lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Addu’a ita ce sirrin ibada

Addu’a ita ce sirrin ibada

da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Allah mai hikima cikin littafinsa mai daraja yana cewa:

﴿وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِي إِذَا دَعَانِي فَلْيَسْتَجِيبُوا لِي وَلْيُؤْمِنُوا بِي لَعَلَّهُمْ يَرْشُدُونَ

Idan bayin na sun tambaye ka gameda ni to lallai ni ina kusa-kusa ina amsa addu’a mai addu’a idan ya roke ni su nemi amsawa ta su yi imani dani tsammaninsu sa samu shiriya.

bai buya ba Kalmar (tsammani) ta zo a mukamin tabbatuwa da yankewa, saboda sanin Allah da kewayarsa ga komai da komai, kadai dai an yi amafani da Kalmar ne domin fasaha da balaga kamar yadda hakan ya ke a muhallinsa, shiriya ta zo ne sakamakon shimfida da ta gabata a farkon ayar mai daraja, sai a lura.

Wannan aya tana daga cikin mafi kyawun ayoyi da suka zo kan falalar addu’a da bayanin madaukakin matsayinta, daga cikin abin ke nuni kan girman fata da sa rai cikin zukatan bayi, da kuma kasantuwa ka da su kasance daga cikin masu yanke kauna daga rahamar Allah mai girma da daukaka, duk da kasantuwa dukkanin ayoyin kyawawa ne sai dai cewa daga cikin mafi kyawunsa shi ne fadinsa:  

(اللّهم إنّي أسألك من جمالك بأجمله، وكلّ جمالك جميل، اللّهم إنّي أسألك بجمالك كلّه)

ya Allah lallai ni ina rokonka daga kyawunka da dukkaninsa, da dukkanin kyawunka kyakkyawa, ya Allah ni ina rokonka da dukkanin kyanka.

Hakika anyi amfani da lamirin mai Magana cikin wannan aya mai daraja har karo bakwai, wanda ke nuni da shiryarwa zuwa ga Allah matsarkaki, ya ke kuma nuni kan girman yin addu’a, da girma mai yin addu’a da wanda ake kira da rokonsa cikin addu’ar, da girman kyautarsa da karamcinsa da amsa addu’ar bawansa. da girma fata da sa rai da Allah matsarkaki ya kuma ce:

Na farko : shi ne harafin (ya’un) da ya ke nuni zuwa ga lamirin mai magana, cikin fadinsa madaukaki :

 (عبادي)،

Bayina.

Na biyu: harafin (ya’un) cikin fadinsa madaukaki: 

 (عني).

Daga gaeni

Na uku: harafin (ya’un) cikin fadinsa madaukaki: 

 (إني).

Lallai ni

Na hudu: lamirin (fa’ili) mai aiki cikin fadinsa madaukaki

 (أجيب). 

Ina amsa

Na biyar: harafin ya shafaffe da akai hazafi wanda wasali kasa kisra ke nuni zuwa gare shi cikin fadinsa madaukaki:

 (دعانِ)

Ya kira ni.

Na shida: harafin (ya’un) cikin fadinsa madaukaki:

 (لي)

Nawa.

Na bakwai: cikin harafin (ya’un)  

 (ي).

Sannan daga cikin ludufan wannan  aya mai albarka da karamci shi ne :

Farkonta fadin Allah madaukaki

 (إني قريب)

Lallai ni ina kusa-kusa, ma’ana na fi kusa gareku daga jijiyar wuyanku, bari dai shi ubangiji ya na shiga tsakanin mutum da zuciyarsa, ya isheka ka kiraye shi ko da kuwa cikin zuciyarka ne a boye ba tare da wani tsani ba, lallai shi yana kusa kuma mai amsawa ne.

Na biyu: fadinsa madaukaki:

 (أُجيب)

Ina amsa.

Wanda fi’ili ne muzari’i da ya ke nuni kan cigaban aiki da dawwamarsa ba tare da yankewa ba, duk sanda ya kasance, a ko ina ya kasance, ta kowanne yanayi ya kasance , ga kowanne irin al’amari ne ya kasance. Lallai ni ina kusa-kusa kuma ni mai amsawa ne.

Na uku : ita addu’a akankin kanta ibada ce mai zaman kanta, kamar misalin sallah da azumi tare da kau da kai daga amsata, bari dai ya zo cikin hadisin manzon Allah (s.a.w) fadinsa :

(الدّعاء مخّ العبادة)

addu’a ita ce matsayin kwakwalwar ibada.

Daga cikin abin dake nuni kan asalantuwarta da matsayinta kamar matsayin kwakwalwa a cikin jiki, shi ne ita  kwakwalwa na cikin kashin kai kuma ita ce ke tafiyar da sauran gabbai na ciki da na waje jikin mutum da hankali, to haka al’amarin ya ke dangane da addu’a ita ma addu’a na taka irin rawar da kwakwalwa ke takawa sai dai cewa ita na taka tata rawar a rayuwar mutum cikin gundarinta, kamar yadda ya kasance daga falsafar halitta da sirrin rayuwa ibada tare da sani, saboda haka mafificiyar ibada itace addu’a koda kuwa ba a biyawa mutum bukatarsa ba a amsa masa addu’arsa ba, saboda fadinsa madaukaki:  

﴿وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالإِنسَ إِلاَّ لِيَعْبُدُونِ

ban halicci mutum da aljani face don su bauta mini.

Bari dai shi Allah zai amsa saboda alkawalinsa na amsawar, sai dai cewa kuma ita amsa addu’a na da matakai da misdakai kamar yadda al’amarin ya ke a muhallinsa ya kuma kasance sananne wajen ahalinsa, babu wani abu da yake falala wajen Allah daga bawansa ya roke shi abin da ya ke gare shi, wanda ko ya kasance bai rokon Allah zai kasance daga ma’abota girman kai daga bautar Allah kamar yadda Allah madaukaki ke fadi :

﴿وَقَالَ رَبُّكُمْ ادْعُونِي أَسْتَجِبْ لَكُمْ إِنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ

Ubangijinku ya ce ku kirani zan amsa muku lallai wadanda suke girman kai daga ibadata da sannu za su shiga jahannama suna kaskantattu.

 [عن الإمام الباقرعلیه السلام في تفسير الآية : هو الدعاء وأفضل العبادة الدعاء[5].

﴿إِنَّ رَبِّي لَسَمِيعُ الدُّعَاءِ[6]. ﴿قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلا دُعَاؤُكُمْ[7].

Lallai ubangijina mai jin addu’a ne.

ka ce ubangijinku bai damuwa da ku ba don addu’arku ba.

An karbo daga imam bakir (as) cikin tafsirin wannan aya  ya ce ita ce addu’a kuma addu’a itace mafificiyar ibada.

Haka riwayoyi masu tarin yawa sun zo gameda falalar addu’a.

Na hudu: fadinsa madaukaki:  

 

﴿إِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي

Idan bayina suka tambaye ka.

Bai ce idan mutum ya tambaye ka ko idan mutane suka tambaye ka, daga cikin abin dake nuni zuwa ga rahama da jin kain da tausayin Allah da rahamarsa makusanciya ga muminai da masu kyawunta aiki ku kiraye shi kuna cikin kwadayi da tsoro:

 ﴿وَادْعُوهُ خَوْفاً وَطَمَعاً إِنَّ رَحْمَةَ اللَّهِ قَرِيبٌ مِنْ الْمُحْسِنِينَ

Ku kira shi cikin kwadayi da tsoro lallai rahamar Allah na kusa-kusa da masu kyautatawa.

Na biyar: fadinsa madaukaki: (kiran mai kira) ba dukkanin roko da addu’a ke kasancewa kiran mai kira ba, bari ya zama dole ya kasance da gaske ya ke daga addu’a, ma’ana da sharuddanta da kiyaye ladubbanta kamar yadda ya zo cikin littafin (uddatu da’i) na babban malaminmu ibn fahad hulli (rh) lallai ita addu’a nema ne na hakika da ake yinsa da zuciya da kuma harshe, bawai kadai jujjuyar fatar harshe ba tare da lura da fadaka ba da fahimta ba da bukata cikin badinin mutum da zatinsa, yin addu’a da fatar harshe idan ba ta daidai da abin da ya ke cikin zuciya ba to wannan ba za a kirayeta addu’a ba kuma ba ta kasance daga kiran mai kira ba, kamar yadda tilas ga addu’ar da ta dace da amsawa ta kasance kan tsarin halitta da kuma hukuncin shari’a, da dukkanin abin dacikinsa akwai maslaha mai yin addu’ar a kankin kansa, sau da yawan lokuta ba’arin mutane babu abinda ya fi zama masalaha gare su sai talauci, da zasu nemi dukiya daga wurin Allah to da hakan zai cutar da su zai kuma lalata su, sai Allah ya ki amsa bukatarsu saboda son da ya ke musu, kamar yadda ya ke cikin kissar wani mutum munafuki wanda ya mutu cikin munafunci bayan da ya zama mai wadatar dukiya sai yaki bada zakka lokacin da manzon Allah (s.a.w) ya aika dan aike wurinsa ya karbo zakka, kamar yadda kur’ani ya kawo kissarsa da hadisai masu daraja.

ya zama dole cikin addu’a a samu tsantsar yankewa zuwa ga Allah matsarkaki da naci da magiya da rokonsa da kwadayin abin dake wajensa daga alherai da ihsani da jin kai da rahamarsa mayalwaciya, dukkanin addu’a amsashshiya ce, duk addu’a da ka ga ba a amsa ba to ba ta daga hakikanin addu’a, ko da kuwa a zahiri za a kirayeta da sunan addu’a saboda karkada fatar harshe, sannan zunubai suna hana amsar addu’a     

 (اللّهم اغفرلي الذنوب التي تحبس الدعاء).

Allah ka yafe mini zunaban da suke tsare addu’a.

﴿فَادْعُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ وَلَوْ كَرِهَ الْكَافِرُونَ

Ku roke shi kuna masu tsarkake addini gare shi ko da kuwa kafirai ba sa so.

عن سُدير قال: قالت: لأبي جعفر علیه السلام(الإمام الباقر) أي العبادة أفضل؟ فقال: ما من شيء أفضل عند الله عز وجل من أن يسأل ويطلب ممّا عنده، وما أحد أبغض إلى الله عز وجل ممَن يستكبر عن عبادته ولا يسأل ما عنده.

An karbo daga sudairu ya ce: na cewa baban jafar amincin Allah ya tabbata gare shi, ma’ana imam bakir wacce ibada ce mafi falala? Sai ya ce: babu wani abu da yafi falala wajen Allah mai girma da daukaka fiye da a roke shi a nemi abin da ya ke wurinsa, babu wani mutum da ya fi kiyantuwa wurin Allah fiye da mutumin da ya ke girman kai daga ibadarsa  ba ya rokon abin da ya ke wurinsa.

عن ميسر بن عبد العزيز عن أبي عبد الله علیه السلام (الإمام الصادق) قال: قال لي: يا ميسر أدع ولا تقل: إن الأمر قد فُرغ منه، إنّ عند الله عز وجل منزلة لا تنال إلّا بمسألة، ولو أن عبداً سدّ فاه، ولم يسأل لم يُعط شيئاًن فسَل تُعط. يا ميسر، إنه ليس من باب يُقرع إلّا يوشك أن يُفتح لصاحبه.

Daga muyassar ibn abdul aziz daga baban Abdullah (as) imam sadik ya ce mini: ka yi addu’a ka da ka ce: ai al’amarin an riga an wuce shi an gama, lallai wurin Allah mai girma da daukaka akwai wani matsayi da ba a samunsa sai da rokonsa, da a ce bawa zai rufe bakinsa ya ki roko to da ba za a ba shi abubuwa guda biyu ba, ya muyassar ka roka za a baka, lallai yadda al’amarin ya ke shi ne cewa babu wata kofa da za kwankwasa ta face an budeta ga ma’abocinta.

Ya kai `dan’uwana mai girma: shin bayan wannan bayani kana ruduwa da kuma kosawa da gajiya da yin addu’a? yanzu dai daga hannayenka zuwa ga addu’a ka roki Allah komai daga falalarsa kai hatta gishirin dake cikin abinci roke shi, na hore ku da yin addu’a lallai ita addu’a makamin annabawa ce, garkuwar muminai da salihai, amudin addini, karfaffen shinge, hasken sammai da kassai, makullin aljanna da rabauta, maratayun nasara da rabauta, hasken sasanni da ta ke gangaro da arzikai.

﴿ وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِي عَنِّي فَإِنِّي قَرِيبٌ أُجِيبُ دَعْوَةَ الدَّاعِي إِذَا دَعَانِي ...﴾.

Idan bayi na suka tambaye ka gameda ni lallai ni ina kusa-kusa ina amsa addu’ar mai addu’a idan ya kirani….

Allah ya faranta muku ya azurta ku cikin lokutanku ko dawwama cikin alheri muna rokonku addu’a.

Bawan Allah adil alawi

Hauzar birnin qum mai tsarki 13 ga watan shawwal 1438.


Tura tambaya