lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

HAJJAJU IBN YUSUF!

 

Wata rana Hajjaju Ibn Yusuf ya fito farauta sai yaci karo da wasu karnuka guda tara kusa da su kuma gani wani karamin yaro wanda shekarunsa basu wuce goma ba, Allah yayi masa baiwar gashin goshi.

Sai Hajjaju ya ce masame kake yi anan ya kai wannan karamin yaro?

Sai ya yaron ya daga idonsa ya kale his ya ce masa: ya kai mai tattara labarai, hakika ka kalleni da idon raini, ka yi mini Magana cikin alfahari, kalaminka kalami ne na Jabberin mutum, sannan hankali irin hankali Alfadari ne!!!

Sai Hajjaju ya ce masa: dama ka sanni ne? sai yaron ya ce: na ganeka da duhun fuskarka sakamakon ka zo a fara yi Magana gabanin yi mini sallama, sai Hajjaju ya ce: kaiconka ni ne Hajjaju Ibn Yusuf.

Sai yaron ya ce: kada Allah ya kusanto da gidanka da maziyartarka, me yafi yawa daga surutun da kake yi me yafi karanta daga karamcinka!!

Kafin yaron ya rufe bakinsa sai ga sojoji su kewaye shi ta ko’ina, sai Hajjaju ya umarce su da su dauki wannan yaro su tafi da shi fadarsa.

Sai ya zauna a majalisinsa mutane suna kewaye da shi a zazzaune, saboda tsabar tsoransa duk sun sunsunkuyar da kawunansu kai kace suna gaban wani Zaki ne, sai ya nemi a kawo uaron majalisinsa, yayin da yaron ya hallara a gabansa sai yaron ya daga kansa ya jujjuya idanunsa sai ya yanda ginin fadar ya daga ya mika sama an cancanda masa ado da zane-zane ya cika da matukar kyawunta, sai yaron ya ce: shin yanzu kuna yin ginin sitadiyo a kowanne tsauni kuna yin wargi da wasa kuma kuna rikar matsarar ruwa tsammaninku zaku dawwama kuma idan kuka yi damka sai kuyi da damka kuna masu tankwarawa.

Sai Hajjaju ya daidaita ya gyara zama alhalin da yana kishingide sannan ya ce: shin ka haddace Kur’ani ne? sai yaron shin Kur’ani yana guje mini ne da har zai tsaya ina haddace sh.

Sai Hajjaju ya tambaye shi shin ka tattara Kur’ani? Sai ya ce: shin dama Kur’ani a warwatse yake da har zan tattaro shi? Sai Hajjaju ya ce masa shin wai baka fahimci tambaya ta bane? Sai yaron yas amsa masa da cewa: ya kamata ne kace shin ka taba karanta Kur’ani ka kuma fahimci abinda yake kunshe a cikinsa.

Sai Hajjaju ya ce: to gaya mini wanda aka halicce shi daga iska? Da wanda aka kiyaye da da iska? Da wanda aka halakar da iska?

Sai ya ce: wanda aka halitta daga iska shi ne shugabanmu Isa (as), wanda aka kiyaye da iska shi ne shugabanmu Sulaimanu (as) amma wadanda aka halakar da iska sune mutanen Annabi Hudu (as).

Sai Hajjaju ya ce: to bani labari kan wanda aka halitta daga itace? Da wanda aka kare da itace ? da wanda aka halakar da itace?

Sai yaron ya ce amma wanda aka halitta daga itace shi ne maciji an halicce shi daga Sandar Musa, wanda kuma aka kiyaye da itace shi ne Nuhu (as) wanda kuma aka halaka da itace shi ne Zakariya (as).

Sai Hajjaju ya ce: to gaya mini wanda aka halitta daga ruwa? Da wanda ya tsira daga ruwa? Da wand aka halakar da ruwa?

Sai ya ce: wanda aka halicce daga ruwa shi ne babanmu Adamu (as), wanda aka tseratar daga ruwa shi ne Musa (as), sannan wanda aka halakar da shi da ruwa shi ne Fir’auna.

sai Hajjaju ya ce:  gaya mini wanda aka halicce shi daga wuta? Da wanda aka kiyaye daga wuya? Sai ya ce: wanda aka halitta daga wuta shi ne Iblis, wanda kuma aka kiyaye shi daga wuta shi ne Ibrahim (as).

Sai Hajjaju ya ce: bani labarin hankali? Da Imani? Da kunya? Sa kyauta? Da jarumta? Da karamci? Da sha’awa?

Sai yaron ya ce: hakika Allah karkasa hankali zuwa kashi goma ya sanya guda tara cikin maza ya ajiye guda daya cikin mata, haka ya kasa Imani kashi goma ya ajiye tara a Yaman sauran dayan kuma cikin sauran duniya, ya kasa kunya zuwa kaso goma ya ajiye tara a cikin mata dayan kuma cikin maza, ya kasa kyauta kaso goma kaso goma cikin maza kaso daya cikin mata, ya kasa jarumta da karamci kaso goma tara ya ajiye su cikin Kabilar Larabawa sauran kuma cikin sauran Kabilun duniya.

Sai Hajjaju ya ce: bani labara kan abu mafi kusanci zuwa gareka? Sai yaron ya ce: ranar lahira, sai Hajjaju ya ce: tsarki ya tabbata ga Allah hakika ya bada hikima ga wanda ya so daga bayinsa, ban taba ganin dan karamin yaro ba da Allah ya bashi ilimi da hankali da kaifin basira misalin wannan yaron ba, sannan ya ce: to bani labari dangane da mata? Sai ya ce yanzu kana tambaya ta dagane da mata alhalin ni yaro ne karami banda tsinkaye kan yanayiyyikansu da sha’awe-sha’awensu da zamantakewa da su, sai dai cewa tare da haka da sannu zan kawo maka abinda ya shahara daga al’amarinsu, mace`yar shekara goma tana daga matan aljanna, `yar shekara ashirin kuma ita hutu ce dadin ga masu kallonta, `yar shekara talatin korama ce mai cike da ni’ima, `yar shekara arba’in kiste ce da taushi, `yar shekara hamsin kam uwar yara mata da maza c, `yar shekara sittin bata da wata fa’ida ga masu tambaya kanta.

Sai Hajjaju ya ce: ka kyauta ya kai yaro ka kuma kayatar hakika ka cika mu da kogi daga iliminka, ya zama wajibi kan mu mu karramaka , sai Hajjaju ya bada umarni a baiwa yaron dinare dubu daya tare da tufafi mai kyawu da baiwa da takobi da doki.

Yayinda aka hannanta kyauta ga Hajjaju sai ya ce: dibi duk abinda kake so ya kai Yaro, sai ya ce: idan ka kasance kana bani zabi cikinsu to zabi doki, amma indai kai ka kasance `dan halaliya to ka bani baki daya, sai Hajjaju ya ce: debi dukkansu kada Allah ya sanya maka albraka cikinsu.

Sai Yaron ya ce na yarda kaima ka da Allah ya mayar maka da mayinsu da wasunsu, ka kuma Allah ya kara kaddara haduwa ta da kai nan gaba.

Yaron ya fita daga fadar cikin aminci yana mai cike da ganima albarkacin kaifin basirarsa da fahimtarsa da kyawun tsinkayarsa.

Ya Allah ka azurta mu da ilimi da fahimta ka kuma riskar damu da Salihai ka nesanta mu daga mutanen da suke Fasikai.

Tura tambaya