lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Daga ƙissoshin Annabawa amincin Allah ya kara tabbata gare su: kissar Annabi Sulaimanu (as) da shawarar da jemage ya bayar

 

Ta farko ita ce rana: sai rana tace ya Annabin Allah ka roka mini Allah da ya sanya ni cikin wuri guda kamar ragowar halittu, ka da in kasance cikin dawwamar motsi tsakanin mahuda da mafada ma'ana gabas da yamma.

Na biyu maciji: maciji ya ce: ya Sulaimanu ka roka mini Allah da ya karramani da bani hannuwa guda biyu da kafafuwa guda biyu kamar sauran dabbobi, lallai ni na gaji da tafiya kan cikina.

Na uku itace iska: iska tace: ya Annabin har zuwa yaushe zan daina kai kawo daga wannan wuri zuwa wancan wajen, ka roƙa minin Allah ya ajiye ni a wuri guda kuma ya jinkirta mini.

Na hudu shi ne ruwa: ruwa ya ce: ya Sulaimanu har zuwa yaushe zai dinga kai kawo da ywo cikin kasa da tsakanin sama da kasa ina rude da firgice, banda wani muhalli da zan tsuguna cikinsa, ka roƙa mini Allah ya tsugunar da ni cikin muhalli guda duk mai buƙata ta sai ya neme ni ya nufe ni.

Haƙiƙa Allah ya sanar da Sulaimanu zancen tsunstu sai Sulaimanu ya tara tsuntsaye don neman shawara tsakanin tsuntsayen akwai jemage ya ay kasance shi ne mafi raunin cikinsu, sai Sulaimanu ya nemi bayayana matsayin jemage tsakanin sauran tsuntsaye, sai ya  labarin daga halittun Allah  huɗu  da buƙatunsu.

Sai jemage ya ce: ya annabin Allah da a ce rana ta kasance cikin mutsuguni ɗaya da mutane basu san dare daga rana ba, da tsari da lokutan mutane da ibada sun samu matsala sun raurawa, daga cikin maslaha kowa da kowa shi ne rana ta dinga jujjuyawa ta dinga huda a kowanne waje, kamar yadda zata tsarkake muhalli daga gurbatuwar iska mara kyawu .

Amma ruwa: lallai Allah ya sanya komai na rayayye daga ruwa, da zai tabbatu a wuri guda da dukkanin mutane da dabbobi sun halaka, ta kaka za a iya zuwa inda ya ke  tare da nisan zango da wahalhalun hanyoyi, wannan zai iya jawo halaka.

Amma maciji: lallai shi maciji makiyin mutum ne idan har ya kasance tare da cewa ya na jan ciki amma kuma mutane na tsorata daga gare shi yaya idan kuma ya kasance yana da hannaye biyu da kafafuwa biyu, lallai zai halaka mutane da gubar da take tattare da shi.  

Amma iska: ba da ban ita ba ta yaya lokutan hunturu da bazara da damina zasu kasantu haka ma ta kaka za a samu barbarar tsirrai da bishiyoyi.

Sai Sulaimanu ya karbi wannan daga jemage sai dai cewa shi ya karba a mukamin jayayya da rigima, rana tace in azan sami jemage in kona fuffukensa, iska tace: ni zan daddatsa shi gunduwa-gunduwa, ruwa ya ce: sai na nutsar da shi, maciji ya ce: ni sai na kashe shi da guba ta.

Sai jemage ya nemi taimako daga Allah daga kiyayyarsu ga shi kuma ya kasance rarraunan tsuntsu ta yaya zai karawa da su,  kadai shi ya nufi yin nasiha ne da kuma bayyana abin da gyaruwar bayin Allah ke cikinsa.

Sai magana ta sauko daga Allah madaukaki matsarkaki tushen girmama da cewa: dukkanin wanda ya dogara damu zamu isar masa, dukkanin wanda ya nemi taimakonmu zamu cece shi, saboda haka kada kaji tsoro ka da kai bakin ciki, hakika na sanya tashinka sama cikin dare, ranar ba zata cutar da kai ba, na sanya iska mahayinka matukar baka fitar da iska daga bakinka ba ba zaka iya tashi sama ba, na sanya kashinka mafi galibin lokaci kan gubar maciji, da maciji zai shaki warinta  daga zango mai nisa da ya mutu, amma ruwa kan kirjinka na sanya nonuwa guda biyu cikinsu akwai nono tsawon shekara, duk sanda kaji kishirwa sai ka kwankwada daga gare shi ka koshi ba zaka bukatu da ruwa a wannan lokaci ba:

Izina da fadakuwa:

babu kokwanto lallai cikin wadannan kissoshi na annabawa akwai ayoyi da darasussuka ga salikai da masu neman ilimi, da bushara da farin ciki ga muminai, cikin wannan kissa zamu iya tsintar gomomin izina da darussuka, daga cikinsu akwai:

1-wajibi ne kanmu mu sauke nauyin da yake wuyayenmu da gwargwadon yadda aka bukata daga garemu, mu gamsu da waki'iyya cikin duniyar halitta da shari'a.

2-mu fadi gaskiya ko da kuwa akwai hatsarin tattare da fadinta, face abin da ya togatu da dalili.

3-mu kasance daga masu nasiha.

4-ka da muyi ha'inci a cikin mukamin bada shawara da nasiha daga wanda ya nemi shawararmu da nasiharmu.

5- mu dinga neman shawara ko da daga wanda yafi mu rauni ne me yiwuwa Allah ya zartar da gaskiya kan harshensa.

6-idan akwai wani wanda ya ke kiyayya da mu daga halittun Allah, ka da ka ji tsoro ka da ka yi bakin ciki, lallai Allah yana tare da mu zai tseratar da mu zai taimake mu idan muka fake da shi muka nemi taimakonsa.

  7- mu sallama al'amarinmu ga Allah mu dogara da shi mu fawwala al'amari a hannunsa, muyi imani da cewa abin da ya ke aikatawa shi ne hikima, dukkanin abin da ya ke kaddarawa shi ne maslaharmu da alherinmu, alherinsa na sauka zuwa gare mu

Tura tambaya