lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Addinin musluinci shugaba ne na har abada

Ya kai mai karatu mai daraja: ka sani lallai su hukunce-hukuncen hankali da na shari’a kadai dai su suna biye da maudu’ansu ne cikin samuwa ko rashi, cikin adadi da kaifiya (yanayi), da dukkanin abin da yake kewaye da su daga lawazim da sabubba da suka ta’allaka da zamani da wuri da yanayiyyika, lallai hukunci yana caccanjawa da caccanjawar maudu’i, idan ya kasance daga masadir din fikihun muslunci na nazari da na aiki da hankali da siratul ukala’u matukar dai ba kasance akwai wani tsawatarwa da taka birki daga Allah matsarkaki ba, to lallai abin da yake lazimta shi ne kowanne irin cigaba na hankali cikin jama’ar mutane da ake samun nutsuwa cikin kasantuwarsa mai cika haduffa da manufofin shiriya da azurta mutum to lallai shi ana kidaya shi daga abubuwan da shari’a ta laminta da su, wannan shi ne abin da yake shiriyarwa a bayyane kan cewa shari’a mai tsarki ba ta togace iya cikin ibadoji ba da ayyukan addini, bari dai tana tattaro mu’amaloli da sura gamammiya wacce fakihi wanda ya cika sharudda ke istinbadinsu daga masadir din shari’a.

Sannan lafazin (Shari’a) da (Shar’u) a luggance: yana da ma’anar korama da take hade da gabar tafki..

﴿إِنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللَّهِ الإِسْلامُ﴾ (آل عمران: 19)

 

Addini a wurin Allah shi ne muslunci.

 

Da ma’ana gamammiya ga dukkanin shari’o’i da manhajoji da risalolin sama, shi tafkin shi ne addini da baki dayan cikarsa, shari’o’i suna matsayin koramu da suke kaiwa ga addini gwargwadon hukuncin zamani da wuri.

 

 ﴿لِكُلٍّ جَعَلْنَا مِنْكُمْ شِرْعَةً وَمِنْهَاجاً﴾ (المائدة: 48)

 

Ga kowanne daga gareku mun sanya shari’a da hanya.

 

Shari’o’in sama kamar misalin shari’ar Musa da shari’ar Isa da shari’ar Muhammad (s.a.w) kadai dai su koramu ne masu gudana matukar dai ba Ai nasakinsu ba (Shafewa da zuwa da wata shari’ar sabuwa) cikin kowanne irin zamani da wuri duk wanda ya kasance cikin hanyar wadannan koramu da abin da Alah ya yi umarni da shi lallai shi zai amfanu cikin rayuwarsa ta yau da kullum da rayuwarsa ta lahira, amma sassabawar shari’o’in sama lallai su suna daidaita da zamani da wuri kamar yanda suke cikin tafiyarsu ta kammaluwa hakika shari’a ta fara kammaluwa tun daga Adamu har zuwa kan cikamakin annabta da risalal muslunci Muhammadi na Asali

﴿وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإِسْلامِ دِيناً فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ﴾ (آل عمران: 85)

Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za a taba karba daga gare shi ba.

 

 ﴿الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمْ الإِسْلامَ دِيناً﴾ (المائدة: 3)

Yau ne na kammala muku addininku na cika muku ni’imata kanku na yardar muku muslunci addini.

 

﴿قُلْ فَأْتُوا بِكِتَابٍ مِنْ عِنْدِ اللَّهِ هُوَ أَهْدَى مِنْهُمَا  ـ من القرآن والتوراة ـ أَتَّبِعْهُ إِنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ ﴾ (القصص: 49)

.

Ka ce ku zo da littafi daga wurin Allah wanda shi yafi shiriya daga gare su biyun-kur’ani da Attaura-zan bishi in kun kasance masu gaskiya.

 

Wannan na daga abin da yake shiriyarwa kan cewa abin yiwa biyayya da shari’a ta gaskiya ya zama dole su kasance mafi falalar hanya da tafarki da siradi mikakke cikin zamaninsa, bai halasta ayi biyayya ga wahamai ba da tatsuniyoyi da hiyalai da bidi’o’i da bata ba, sannan ace mu ajiye dalili da tabbatattun abubuwan shari’a a gefe guda muyi watsi da su.

sannan kamar yanda jikin mutum yake kammaluwa da cin abinci da shan ruwa tare da sabawar nau’o’insa da sinfinsa haka ma ruhi mutum yak, lallai ruhi murakkabi daga sinadari biyu na asasi: ruhi da gangar jiki, na farko wato ruhi daga sama yake da duniyar Malakut na biyu kuma gangar jiki daga kasa yake duniyar Nasutiya, abu na farko da yake abincin ruhi shi ne addini da mazhabar gaskiya, lallai shi yana amintarwa mutum da cimakar ruhi domin ya kammala ya habbaka ya kai ga zuwa shiriyarsa ya zuwa kololuwar kamalarsa da kyawuntarsa wanda shi ne halifantar Allah matsarkaki cikin sunayensa da siffofinsa, da kuma dabi’antuwa da halayen Allah Azza wa Jalla, da kuma komawarsa zuwa ga ubangijinsa mahaliccinsa yana cikin lafiya da yarda yana yardajje

 

﴿ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً﴾ 

 

Ki koma zuwa ga ubangijinki kina mai yarda yardajjiya.

 

﴿وَنَفَخْتُ فِيهِ مِنْ رُوحِي﴾ (الحجر: 29)

Na yi huri cikinsa daga ruhina.

 

An danganta zuwa ga Allah don daukakawa.

Idan ya kasance cikin cimakar gangar jiki daga cikinta akwai abin da yake  mai amfanarwa da kuma mai cutarwa, ma’anar me cutar da gangar jiki, to haka zalika ruhi, wani lokaci zaka ciyar da ruhinka da abu mara kyawu kamar zunubi da sabo sai su cutar da ruhin su kashe shi kamar misalin guba, daga cikin cimakar akwai mai amfanar da shi kamar siffofi ababen yabawa da ayyuka nagargaru, bayanin haka kadai yana cikin addini da shari’ar Allah da kuma hukuncin lafiyayyen hankali da dayantacciyar tsarin halitta mai kauna ga kyawu mudlaki, wajibi kan dukkanin musulimi da musulma da farko su san addininsu da abin da yake cikinsa daga Akidu Akhlak da mas’auliya da wazifofi da hukunce-hukunce sannan ka da su takaitu da iya neman ilimin addini kadai, na biyu dole ne su nemi fahimtarsa da fuskantarsa, su kasance masu sanya hankali da basira da kammalallen wayewa da fadaka.

Na uku: dole a dabbaka abin da aka koya.

Na hudu: bai buya ba cewa mutum yanada marhaloli guda uku na samuwa, da suke sabawa da sassabawar martabobinsu da lawazim dinsu da abubuwan da suka ta’allaka da su.

Na farko marhalar hankali da zurfafa tunani wacce itace mafi daukakar marhaloli da martabobi kuma da ita mutum yake fifita da banbanta daga dabbobi da tsirrai da daskararrun abubuwa ya kasance mafi daukakar halittun Allah matsarkaki.

Na biyu: marhalar karkata da garizozi da soye-soyen rai, cikin ba’arinsu suna tarayya da ba’arin wasu dabbobi, kamar garizar son jima’i da garizar ci da sha.

Na uku: marhalar gangar jiki da gabbai da gabobin waje kamar hannaye da idanuwa guda biyu.

Na hudu: lallai takalifin Allah cikin umarninsa da haninsa kan mukallafai kadai dai ya kasantu da la’akari da marhalar farko, lallai dabbobi bi ma haka, haka zalika ma kan wanda yake da larurar rashin hankali hakika ya fita daga cikin da’irar taklifin Allah.

Sannan shi ma’abocin hankali azurtacce shi ne wanda yake daga marhaloli ta biyu da ta uku karkashin jagorancin da hukumar marhalar farko, kamar yanda shi taklifi da mukallafi suna tabbatuwa da la’akari da marhalar farko, lallai shi hankali sharadin takalifi ne.

Amma dabbobi wanda su kwata-kwata basu da hankali hakama mahaukaci to su sun fita daga farfajiyar takalifi da shari’a, sai dai cewa cikin duniyar halitta lallai babu wani abu face yana tasbihi da godiyar ubangijinsa.

Amma addini, to yanada da ma’anar hanya ne (gareku addininku nima gareni addini na) babu kokwanto cewa addinin sama ya zo don tarbiya da koyar da mutum da raba shi da jahilci da tsiyata domin ya kai ga kololuwar ilimi da azurta, da kammaluwa da daidaita marhaloli uku ba tare da takaitawa ba da wuce goda da iri.

Kan asasin cewa wadannan marhaloli suna kasantar da addini cikin mafhumansa da marhalolinsa da dabbakuwarsa daga abubuwa uku, Akidu Akhlak Ahkamul shar’iyya, bai buya ba cewa mutum ya kasantu daga halittunsa daga hankali da gangar jiki da ruhi, amma shi hankali: shi ne masaukar akidunsa, shi ne wanda aka kallafawa tabbatuwa da tabbatarwa

Amma ruhinsa: shi ne fagen sulukinsa da Akhlak dinsa, sannan Akhlak ke tarbiyantar da ruhinsa, amma gangar jikinsa: sai ilimin fikihu ya dau nauyin koyar da shi.

Cikin hadisin annabi ishara ta zo kan wadannan ilimummuka da suke amfanar da mutum cikin rayuwarsa da bayan mutuwarsa, sannan matukar bai nemi saninsu ba lallai zai cutu, lallai suna daga ilimummukan da suke amfanar da wanda ya sansu da cutuwa ga wanda bai nemi saninsu ba.

   

قال رسول الله|: (إنّما العلم ثلاثة: آية محكمة (علم الكلام) وسنة قائمة (علم الأخلاق) وفريضة عادلة (علم الفقه) وما سواهن فضل

Manzon Allah (s.a.w) yace kadai ilimi abubuwa uku ne: aya bayyananniya (Ilimul Kalam) sunna tsayayya (Ilimul Akhlak) farilla adala (Ilimul fikihu) duk wani abu koma bayansu kari ne kawai.

 

Hauzozin Ilimi sun tashi tsaye tare da malamansu da yin bayanin wadannan ilimai na muslunci tun karnin farko-farko har zuwa wannan zamani namu za kuma a cigaba har zuwa bayyanar Imam Mahadi (a.s) sai suka rubuta littafai da wallafe-wallafe cikin wadannan ilimai a tsawon zamani suka cika dakunan nazari na muslunci da ilimummukansu da sakafarsu da abin da yake dacewa tare da zamani da wuri, kuma basu gushe ba kan wannan hanya Allah ya jikan wadanda suka gabata ya kuma kare wadanda suka rage ya kuma sakawa dukkaninsu da gwaggwaban lada da sakamako.

Tura tambaya