b Taskar Adduoi 4
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Taskar Adduoi 4

Da sunan Alllah rahama me jin kai

Wanan shine  kashi na hudu na taskar aduoi da zikirori domin biyan bukata

Daga littafin (zubdatul asrar) na ayatollah Adil alawi

1.       Wanda zai je gaban wani sarki ko mai mulki da makamantan su Kaman shuwagabanni na ofishi da sauran su zai rubuta( بدّوح) a goshin sa da dan yatsar sa sannan ya rubuta( ح) a kan fuskar sa ta yadda zai cike fuskar gaba daya.

2.       Haka zalika wanda zai tura wani sako ko zai yi tafiya zai rubuta ( بدّوح) akan jakar sa ko wannan sako din da yarda Allah zasu isa har zuwa yadda ake so su isa lafiya

3.       Haka kuma wanda ya rubuta (. بدّوح) akan gilashin motar sad an neman kariya daga hadarin hanya zai samu kariya da izinin Allah,shi da ( بدّوح) mala’ika ne daga cikin manyan mala’iku wanda daga cikin aikin sa shine isar da duk abun da aka rubuta sunan sa akai zuwa wurin da ake so ya isa cikin aminci,haka kuma ga wand ayake so ya kasance tare da shi a lokacin da yake gida ko cikin tafiya  yana tuna shi da alkhairi Kaman ya karanta al-qurani da niyan Allah ya bashi ladan ko yayi masa sadaka ko a yayin da zai ziyarci daya daga cikin ma’asumai ya ziyara a madadin sa da dai sauran ayuka na alkhairi

4.       Domin kariya da albarkan yara ana iya karanta ( یا بدّوح) kafa ashirin,Kaman yadda yazo duk abun da aka karanta masa ( یا بدّوح) kafa ashirin zai na bada kariya ga wannan abu.

5.       Mutum zai isa ga abun da yake nema  idan ya karanta ( بدوّح) kafa 160 .

6.       Don neman karin dukiya ana rubuta wannan aya tare da bisimillah

7.        (بسم الله الرحمن الرحیم وَلَقَدْ مَكَّنَّاكُمْ فِي الأَرْضِ وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ قَلِيلاً مَّا تَشْكُرُونَ)  a ranar jumma’a a tsakanin sallah guda biyu sai a sanya shi a cikin wurin da ake ajiyan dukiya ko jakan da ake ajiye dukiya a ciki, hakan yana temakawa wurin Karin dukiya da izinin Allah

8.       Idan ana neman kariya da ga lalacewar amfanin gonannaki za a rubuta ayatul kursiyu sannan a bissine shi cikin gonan, kuma zaa sami Karin amfanin insha Allah, haka idan aka rubuta shi a kofar gida barawo ba zai shiga ba, haka zalika idan aka rubuta a kofar shago zaa sami bun kasan ciniki.

Tura tambaya