lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

hikayar barbela

 

Lokacin kaka ya kasance iska na xauko qamshin fure tana yayyaxawa, daddaxan qamshin tufa da Aluce, Imam Rida (a.s) tareda sahabinsa Sulaiman sun zauna cikin farfajiyar gida suna tattaunawa tareda juna, ayarin barbeloli suna ta kuka suna karkaxa fukafukansu a saman kansu, sannan kuma suka sauka saman bishiya, Imam (a.s) ya xaga kansa ya kalle su, sai barbelar ita ma ta kalle shi tace masa ta dinqa qara da qarfi qwa-qwa.

Bayan xan wani sai wannan barbela ta ximauce fiye da baya ta dinga fuffukawa saman kansu, a wannan lokaci sai ta xan sauko qasa-qasa ta gifta ta gefan idon Imam (a.s), Sulaimanu yana bibiyarta da idonsa yace: wannan wacce rin tsagerar barbela ce! Tabbas yunwa take ji.

Sai wannan barbela ta qara tashi ta je ta sauka kan reshan bishiyar kayan marmari ta ciori guda xaya sai ta fara magana, sai dai cewa har yanzu a xau tsawon wani lokaci ba ta qara ta shi saman kan Sulaiman da Imam (a.s) tana kaikawo ta qara giftawa ta gaban idon Imam, sai Sulaiman yace: ina neman tsarin Allah! Wacce irin tsageran barbela ce, taqi kyale mu mu huta.

Imam (a.s) ya waiwaya ga Sulaiman yace: shin kasan me wannan barbelar take faxi?

Sulaiman cikin mamaki yayi tambaya yace: a.'a ya farincikina! Me take faxa ne?

Imam yace: wannan barbela uwa neman taimako take daga garemu, saboda `ya`yanta suna cikin hatsari babba!

Sulaiman cikin ximauta da damuwa yace: yanzu me zamu yi kenan? Wacce shawara kake bayarwa yanzu?

Imam ya tashi ya xauki wani sanda daga wani loko a farfajiya yace masa rieq wannan sandar! Kai sauri kaje shekarta ka kare `ya`yanta daga hatsarin da suke ciki.

Sulaiman ya karvi wannan sanda daga hannun Imam, kai kace a wannan lokaci wannan barbela taji komai, sai cikin nutsuwa ta nufi lambu.

Sulaiman yayi gudu yana bin bayanta ta tsallake wani gajeran Katanga cikin lambu, ya qara bin bayanta har takai qarshen lambun wanda akwai wata qatuwar bishiya sai ta sauka kai.

Sai Sulaiman ya tsaya ya kalli wannan bishiya  saman jijiyar bishiyar wannan waje da reshe ya karkasu anan ta saka sheka sai ga wani baqin maciji yyi sheqa sai ya zamanto `y`yan barbela suna jin tsoro da shiga hatsari, cikin sauri-sauri suka dinga qaraji qwa-qwa.

Barbela ta sauka bayan ta xan zazzaga kaxan ta sanya idonta kan wannan baqin maciji, Sulaiman take ba rareda vata lokaci ba ya sanya sanda ya kawar da wannan maciji ya wurga shi qasa, bayan wannan maciji ya tafi sai Sulaiman ya qara xaga kansa ya kalli wannan sheqa, mahaifiyar jinjirayen barbeloli sai ta zauna kusada sheqa ta dinga murna da nuna farinciki ta nuna godiya ga Imam (a.s) ta hanyar qwa-qwa!

Sulaiman yayi murmushi da yaji muryar barbela yace: kalli Imaminmu mai kirki ji yarda yake fahimtar maganar barbela.     

Tura tambaya