lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Sallar Istigfari {NIman gafara} da tasirinta.

Da suna Allah mai rahama mai jin qai,

Godiya tatabbata ga Allah mai azurtawa kuma mai ckanken iko tsira da amunci sutabbata ga shugaban annabawa da manzanni Muhammad Al-amin da iyalin gidan sa masu tsarki.

Ina godiya ga ‘yan uwa tasuke tare da mu a wanna shiri namu ,masammama ga wadanda suke yada wanna karatu domin yaxa ilimin iyalan gidan manzo, kamar yadda ‘yan uwa suka sani a zaman da yagabata muntattauna akan tasirin zunufi da yan yin Istigfari a rayuwar duniya .kuma nayimuku al-qawari na sallah domin qara yalwatar arzuqi kamar yadda ni najarbata nagani da idona kuma wasu daga cikin ‘yan uwa muminai suka jarraba suka gani.Kuma shi arzuqin na kuxi ko na ilimi ko matsayi da sauransu,sabo da zaiyiyu mutum yadace a cikin wata xaya ko sati ko kuma rana xaya,to ina roqon mutum idan Allah ya datadda shi ,to ya sanar da ‘yan uwa muminai domin suma su amfana.

Kuma wanna salla itace kamar haka;

Mutum zaiyi niya tayin sallah raka’a biyu domin neman yalwatar arzuqi.

A rakar farko zai karanta Alhamdu sai Ina anzalnahu fi lailatulqada saudaya sai ((سمع الله لمن حمدهsau goma shabiyar sana sai ruku’I sai zikiri na ruku’I kamar haka(سبحان ربّي العظيم وبحمده) kuma bayan shi sai mutum yace (أستغفر الله). Sau goma sanna saiya xago daga ruku’I yace (سمع الله لمن حمده] sai yace (أستغفر الله) kafin sujjada sau goma sai kuma yayi sujjada ga zikirin sujjada(سبحان ربي الأعلى وبحمده) sai (أستغفر  الله) sau goma saai jalasatul istiraha sai (أستغفر  الله) kafa goma sai sujjada tabiyu sai yayi zikirinta kamar yadda yayi nafarko sai (أستغفر  الله) qafa goma sai zama kaxan sakayi (أستغفر  الله) qafa goma sai kuma mutum yatashi domin raka’I ta biyu kamar yadda yayi ta farko,to mutum zaiga adadin Astaqafurllah yakama qafa saba’in da biyar  a raka’a xaya.Bayan yayi raka’I tabiyu sai yayi tashahud da sallama wahida sayace(لا إله إلا الله وحده وحده).daga wanna sai Tasbihati Zahara  Allahu akbar  talatin da huxu 34 Alhamdu lillah 33 subhanallah 33 sai kuma yayi sujjada sai yakaranta wanna(يا مخلّص يونس ابن متّى من بطن الحوت خلّصني).

Dafata Allah yasa mudace amin.

A qarshe inaso na faxamuku wasu wuridai domin qarin arzuqi ga su kamar haka:

1- (یا معطي السائلین) duk wanda yake yawan faxar wanna wuridin ,to Allah zai wadata shi.

2-duk wanda yadauwama akan faxar wana(یا رزاق) to, arzukin shi zai yawaita.

3-duk wanda yake neman wana abu a gwamnatance,to zai karanta fatiha qafa xaya kullin batare da kuskure ba a kowata rana sanna zai karanta wanna addu’ar kafa goma sha uku   (یا مفتح فتّح، یا مفرّج فرّج، یا مسبّب سبّب، یا میسّر یسّر، یا مسهّل سهّل، یا مدبّر دبّر، یا متمّم تمّم، برحمتك یا أرحم الراحمین).

4- duk wanda yadauwama  akan faxar (یا وهّاب) da nimfashi xaya bayan kowata salla yayin dayayi sujjadar shikur,to Allah zai azurta shi.

5-dan neman arzuqi na duniya da lahira,tp mutum zai dauwama akan karanta wanna Ayar sau goma shaxaya(و من یتق الله یجعل له مخرجاً، و یرزقه من حیث لا یحتسب، و من یتوكل علی الله فهو حسبه، إن الله بالغ أمره قد جعل الله لكلّ شیء قدراً) الطلاق 2- 3

Allahamdulillah.

Tura tambaya