lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Hikayar SOYAYYA

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai tsira da aminci su kara tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Imam Sadik (as) yana cewa: shin addini wani abu ne da ya wuce soyayya.

 

 Wani matashin yaro ya kasance ya na masifar son wata yarinya budurwa ita ma haka ta na masifar son sa, ya kasance suna aiki a wajen aiki guda cikin ma’aikatar gwaje-gwajen kimiyya sun kasance basa rabuwa da juna tsawon yini, sun kasance suna tafiya aiki tare da juna suna cin abinci tare da juna suna wasa da juna duk tare babu abin da yake raba su sai bacci, duk sanda suka tashi daga aiki suna tafiya Sinima suna tare da juna ko kuma wani wajen cin abinci, muhimmi shi ne suna tare da juna.

 

A wata rana yaron ya tafi wajen aikinsa ya gama aiki da wuri sai ya tafi wajen mai sayar da kayan adon mata domin ya sayi zobe domin ya yiwa waccan budurwar ta sa da hadayarsa gareshi ya nemi aurenta, ita ma bisa dacewa sai ya zamanto a kowacce rana tana zuwa wajen gwaje-gwajen kimiyya sai dai cewa wannan rana wata matsala ta faru gareta tana cikin gwajin sinadarin gwajin halitta sai ya subuce daga hannunta ya fadi kasa sai ta gigice ta fara ihu sai likitoci su ka ji ihunta sai suka dauketa suka kaita asibiti sai dai cewa a can labari ya munana ta yanda likitoci suka bayyana cewa zata kamu da ciwon makanta sakamakon abin da ya faru da ita, yayin da wannan matashi yaji wannan labari sai kai tsaye ya tafi asibiti daga nan ba a kara jin labarinsa ba.

Bayan an yi mata aiki a fuska sai ganin wannan yarinya ya dawo gareta ta wayi gari tana gani kamar kowa kai bari hatta kyawunta ya ma karu, sai ta tafi wajen aikinta domin ta binciki halin da masoyinta yake ciki, ta bincika kowanne wuri amma ina bata same shi ba, daga karshe dai sai ta tuna wani waje da yake zuwa duk sanda ya tsinci kansa cikin damuwa sai ta same shi wannan waje a zaune shi kadai tsakankanin bishiyoyi, sai hawaye ya fara kwarara daga idanunta, ta tafi gareshi domin tabbatar da cewa baya gani domin shi ne ya sadaukar da idonsa ya bata don ta samu damar gani shi ya hakura da nasa ganin ya kuma nesanceta domin ta kara samun damar kara rayuwa tare wani mutum daban.

Wayyo inama har yanzu akwai irin wannan soyayyar a wannan zamanin.

Imam Sadik (as) yana cewa shin addini wani abu ne da wuce soyayya.

Ita soyayya tana nufin sadaukarwa.

 

Umar Alhassan Salihu

Faroukumar66@gmail.com


Tura tambaya