b Kibiya ta hudu
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kibiya ta hudu

Wani bangare da zantuka Malaman muslunci cikin jabuntakar Wahabiyya:

Sun kasance suna halasta zubar da jinin musulmi da suke imanid akidar Ahlus-sunna kuma Karin kan halascin jinanensu suna cin ganimar dukiyarsu, wannan shi ne abin da Muhammad bn Abdul-Wahab yayi fatawarsa, da wannan fatawa ta rashin imani da tausayi Alu Sa'ud suka halasta jinanen musulmi suka yada barna a doran kasa suka kashe mutanen da basu da laifin komai suka kwacedukiyarsu da kudadensu suka halasta dukkanin alfarmominsu, bidi'arsu da sunan addini ta bayyana karara, sai dai cewa Malaman muslunci sun gaggauta motsawa da tashi cikin martani da raddi kan batan Wahabiyya da karkatarsu , musammam ma raddi kan Fajirin jagoransu Muhammad bn Abdul-Wahab.

Shaik Abu Hamid bn Marzuk Addamashki yana cewa: hakika Malamai masu daga wanda suka yi zamani daya da shi sun yi masa martani da raddi, har zuwa yau kibiyoyin raddi gabas da yamma basu gushe ba suna sauka kansa da wannan kirkirarriyar fitinar tasa.

Wahabiyyawa Shaidan ya rigaya yayi galaba kansu ya kuma batar da su daga madaidaicin tafarki, suna tsammani cewa suna kyawunta aiki, lallai basa bakin komai face cikin bata mabayyani, su kamar dabbobi bari dia sun fi dabbobi bata daga hanya, daga cikin batansu da gurbatarsu shi ne suna imani cewa su kadai ne suke kan hanyar daidai hanyar tsira, baki dayan mutane suna cikin bata duniya da lahira, ya zama tilas a yake su a duniya, tabbataccen batu bisa dogaro da sanannan hadisin Annabi tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gareshi da Alayensa:

 (ستفترق اُمّتي ثلاث وسبعين فرقة )

Da sannu Al'ummata zata karkasu zuwa kungiya saba'in da uku.

Kadai dai zasu kasance daga halakkku ranar lahira, amma a gidna duniya daga babin wahada hadin kan musulmai baki dayansu zasu rayu cikin zaman lafiya da fuskantar juna lallai su hannu ne guda daya kan kishiyantar Makiyansu daga Kafirai da Yahudu Isra'ilawa da wasunsu daga Kafirai da Mushrikai da Mulhidai, sai dai cewa su Wahabiyyawa suna ganin cewa dukkanin musulmai sun kafirta in banda s, a farkon fara da'awarsu sun kai hare-hare kan garuruwan musulmai sun kashe wadanda basu da laifin komai sun kwace dukiyoyinsu, har yanzu hatsarin wannan muguwar Akida bai gushe ba sai dai kawai Allah ya hana su samun damar kashe musulmai a wannan zamani da muke ciki, amma tare da haka suna nan suna jira da dakon ranar da suke raya cewa an yi musu alkawarinta da zasu sake kai hari kan garuruwan musulmai su kara yada barna a kasa, kada Allah ya basu wannan dama kuma ya kaskantar da su da gaggawa, lallai Wahabiyawa miyagun mutane ne kaskantattu da basa taka tsantsan cikin aikata ta'addanci, duk wanda ya zauna da su zai tsinkayi hakikarsu ya fahimce su, suna daukar kawukansu matsayin kungiya da take kan tsira, sai `dan'uwan Muhammad bn Abdul-Wahab Shaik Sulaiman bn Abdul-Wahab ya basu amsa yana cewa: kungiyar da take rabautacciya wacce take kan tsira Manzon Allah ya siffanta ta da wasu siffofi, haka zalika ma'abota ilimi sun siffanta su, lallai baku da siffa daya daga cikin siffofin.[1]

Ka saurari kaji abin da Allama Jamilu Sadaki Azzahawi yake cewa:

Allah ya tsinewa Wahabiyya su a cikin komai kokarin ganin sun kafirta musulmai suke wannan wani abune d ayake bayyanar da cewa su babban abin da yafi damunsu shi ne kafirta musulmai, zaka same suna kafirta wanda yake tawassuli zuwa ga Allah d akamun kafa da Annabinsa suna neman taimako da cetonsa zuwa ga Allah ta'ala cikin samun biyan bukatunsu, musammam ma cikin zamaninmu, amma su fa Wahabiyawa basa jin kunya suyi kamun kafa da Kasashen Kafirai kan biyan bukatunsu a wannan zamanin namu, da najasta kasa mai tsarki da kafafun Sojojin Amerika Kafira-wacce take nuna fin karfi kan musulmi da yakarsu da raba kawukansu.[2]

Bara mu ji abin da Mufti Makka Assayid Ahmad Zaini Dahalan ya ce: Assayid Abdur-Rahman Ahdal Mufti yana cewa: babu bukata wallafa littafi kan raddi da martani kan Wahabiyya, bari dai ya isar cikin raddi kansu fadinsa: (siffofinsu aske gashin kai salsali, lallai yanda al'amarin ko da wani daga `yan bidi'a daga wasunsu bai aikata hakan ba, wata rana wata mace ta kfa hujja kan Muhammad bn Abdul Wahab lokacin da suka tilasta ta kan binsu sai ta bisu, Bn Abudl-Wahab ya umarceta da ta aske gashin kanta, sai tace masa: tunda kana umartar mace ta aske gashin kanta to sai ka umarce Namji ma ya aske gemunsa, sabida gashin kan mace ado ne gareta haka gemun Namiji ado ne gareshi, sai ya kasa bata amsa.[3]

Ya kara cewa: cikin wannan ta 1305 hijiri- as cikinta farkon fara yaki tsakanin Maulana Sharif Galib da kungiyar Wahabiyya mabiya Muhammad BN Abdul-Wahab cikin akidarsa ta kafirta dukkanin musulmai, gabanin kawo yakin ya kamata fara Ambato farkon al'amarinsu da hakikanin yanda suke, lallai fitinarsu tana daga mafi girman fitina da ta bayyana cikin muslunci, hankula sun zautu sun bushe ma'bota hankula sun dimauta daga masibar wannan fitina, bayyanar Muhammad bn Abdul Wahab ta kasance a shekara 1143 hijiri, lamarinsa ya shahara bayan shekara hamsin, sai ya bayyanar da jabun akida a garin Najad, sai Muhammad bn Sa'ud Sarkin dar'iyya garin da aka haifi Musailamatul Kazzab, sannan Bn Sa'ud ya umarci mutanen garinsa da su bi Bn Abdul-Wahab cikin dukkanin abin da yake fada, sai mutanen garin suka bi Muhammad bn Abdul-Wahab.[4]

Ga abin da Shaik Khalid Albagdadi yake fada cikin littafinsa: da zamu karanta litattafan Wahabiyya cikin nutsuwa da dandake karatu zamu ga suna kokarin yaudarar musulmai da batar da su, tunaninsu gurbace yake da watsatstsun ra'ayoyi miyagu bayan sun rina su da rini rarraunan launin hankali sun masu ado da kalmomi da aka yi musu fenti da ruwan zinariya, zaka samu Jahilan mutane suna gasgata su suna zaton cewa wannan kalmomi na Wahabiyyawa sun daogara kan hankali da mandiki sai su dinga binsu, amma Malamai ma'abota dacaccen ra'ayi  har abada ba zaka same suna fadawa cikin wannan tarkon na Wahabiyya ba, hakika Malamai tun karnoni goma sha hudu da ya gabata sun yi talifi dubunnan litattafai masu daraja wadanda suke cike da fa'ida domin farkar da Samari da matasa daga hatsarin Wahabiyyawa `yan ba ruwana da mazhaba wadanda suke suke kora musulmi zuwa ga halaka ta dindin ta har abada.[5]

Allama Shaik Malik bn Shaik Dauda yana cewa: dalilan da suka zo cikin raddi kan akidun Wahabiyya ba zasu kidaitu ba, hakika Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi da Alayensa a cikin adadin wasu hadisai ya hana kafirta musulmi, daga cikinsu: fadinsa: 

 (إذا قال المرء لأخيه يا كافر فقد باء به أحدهما)، رواه مالک والبخاري والترمذي »[7] .

Idan mutum ya cewa `dan'uwansa ya Kafiri hakika Kalmar kafirce ta na koma kan dayansu, ko dai shi ne Kafiri ko dan'uwansa da ya kira da Kafiri.

Kadi Abdur-Rahman Kuti yana cewa: hakika sun shafawa fuskar addinin muslunci bakar toka su msa bakin fenti, sun maida masu sabani da akidunsu Mushrikai Makiya addini da kalmomin da suke fitiowa daga bakunansu a tarukansu da gurbatattun risalolinsu, ya cigaba da cewa: (da sannu wani Shaidani zai bayyana a garin Najad garuruwan larabawa zasu girgiza sakamakon fitinarsa) wanda yake nufi da fadi wani Shaidai shi ne Muhammad bn Abdul-Wahab, an haife shi a Najad shekara 1111 hijiri, sannan fitinarsa ta Wahabiyya a a hankali sannu sannu d abazu a dukkanin nahiyoyi da yankunan musulmai, daga nan kuma wannan mugun ciwo mai wahalar da likitoci ya tsallaka zuwa kasar Indiya musammam ma a garin Kirata a shekara 1914 miladi.[6]

Ya kai mai karatu mai daraja, kasa hankali da tunani ya zama jagora cikin karatunka, sannan ka biyo ni mu karanta abin da Ustaz Muhammad Ahmad Hamid Assudani yake fada: lallai daga sanann al'amari ga dukkanin musulmai a yau shi kungiyar `yan mishan masu maida mutane kirista tare da dukkanin karfinta bata iya gamsarwa, hakama Kiristanci a kankin kansa da hanyarsa da tsarinsa na kyautata dabi'u bai iya cike dukkanin gurbin rayuwa, wannan ya sanya `yan mishan na duniya bayan deba tsammani da fata daga maida mutane kiristoci da samun ikon kansu da mamaye su ta hanyar amfani da hanyoyi daban-daban sai suka koma da amfani da dabarar samun karan farauta cikin shuganbannin musulmi da ba'arin wasu malaman addini malaman fadar Sarki da zasu yi aiki da su don kare manufofinsu da kudure-kudurensu, wadannan mutane zasu yi zo da sunan sassauci da tabbatar da zaman lafiya da watsi da ta'addanci duka domin dusashe dokokin muslunci.

Sannan `yan Mishan suka fara zartar da kudurinsu ta hannun Karnukan farautarsu daga Maha'intan shugabanni da tallafa musu don durkushe dukkanin wani motsin `yanci na muslunci da dukkanin hukumomin masu son cigaban al'ummarsu, da kuma barazana kan kasar Iran, sannan rura wutar yakin yankin Gulf ta hannun Karnukan farautarsu `yan Saudiyya wadanda suka gamsar da Saddam Husaini kan shiga cikin yaki, sannan kuma shigowa Faransawa da Amerikawa da sojojinsu cikin Kasar Chadi, dukkanin wadannan abubuwa sun faru bada nisa kwakwalen mutane zasu iya tuna su, wannan duka yana daga  abin da yake bayyanar kiyayya da muguntar `yan Mishan da basu wadatu da satar dukiyoyi da arziki da mulkin mallaka kan kasashe ba.

Yanzu kuma sun kara dawowa da sunan masu taimako suna kokarin farlanta ikonsu kan al'umma sai dai cewa haihata haihata.

Shaik Muhammad Jawad Mugniya daga Malaman shi'a yana cewa: babban abin da yajke jan hankali cikin wadannan litattafan na Wahabiyyawa da masadir dinsu-shi ne kwadaitarwa mai tsanani kan kafirta al'ummar Manzon Allah (S.A.W) wannan kwadayi yak an haddin sha'awa ko kuma daukar fansa, dokarsu ta addini da zamantakewa da siyasa shi ne:  ko dai ka kasance Bahawabie ko kuma mu kashe ka da kwace dkiyarka da daukar zuriyarka matsayin ganimar yaki.[7]

Ya ce: na ziyarci dukkanin shagunan sayar da  litattafai na garin Makka na bincika cikinsu ban samu littafi ko da kwaya daya ba na shi'a da ake sayarwa a bayyane face littafin Majma'ul bayan da Makarimul Akhlak na Dabarasi bugun Misira, amma  naga litattafan turawa dauke da hotunan mata tsirara kai hatta littafi Mayo na gani ana sayar da garin da dakin Ka'aba mai tsarki yake musammam shagon nan da yake kallon wurin Sa'ayi fuska da fuska, zan fuskanci wahabiya da wannan hakika na rubuta sunayen litattafan da na gani a wurin daga cikin akwai: Nisa'ul Laili,-Shaharul Asali-Imra'atu min Faris- Shirriratu, dss.

Tare da cewa ban san abin da da litattafan suka kunsa ba, sai dia cewa a bangon litattan nag a hotunan maza suna cakume da mata tsirara suna sumbatarsu da rumgumarssu, da zarar mai Harami ya fito daga cikin Harami zai ci karo da wannan Munkarai da hotunan Alfasha wadanda Askarawan Saudiyya masu kirarin umarni da kyakkyawa da hani da munkari suka kyale sabida a wurinsu kenan wadannan abubuwa basa cin karo da addini da ladabi amma sumbatar Kabarin Annabi (S.A.W) ko shafa shi shirka da ilhadi a lissafinsu, wannan fa shi ne tunanin Wahabiyyawa, wannan itace al'adarsu, suna bada `yanci ga Macizai da suke fesar da guba hatta kusa da kofar dakin Ka'aba mai tsarki amma  kuma a daidai wannan lokaci nsun toshe duk wata tagar haske da shiriya daga barin masu nemanta da dimautattu da suke neman haske da shiriya, waya sani? Me yiwuwa sun bada dama da izini ga wadancan abubuwa da wadannan rubututtukan zamani masu cin karo da kyawawan dabi'u domin su tabbatar da cewa Masarautar Saudiyya ta gabaci gabas da yammacin duniya cikin wayewar zamani.

Allah ya kiyaye musulmai ya kuma tsaresu daga fitinar Wahabiyanci.    


Sawa'ikul Ilahiyyati 41.[1]

[2] Fajarul Sadik 733 bugun misira.

[3] Fitinatul Wahabiyyati 77.

[4] لBayanul Ulama'ul Haramaini 2-227

[5] Iman wal Islam 42.

[6] Haka'ik islamiyya 21.

[7] Mukaddimatu Kitab Sabiul Najat.


Tura tambaya