lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Me ya sanya Imam Sajjad (a.s) bai yunkura ba don kafa hukuma?

la'akari da yanayin sahar siyasar zamanin Imam Sajjad zuwa wani mikdari zamu iya cewa komai a bayyane yake zamu iya fahimta dalilin da ya hana shi tashi da yunkuri? Saboda tareda razani da matsanancin tsoro  da matsi cikin mulkin Umayyawa tareda cikakken iko da mamayarsu duk wani irin yunkuri da motsi dauke da makami tabbas ba zai samu nasara ba, sannan babu wani boyayye n motsi komai kankantarsa da zai iya buya daga idanuwa da kunnuwan `ya leken asirin hukuma, wata rana daya daga `yan leken asirin Abdul Malik a garin Madina ya kawo masa bayanai kamar haka: hakika Aliyu Ibn Husaini yana da wata baiwa da ya `yantar da ita wacce daga baya ya zo ya aureta, cikin wasikar da Abdul Malik ya aikawa da Imam Sajjad ya nuna rashin jin dadinsa kan auren Imam daga Baiwa kuma ya bayyana wannan aiki a matsayin tawaya saboda menene Imam ba zai auri daya daga matayen da suke dace da shi matsayinsa da girmansa ba daga matayen Kuraishawa?!. Imam ya bashi amsa: babu wani mutum mafi girma da daukaka daga Manzon Allah (s.a.w) hakika ya auri bazawara baiwa, hakika ubangiji ya daukaka duk wani kaskataccen da muslunci, duk wata tawaya ya kammala ta da muslunci babu wani kaskanci da yawuce Jahiliya.

Abdul Malik yana so ya zamana duk wani motsin Imam da gidansa ya kasance karkashin sa idonsa, a misalin wannan yanayi da matsanancin matsi ta yaya yunkuri sauya hukuma zai kasance?

 

Menene ya hana Imam Sajjad yin aiki tareda masu yunkuri kifar da hukuma a Madina?

1-tareda duban yanayi da zuruf da la'akari da matsi da kuntatawa da suka kasance tun bayan shahadar Mahaifinsa Imam Husaini (a.s) Imam yayi kirdadon da hangen rashin samun nasara ga yunkurin Madina , yana ganin cewa idan yayi tarayya cikin wannan yunkuri bawai kadai ba zai samu nasara bari dais hi da mabiyansa duk kashe su za a yi  sannan babu batun wanzuwa sauran burbushi da karfin shi'anci lamarin zai kare babu wata natija mai kyau.

2-tareda la'akari tarihin Abdullahi Ibn Zubairu da tasirin da yake da shi cikin masu yunkuri kifar da hukuma wannan yunkuri ba zai taba kasancewa irin yunkurin shi'anci ba na asali , snanan Imam (a.s) ba zai taba yarda mutum misalin Abdullahi Ibn Zubairu mai kishirwar mulki da iko ya mayar da shi tsani da gada da taka shi ya tsallaka zuwa ga bukatarsa da cimma nasararsa ba.

3 kamar yanda ya gabata, masu yunkurin kifar da hukuma sun zabi Abdullahi Ibn Hanzalatu matsayin shugaba kuma basu neman shawara da jin ra'ayin Imam Sajjad (a.s) duk da cewa jagororinsu mutane tsaftatattu nagargaru sannan sukansu kan hukumar Yazidu duka gaskiya ne, sai dai cewa ya tabbata wannan yunkuri ba tsantsar yunkuri ne na shi'anci ba sannan babu tabbas idan suka samu nasara ko zata amfanar da shi'anci

Tura tambaya