lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

dangantakar addini da siyasa

 

1- akwai tabbatar damfaruwar addini da siyasa cikin ba'arinsu da ba'ari da kallon zuwa ga mahiyyar addini da tsarin yadda annabawa suka rayu da ma'asumai amincin Allah ya kara tabbata a gare su da kuma ayoyin kur'ani mai girma.

2- bayanin matsayin mafarar mihwariyyar mutum cikin tunanin masu yunkurin raba addini da siyasa.

3- kari bayani da karin haske kan dalilan kungiyoyin `yan baruwanmu da addini daban-daban da ba da amsa kansu.

Alaka tsakanin addini da siyasa tana misalta daya daga cikin muhimman maudu'ai da batutuwa da ya kamata mai da hankali kansu gabanin bayani bahasosi da suka ta'allaka da hukumar muslunci, idan bayanin wannan alaka da danganta bai tabbatu ba to lallai bahasin maudu'in hukumar muslunci ba zai taba kasancewa mai amfanarwa ba.

Hakika an bijirar wasu adadin ra'ayoyi daban-daban cikin wannan fage, daga wata fuskar wasu sun karfafa larurar raba addini da siyasa, daidai lokacin da wasu kuma ke da'awar danfaruwarsu da juna, sai cewa kuma akwai wasu nazariyoyin daban da maganganunsu ke kai kawo tsakankanin wadannan ra'ayoyi guda biyu.

Da sannu cikin darasinmu za mu bijiro da dalilai da hujjoji da ke tabbatar da ra'ayi na biyu tare da jingina kan mihwariyar mutum, sannan daga baya za mu yi ishara zuwa ga  dalilan ra'ayoyi masu kishiyantar juna sannan muyi bincike cikinsu filla-filla.

A) bahasi kan nazariya mahiyyantakar addini da siyasa

Ana la'akari da dangantaka tsayayya tsakanin addini da siyasa daga cikin samfuri cikin addinin muslunci, saboda haka wajibi kanmu a farko mu kutsa cikin mahangar muslunci ga wannan ra'ayi.

1- alaka da dangantaka tsakanin addini da siyasa kan asasin tahlili da bayani kan mahiyyar addini.

 A baya mun ce lallai shi addini bayani ne kan dukkanin abin dai zai iya kai mutum da kusanta shi daga azurta da farin ciki kuma lallai iradar Allah subhanahu ta shari'a ta tsayu ne kan wannan hadafi.

A hakika shi addini yana bayyanar da iradar Allah wacce za mu iya istinbadinta da fito da ita ta hanyar tsanantuwa da wahayi ta hanyar littafin Allah da sunna, da kuma riskarta da kwakwalenmu da hankulanmu a wani lokacin daban.

Dogaro da wannan mahanga daga addini hukunce-hukunce addini cikin ba'arin wasu lokuta za su wayi gari masu kyawu, a wasu lokutan kuma za su wayi gari marasa kayu, saboda haka maj'mu'ar tasarrufin boye na badini da na zahiri ga mutum wacce dagha cikin sha'aninsu kusanta mutum ga Allah Azza wa jalla suna misalta hukunce-hukunce masu kyau cikin addini, a daidai lokacin da tasarrufofi da ayyuka wadanda suke nesanta shi daga ubangijinsa matsayin abubuwa marasa kyau, a kan wannan asasi a kowanne irin shakali daga shakalai ba zai yiwu a raba addini daga duniya ba,bari dai tilas ne ga dukkanin sha'annunka da mas'aloli duniya su narke a karkashin tutar addini da jagorancinsa.

Da jumla mafi dandaka lallai cikin addini akwai fagage uku da kashe-kashe wanda sune: Akidu, hukunce-hukunce, Akhlak, cikin fagen Akidu suna alankantuwa da asalan Akidu ga musulmai tare da siyasa da shakali cikakke, domin yana misalta tabbatauwar hukuncin Allah da kawo karshen hukumar dagutanci hakan juzu'i daga abubuwan da tauhidi yake hukuntawa, matukar wannan al'amari bai hakkaku ba a hakika to lallai shi tauhidi ba zai taba samun hakkakuwa da cikakken shakali ba.

Kari kan haka lallai ita siyasa boye take cikin gundarin annabta da imamanci hakan ya kasantu ne saboda shi dabbaka hukunce-hukuncen Allah wanda yake bukatar nutsawa cikin bahasin maudu'in siyasa ana kirga juzu'I daga sha'anin annabi ko imami ballantana assasa hukumar a kankin kansa, akwai wasu hukunce-hukuncen addini masu yawan gaske da suke tabo sha'anunnukan zamantakewa da siyasa idan mun nufi tunbukke siyasa daga jikin addini lallai hakan yana hukunta jahiltar wani adadi mai girma daga hukence-hukuncen addini wadanda ake kidaya kumusi da zakka da umarni da kyakkyawa da hani da mummuna da jihadi da sallar jam'i da alkalanci da dabbaka haddodin Allah daga cikinsu  dama wasu kaso kadan daga hukunce-hukunce zamantakewar juna da siyasa cikin muslunci.

Haka al'amarin yake cikin fagen Akhlak shi ma yana kunshe da wani adadi daga hukunce-hukunce da suke ta'allaka da batutuwan siyasa kamar misalin ayyana hakkoki musayan juna tsakanin mutane da abin dai ya yi kama da haka.

2-alaka tsakanin addini da siysa kan asasin tsarin yadda A'imma suka rayu:

Tarihi da tsarin yadda jagororin addini da ma'asumai amincin Allah ya kara tabbata gare su suka rayu kai na bayyana manacewa lallai dangantaka tsakanin addini da siyasa ba ta samu daga wannan zamani ba, bari dai tun fari sun kutsa sasannin siyasa da hukuma ba su yi kasa agwiwa ko raunana daga tabbatar da haduffan addinida dabbaka hukunce-hukuncen addini.

Annabawa amincin Allah ya kara tabbata a gare su ta hanyar rawar da suka taka sun yi la'akari da aiki cikin siyasa wani yanki daga sakon da ya zo musu daga Allah, bari dai hakika wasu ba'arin adadi daga annabwa  amincin Allah ya kara tabbata a gare su sun bugi kirji cikin kutsawa cikin bangarorin siyasa da hukuma kamar misalin sayyidina Sulaimanu da Dauda da Yusuf amincin Allah ya kara tabbata gare su, haka manzonmu mai girma tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi dukkaninsu sun fuskanci wahalhalu da tsanani sai dai cewa su sun sayi hakan da rayukansu da rayuwarsu da hadafin lamintar samar da karfaffar runduna domin shiriyar da mutane

Haka ma tarihin rayuwar A'imma tsarkaka amincin Allah ya kara tabbata a gare su ta kasance wacce take ishara zuwa ga hakikanin kanta ta yanda tarihi ke bamu labarin cewa imam Ali amincin Allah ya kara tabbata gare shi tare da zobaitarsa da zamansa a gidansaa wani dan lokaci bai dinga kutsa kansa cikin sha'anin halifanci ba kai tsaye sai dai cewa tare da hakan bamu same shi ya kauracewa ayyukan siyasa ba kwata-kwata ko da sau daya bari dai ya yi ta sa'ayi da kaikawo ya zuwa lamintar maslahar muminai hatta lokacin da ka kwace masa halifanci daga gare shi, bayan zuruf ya bas hi dama sai ya yi tarayya cikin al'amuran siyasa da shakalin kai tsaye ya kasance halifan musulmi jagoransu, sannan dansa imam Hassan amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya karbi ragamar al'amari bayansa, ya yin da yana yi da zuruf baus bashi dama ba cikin ba'arin wasu lokuta da dabbaka hukunce-hukunce, lallai su sun kasance suna tarayya cikin ayyukan siyasa, sannan hallararsa  fagagen siyasa na yawaita da shakalai daban da munasabobi masu yawa.

Tura tambaya