lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Mene ne ma’anar fadin jumlar (iliminsa yafi hankalinsa yawa) shin wannan jumla za ai la’akari da ita suka zuwa ga Sayyid Kamalul Haidari?

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah kamar yadda shi ya cancanci hakan kuma shi Ahalin hakan ne, tsira da aminci su kara tabbata ga mafi daukakar halittu Muhammad da iyalansa.

Dan’uwa mai tambaya mai daraja amincin Allah ya tabbata gareka da rahamarsa da albarkunsa.

Bayan haka: lallai ni ban kasance cikin amsa tambayar mai tambaya ba-dangane da tsarin tafiyar Sayyid Kamalul haidari-cikin fadina (ilimins ayafi hankalinsa yawa) cikin mukamin sukan Kamalul Haidari ko yabonsa ku gulmarsa da yi masa kage-Allah ya tsare ni daga aikata haka-kamar yadda jumlar na daukar abubuwa biyu, kamar yadda ba’arin wasu malamai suka siffanta cikin mikewar tarihi wani lokaci kan zuwa cikin yabo wani karon kuma suka, kadai ni abin da na nufa shi ne bayyana bakin ciki da tsananin ban takaici  daga rashinsa ga ilimi da hauza gamammen rashi da kebantacce, abin da ya dace shi ne daga gareshi da ire-irensa shi ne su sanya iliminsu cikin hidimtawa hauzozin ilimi wacce kashinsa da namansa ya karfafa daga gareta, kamar yadda da ya kasance cikin munakasha da rushe afkar din wahabiyawa batattu masu batarwa, hakika a wancan lokaci ya sanyaya zukatan muminai sai dai cewa abin da ya faru da shi ya faru da shi har ya zama abin da yake kai yau daga cikin abin da ke yanke damfaruwa zuciya ta yadda a kasance daga gremu cikinmu koma bayan makiya daga gabas da yamma. shi kafirci akida ce guda daya, lallai yanzu ana kidaya shi daga masu kishiyantar hauza da marja’iyya da sabani da ita lokacin da ake sannafa mutane daga aboki da kishiya, matsalar itace wasu na tsammaninsa cewa shi yana kyawunta aiki ne yana kuma son cigabantar da cibiyoyin addini kamar yadda shi yake fadi da bakinsa, sai ya kama kwarara kan wannan makwarara wacce ke bakantawa abokanai masoya, ta ke kuma farantawa  makiya masu sabani damu, wannan shi ne  abin da girman kan duniya da masu mulkin mallaka gabas da yamma da karnukan farautarsu suke so suke kuma yadawa a wannan yanki da muke ciki sakamkon tsoran da suke yi daga buwayar shi’anci da shi’a masu karmaci, sai dai muce innalillahi wa inna ilahi raji’un.

Sannan kuma sai ka ga mabiyansa daga wasu ba’arin samari matasa rudaddu musammam ma masu tunanin almaniyanci (kore samuwar addini) daga cikinsu da kuma `yan zamani `yan birni wadanda suke sukan hauza hauza da marja’iyya kamar mabiyan shaik Abdul-halim gazzi da wanda ya kasance kan tsarin tafiyarsa, mai makon ya baiwa hauza da marja’iyya kariya daga tushen taimakon sayyid wane ko shaik wane, bai san cewa dukkaninmu fansa ne ga hauza mai albarka ba. lallai hauzozinmu na ilimi masu albarka tare da dukkanin gabobinsu daga maraji’ai masu shiryarwa zuwa ga dalibin ilimi na ajin fari cikin zamanin gaiba kubra itace hankali mai tunani fitilar shiriya zuciya mai numfashi ga shi’a da shi’anci, sannan wannan zamanin namu hauza itace izza da karama da runduna mai ishurwa yaki ta karfe kan kishiyantar makiya addini da mazhabar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata garesu ma’abota tunani.

Amma dangane da tsarin tafiyarsa da manhajiyarsa lallai ni nayi imani da cewa lallai duk wata minhajiya da tsari da yake gangaro daga wanda ba maasumi ba to ana tsammanin kuskure da dacewa cikinsa, saboda haka babu abind aya rage a wannan lokacin face mu ladabtu da ladabin kur’ani mai girma cikin fadinsa madaukaki:       

 (الذين يستمعون القول فيتبعون أحسنه)

Wadanda suke sauraron zance subi mafi kyawunsa.

Sai dai cewa idan magana da minhajiya cutarwarsu ta shallake amafaninsu lallai za su kasance matsayin albarasa wacce cutarwarta ta wuce amfaninta, shan digo daya daga gareta yana wajabta haramci da najasa. Amma ayyana hakan lallai shi yana komowa wurin mukallafi da kansa idan ya kasance daga ma’abota ilimi amma idan kuma ya kasance mutum gama gari ba’ame to sai ya koma ga ma’abota ilimi da kwarewa (ku tambayi ma’abota ambato idan kun kasance baku da sani)

Ku dauki abin da ya shahara tsakankanin sahabbanka ka yi watsi da abin da ya karantu ya ratse.

Allah ne mai karewa mai taimako lallai shi mafi alherin mai tallafi da taimako, muna rokon Allah matsarkaki muna kamun kafa da sahibuz-zaman  Allah ya gaggauta yayewarsa da bayyanarsa ya kuma shiryar damu baki daya zuwa ga alheri da daidai da taufiki da datarwa ya kuma azurtamu da kyakkyawan karshe, baki dayan mu komawa masdarin izzarmu da karfinmu da karamarmu  hauza ilimiya mai albarka shiryayya mai shiryarwa, amin amin karshen maganarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.   

Tura tambaya