lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kibiya ta uku

Raddi kan Wahabiyanci daga littafan bangarorin musulmi biyu shi’a da sunna cikin dakin nazarin karatu na Maktabatul-Al’arabiyya

Abu Hamid bn Mazruki ya ce: [1]

Hakika mabiya mazhabobi hudu sun raddi kan Abdul-Wahab da mabiyansa masu makauniyar biyayya sun raddin cikin talifofi masu tarion yawa kuma masu inganci, daga cikin wanda yayi masa raddi daga mazhabar Hanbaliya shi ne `dan’uwansa Sulaiman bn Abdul-Wahab, sannan kuma daga Hanbalawan Sham akwai Alu Shaddiyu, da Shaik Abdul-Kadumi Nabilisi cikin tafiye-tafiyensa , dukkaninsu an buga su cikin Nahiyoyi na ziyarar Annabi tsira da amincin Alla su tabbata a gareshi da Alayensa, sannan wai yin tawassuli da Annabi da Salihan bayi daga al’ummarsa baya halasta, Malamai sun ce Abdul-Wahab da masu binsa ido rufe dukkaninsu Kawarijawan zamani ne

Daga cikin wanda ya nassanta wannan bayani shi ne Allama Assayid Almuhakkik Muhammad Amin bn Abidin cikin Hashiyarsa (Raddul Muktar aka Durrul Muktar) cikin babin (Bugatu) da kuma Shaik Assawi Almisiri cikin hashiyarsa kan Tafsirin Jalalaini, sakamakon bn Abdul-Wahab ya kafirta masu Imani da Kalmar shahada sabida kawai basa bin ra’ayinsa da fahimtarsa, babu shakka kan cewa kafirta musulmi siffa ce ta Kawarijawa da dukkanin `yan bidi’a wadanda suke kafirta masu sabawa ra’ayinsu daga musulmi….

Jigon akidun Muhammad bn Abdul-Wahab da mabiyansa sun takaice sun tattaru cikin abubuwa guda hudu: kamanta Allah matsarkaki madaukaki da halittunsa, tahidin uluhiyya, rashin girmama Annabi, kafirta musulmai, shima yayi taklidi cikinsu ne da Ahmab bn Hanbal da bn Taimiyya, a ta farko yayi taklidi da Karamiyya da Mujassima da Hanbalawa, sannan ciki ta hudu yayi taklidi da Harawiyyun, sannan aminci cikin nakalto addini ta tattaru cikinsa a wajen mabiyansa da Almajirin bn Taimiyya bn Kayyum da kuma cikin Muhammad bn Abdul-Wahab, Wahabiyawa basa aminta da kowanne Malami daga Malaman musulmai, basa ganin kimarsa ko darajarsa sai idan sun sami wata shubuha cikin zantukansa da taka karfafa son rans addini muslunci tare da dukkanin fadadarsa amma an takaice malamansa cikin mutane uku.[2]

Assayid Alawi bn Ahmad Haddad ya ce: na ga amsoshi guda biyu daga manya manyan Malaman Mazhabobi hudu ba zasu daga adadin Malamai masu tarin yawa daga Malaman Makka da Madina da Basara da Ihsa’I da Bagdad da sauran garuruwan musulmai wadanda suka zo ziyara, ciki na samu raddi daga Malamai masu tarin yawa, ya kara da cewa an zo mana da wani babban Malami masanin hadisi mai suna Salihu Falani Almagribi da wani babban littafi kunshe da Risaloli da amsoshi dukkaninsu daga Malaman Mazhabobi hudu: Hanafiyya, Malikiyya, Shafi’iyya, Hanbaliyya, suna raddi da martani kan Muhammad bn Abdul-Wahab,  da yawan Malaman zamaninsa sun masa raddi sannan wadanda suka zo bayansa sum aba abarsu a baya cikin raddi kansm har zuwa yau kibiyoyin raddi daga gabas da yamma basu gushe ba sun sauka kansa, cikin hudar masu raddi biyu kansa sune Hanbalawan garin Ihsa’i na Saudiyya sannan baki dayan raddodin kadia suna karkata a hakika zuwa ga Bn Taimiyya.[3]

Mun ambata a baya cewa farkon wanda ya fara rubuta raddi kan Wahabiyanci shi ne Shaik Sulaimani bn Abdul-Wahab wand aya kasance `dan’uwa ga Bn Abdul-Wahab batacce mai batarwa, Shaik ya bada amsa da wannan littafi (Assawa’ikul Ilahiyya fi Raddi ala Wahabiyya, lokacin da aka nemi dalilai da hujjoji kan gurbata da karkatar wannan mazhaba ta girman kan duniya wacce ta karkace daga gaskiya da muslunci na gaskiya.

Hakika malamin ya tabbata da Jahilci Muhammad bn Abdul-Wahab cikin littafin da bacewarsa da mabiyansa da rashin cancantar su ga istinbadin hukunci, kamar yanda cikin littafin ya tabbatar da karyar jabun akidunsu da gurbatattun ra’ayoyinsu da suka karkace daga gaskiya cikin kafirta wanda bai dace da ra’yinsu ba daga musulmai cikin mas’aloli bakance da neman ceto da addu’a da rokon matacce da iznin Allah da makamancin haka, daga abubuwa da musulmi suke yi basa gani laifi shin daga Ahlus-sunna suka fito ko wasunsu, suna Imani da ingancinsu suna kafa dalili kan dukkaninsu daga tawassuli addu’a neman ceto bakance da ingantattun dalilan shari’a da ijma’i.[4]

Shaik Ihsan Abdul-latif Albakari ya ce:[5]

Daga cikin abin da yale jawo hankalin dukkanin amintaccen marubuci da mai neman gaskiya shi ne babban littafi mai daraja wanda Ustazu Mujahid Shahid dan’uwa Nasir Sa’idi ya wallafa mai suna (Tariku Alu Sa’ud) littafin ya kunshi tarihin Wahabbiyawa a zamaninsu mai duhu, da kuma wanda suke ciki makuntaci, ya tona asirin jagororin hukuma Saudiya yaran turawa `yan mulkin mallaka Mujirimai da suka karfafa ginin addinin Wahabiyyyawa batattu masu batarwa.

Wannan littafi mai girma ya kunshi shafuka daidai har guda dubu cike da kawo tabbatattun abubuwa da suka faru wadanda amintattun masadir ke karfafa su, ba zaka same sub a cikin wanin littafin gabanin buga shi.

A cikin shafukan littafin zaka ga hotunan ba’arin jagororin Wahabiyanci marasa kyan gani daga masu rike da madafun ikon hukumar Saudiya lalatacciya suna zalunci don hidimtawa iyayen gidansu Yahudawa da Amerika.

A hotuna zaka ga yanda suke shan giya suna sanya Sakandami a kirajensu gasu tare da da Karuwai, wannan littafi ne mafi fadada da zai kewayi mai karatu mai daraja da ilimi da sanin miyagun laifukan masu jagorantar wannan kirkirarren addini da kagaggiyar mazhaba.

Sannan ya ciga da cewa: ya dan’uwa musulmi bayan na kewayar da kai da ilimi dangane da Mazhabar Wahabiyya da hakikarsu, yanzu ka san cewa Wahabiyya mazhaba ce da Muhammad bn Abdul-Wahab ya kirkireta, ka san littafan da Malamanmu suka rubuta cikin raddi kansa da rusa shi da ruguje sh, to kayi taka tsantsan matuka daga kunatar mabiyansa da zama da su da bin jabun tunaninsu da lalatattun akidunsu, da karanta littafansu masu batarwa, sannan na haneka na haneka daga kasancewa cikin wadanda Allah ta’ala yake cewa cikinsu:          

 (وَإذا قيلَ لَهُمُ آتَّبِعوا ما أنْزَلَ اللهُ قالوا بَلْ نَتَّبِع ما وَجَدْنا عَلَيْهِ آباؤُنا).

Idna akace musu ku bi abin da Allah ya saukar sai suve bari zamu bi abin da muka samu iyayenmu akai.

Sai Allah yayi musu martani da fadinsa ta’ala:

 (أوَ لَوْ كانَ الشَّيْطانُ يَدْعوهُمْ إلى عَذابِ السَّعير).

Ko da kuwa Shaidanu suna kiransu zuwa ga Azaba mai ruruwa.

Ko kuma daga cikin wadanda:

 (قالوا أجِئْتَنا لِتَلْفِتَنا عَمَّـا وَجَدْنا عَلَيْهِ أباءَنا).

Suka ce shin ka zo ne don ka karkatar damu daga barin abin da muka samu iyayenmu a kai.

 (لَقَدْ كُنْتُمْ أنْتُمْ وَآباؤُكُمْ في ضَلالٍ مُبين ).

Hakika kun kasance da iyayenku cikin bata mabayyani.

Ina fatan cikin karatunka da nazarinka yantacce cikin akidarka da imaninka kamar yanda Allah yake so daga gareka, kada ka zama bawan waninka bayan mahaifiyarka ta haifeka `yantacce.

 (فَبَشِّرْ عِبادِ الَّذينَ يَسْتَمِعونَ القَوْلَ فَيَتَّبِعونَ أحْسَنَهُ ).

Ka yi bushara ga bayina wadanda suke jin magana su bi mafi kyawunta.

Wannan kenan sannan hakika ya kai mai karatu mai daraja mun kawo maka litattafai daidai har guda hamsin daga litattafan malaman Ahlus-sunna cikin raddinsu kan Wahabiyya, to yanzu ga wasu Kari kan na baya ka duba:

1-Tadhirul Fu'ad min Danasil Itikad: Shaik Muhammad Najaitu Mudi'i Hanafi.

2-Kashaful Nuri an As'habil Kuburi: Shaik Abdul-Gani Nabilisi.

3-Saiful Abrari ala Fujjari: Shaik Abdur-Rahman Hanafi.

4-Izhakul Badili fi Raddi ala Wahabiyyati: Assayid Ibrahim Rufa'i.

5-Gausul Ibadi bibayanir Rashadi: Shaik Mustafa Hammami Almisiri.

6-Alwahabiyyati fi Nazarul Ulama'il Muslimin: Shaik Ihsan Abdul-latif Albakari.

7-Alyamani wa Alu Sa'udi, Niftun wa Fada'ihi: Fahad Kahadani.

8-Islam wal Wasaniyyatus Sa'udiyyati: Fahad Kahadani.

9-Albara'atu minal Iktilafi fi Raddi ala Ahlil Shikaki wan Nifaki fi Raddi ala Firkatil Wahabiyyati Dalatu: Shaik Aliyi Zainul Abidin Suadani.

10-Bara'atul Shi'ati min Muftarayatil Wahabiyyati: Ustaz Muhammad Sudani.

11-Saihatus Suwwari: Nasir Assa'id.

Bai buya ba cewa abin da muka kawo daga raddi kan Wahabiyya daga litattafn bangarori biyu na musulmai dan kadan daga tarin raddodi da akayi kansu, haka na tabbata ne karkashin dakin nazarin karatu na Maktabatul Arabiyya ta harshen larabci, amma amma cikin sauran harsuna da yare kamar misalin harshen Turkanci da Urdu da Farisanci da wasunsu lallai raddin ya nunnunka haka sosan gaske, wannan karara na nuni kan munanar wannan muguwar mazhaba ta Wahabiyya da gurbacewarta da kuma cewa Wahabiyanci wata kungiya ce da girman kan duniya `yan mulkin mallaka suka kirkireta, lallai kuma ta fita daga cikin da'irar mazhabobin muslunci, sannan makomarta shi ne rushewa da bushewa daga samuwa kamar yanda sauran kungiyoyi na bata suka rushe misalin Shuyu'iyya (Gurguzanci) da ya rushe a tarayya Sobiyat karkashin Rasha, ko da kuwa yanzu muna ganinta samuwarta a surance kamar misalin samuwar fim din karton , lallai ita karya tana iya zamaninta kuma fure take bata `ya`ya zata gushe, shin wai Ausbahi ba kusa take ba ne?!

Amma bangaren Malaman shi'a lallai suma ba a barsu a bay aba hakika sun yi rubuce-rubuce mai tarin yawa cikin raddi kan batan da bidi'ancin Wahabiyya, ga wasu ba'ari daga wallafe-wallafen shi'a kan Wahabiyanci:

 1-Kashaful Irtiyabi fi Atba'i Muhammad bn Muhammad: Assayid Muhsin Amin Amili.

2-Kashaful Nikabi an Aka'idil Bn Abdul-Wahab: Assayid Ali Nakiyu.

3- Hazihi Hiyal Wahabiyya: Shaik Muhammad Jawad Mugniya.

4-Minhajul Rashad Liman Arada Sadad: Shaik Muhammad Husaini Kashiful Gida.

5-Algadir: Allama Amini (juzu'i biyar cikin mausu'atu Algadir).

6-Alwahabiyyatu fi Mizani: Shaik Jafar Subhani.

8-Risalatu Nakadil Fatawa Alwahabiyyati fi Kitabi Ayatil Bayyinat fi Kam'I Bida'i wa Dalalat: Shaik Muhammad Husaini Kashiful Gida.

9-Safahatu an Alu Sa'udi Wahabiyyin: Assayid Murtada Ridawi.

10-Ma'a Wahabiyyin fi Kudadihim wa Aka'idihim.

[1] Attawassul binnabiyi wa bissalihin: 1

[2] Alwahabiyyatu 14.

[3] Alwahabiyyatu 16.

[4] Alwahabiyyatu 24.

[5] Alwahabiyyatu 40.


Tura tambaya