ma'abota martabobi, wannan na daga abin da ya haifar da sassabawar mutane cikin hankulan su da mariskan su da tunanunnukan su da ra'ayoyin su, haka lamarin yake cikin hankali, mutane ba kudin goro suke ba, ba bai bai daya suke ba cikin hankulan su da ababen da hankalinsu yake riska kai hatta cikin ma'arifofinsu.

Hankali yana da ma'anoni daban-daban ta fuskanin daban-daban

Hankali (Akalu) a luggance: ya samo asalin daga igiyar da ake yiwa Rakumi dabaibayi da ita a kafa yayin da ake durkusar da shi kasa wanda hakan yana nuni da daure shi tamau ta yanda ba zai iya kwacewa ba.

Kamar yanda ya zo cikin littafin Mufradat Ragib: {Akalu} ana kiransa da matsayin wani karfi da yake tukewa don karbar ilimi, ana kiran ilimin da nutum ke fa'idantuwa da shi da hankali, saboda haka nema sarkin muminai Ali (a.s) ya ce:

 (العقل عقلان مطبوع ومسموع ـ ولا ينفع مسموع إذا لم يكن مطبوع)

Hankali kashi biyu ne akwai wanda ake tantancewa da shi, da kuma wanda ake ji da shi-wanda ake ji bai da wani amfani idan bai kasance tare da na tantancewa ba.

 kan na farko ma'ana hankalin tantancewa manzon Allah (s.a.w) ya yi ishara da fadinsa:

(ما خلق الله خلقاً أكرم عليه من العقل).

Allah bai halicci wata halitta ba mafi karamci daga hankali ba.

Sannan kan na biyu ma'ana wanda ake ji ya yi ishara da fadinsa:

 (ما كسب أحد شيئاً أفضل من عقل يهديه إلى هدىً أو يردّه عن ردى).

Wani mutum bai tsiwirwiri wani abu ba mafi falalan daga hankali yana shiriyarwa zuwa shiriya ko kuma ya kubutar da shi daga halaka.

Wannan da ma'ana ta biyu shi ne ma'anar fadin sa madaukaki:

﴿وَتِلْكَ الأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ وَمَا يَعْقِلُهَا إِلاَّ الْعَالِمُونَ﴾

Wadancan misalai ne da muke buga su misali ga mutane babu masu hankaltar su sai masu ilimi.

Haka yazo cikin suratul Ankabut:

 ﴿وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنْكَبُوتِ﴾.

Lallai mafi raunin gidaje shi ne gidan gizo-gizo.

Dukkanin wuraren da Allah yake zargin kafirai da rashin hankali to ishara ce zuwa kan na biyun bana farko ba:

﴿وَمَثَلُ الَّذِينَ كَفَرُوا كَمَثَلِ الَّذِي يَنْعِقُ﴾

Misalin wadanda suka kafirce kamar misalin wanda yake yin me!me! ne.

Zuwa fadinsa madukaki:

 ﴿صُمٌّ بُكْمٌ عُمْيٌ فَهُمْ لا يَعْقِلُونَ﴾

Baibaye Kurame Makafi su basa hankalta.

Kafiri yanada hankalin dabi'a wanda da shi ne Allah ya kallafa masa wazifa da kuma shi zai masa hisabi, koma bayan hankalin ji wanda shi ilimi ne mai amfani ga wanda ya san shi ya kuma yi aiki da shi, sannan duk wurin da aka dage alkalami sakamakon rashin hankali da yake da shi to ishara ce zuwa ga farko.

Asalin hankali a luggance shine kamewa da damkewa, kamar dabaibaye Rakumi da dabaibayi, ana cewa mace ta daure gashinta ko ace ya yiwa bakinsa takunmkumi (Akkala lisanahu kaffahu) ko (Akkalatil mar'atu sha'araha) dss…

Hankali a isdilahance suna da ma'anoni masu banbanci da juna gwagwadon sassabawar isdilahohi, hankali a cikin isdilahin ilimin fikihu da usul ya saba da ma'anar hankali a isdilahin ilimin falsafa da mandik, haka dai kamar yanda ya zo cikin tafsirai da madaukakan hadisai.

Ya zo cikin hikima muta'aliya: da gundarin jauhari wanda yake cikin gangarowar ayyukan mutum karkashin zabin sa wanda sababin sa ne mutum yake bukatar karfin kayan aiki na zahiri da na badini da hawasul Ashara kamar yanda bayani ya gabata a muhallinsa.

Wurin ba'arin Arifai sun yi bayanin hankali a matsayin haske na ruhi wanda da sababinsa nafsu ke samun idraki da riskantattu, an ce da hankali a ke riskar kulliyat abin da yake kara kyawuntar tunani da zurfafar sa da kyawuntar tafiyarwa da gudanarwa, da istinbadi da da neman alfanu da tunkude cutuwa ga kankin kan mutum da sauran jama'a cikin al'amura na madiya da ma'anawiya, da tantance zance daga daidaituwa da kuskurewa hakama daga gaskiya da karya da bata da shiriya, da tanadin don karbar ilimummukan nazari da tafiyar da sana'o'i da cigabantar da su da habbaka su da dai makamantan haka.

Kashe-kashen hankali:

Sannan ka sani nafsun mutum tana da hankula guda biyu: hankalin nazari shi ne wanda ya ta'allaka da abin da za a iya sani, sai kuma hankalin aiki wanda ya ta'allaka da aiki da abin da za a aikata.

Kamar yanda nafsu take da martabobi da matakai da ake nadewa masu tari yawa kuma tana da martaba d atake ayyanuwa a kebance da kebantaccen suna tsakanin ayyanannu.

Hankalin nazari yanada martabobi hudu:

Na farko: tanadi domin neman hankaltau na farko ta hanyar mariskai biyar wanda ake kira da (akalul hayulani).

Na biyu; tana tanadi domin samun nazariyoyin hankali daga hankaltau da sanannu na fari-fari saki babu kaidi nbabu banbanci cikin kasantuwar su daga hanyar mariskai ko kuma tunani, shi ne abin da ake kira da (al'akalu bil malaka).

Na uku: tanadi domin halarto da nazariyoyi da aka tsiwirwira cikin kowanne lokaci ya so wadanda ake kira da (ala'akalu bil fi'ili).

Na hudu: canji abin da yake da tanadi da karfi nan gaba zuwa nan take, ma'ana karar da tanadi da nan gaba da halarto da tsiwirwirarrun ilimummuka da mushahada, wanda ake kiransa da (akalul mustafad)

A wani fadin cikin jumla shi ne cewa: shi hankali nazari ko dai cikin martabar nan take tsantsa ko kuma cikin martabar tanadi da zia karba nan gaba, shi ne ko dai nna kusa ko tsakatsaki ko na nesa, na farko: akalul mustafad, na biyu: akalul fi'il, na uku: akalul malaka, na hudu: akalul hayulani.

Amma martabobin hankalin aiki to guda hudu ne:

Na farko: tsarkake zahiri da amfani da ladubba cikin dabbaka koyarwar muslunci da hukunce-hukunce addini da shari'a, wadanda ake kiransu da: attajaliyatu.

Na biyu: tsarkake badini daga munanan dabi'u da siffofi marasa kyawu, wanda ake kira da: takliyatu, sai dai cewa abin da ya shahara kamar kuma yanda yake shi ne ra'ayinmu ita takliyatu cikin mukamin hankalin aiki tana gabatuwa kan ragowar martabobin.

Na uku: yiwa zuciya ado da falaloli da kamaloli da kyawawan dabi'u, shi ne abin da ake kira da : tahalli.

Na hudu: kaiwa zuwa ga mukamin fana'i cikin zatin Allah da wanzuwa tare da shi, sai ya zamanto iradarka ta kare ta narke cikin iradar Allah matsarkaki, babu abin da kake so sai da abin da Allah yake so, sai ka narke ka kare cikin hasken sa da kyawawan sunayen sa da madaukakan siffofin sa masu tajalli cikin shimfidaddiyar samuwa ta hakika, matsayi cikin kausul nuzuli zuwa duniyar nasutu cikin halittar Allah cikin littafin sa kur'ani mai girma cikin mafi daukakar halittun Allah Muhammad (s.a.w) da iyalan sa tsarkaka.

Babu kokwanto cewa ya zama dole cikin kashafin tabbatattun abubuwa da shuhudinsu da sanin juzu'ai da samun ilimi kan kulliyat dole ace hankali ya kasance jagora wanda shi ne tsantsar hankalin tsaftatacce daga dukkanin datti cikin kagar samuwar mutum cikin rayuwarsa tare da dukkanin sasanninta da fagagenta, lallai yanda lamarin yake shi ne da hasken hankali da kasantuwa tare da shi launukan tabbatattun abubuwa ke banbancewa a fara jin kasmhin dandankewa daga gareta, ruhi ya kyawunta ya kammala da saninta har ta kai ga tsololuwar kamaloli kofar kausi biyu ko mafi kusa daga haka.          

اللهم أرزقنا عقلاً کاملاً ولبّاً راجحاً وقلباً زکيّاً وعزّاً باقیاً وأدباً بارعاً وعملاً کثيراً وإجعله لنا ولاتجعله علينا برحمتک يا أرحم الراحمين.

Ya Allah ka azurtamu da kammalallen hankali da tunani mai rinjaye da zuciya tsarkakka da izza madawwamiya da adabi mai kyawu da aiki mai kyawu, sannan ka sanya shi garemu ka da ka sanya shi kanmu da rahamarka ya mafi jin kan masu jin kai.


Tura tambaya