lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Shin saukar kur’ani daga tajalli ne ko ko daga nisanta ne?

 

Shin saukar kur’ani daga tajalli ne ko ko daga nisanta ne?

                               

Lallai abin da muke kudircewa babu shakka ko kokwanto cikinsa lallai cewa: duk sanda kur’ani ya hallarar da surarsa da ayoyinsa da kalmominsa da mafhumansa (ma’anoninsa) daga cikin abin da ke cikinsa da abin da ke tattare da shi cikin kowanne lamari cikin kowanne irin zamani da bigire, lallai tsato tsarkaka na hallara tare da shi ma’ana Muhammad da mutanen gidansa (as) da irin wannan mustawar ba tare da sabawa ba ko tawaya, haka ma akasin haka, domin su biyun abokan tarayya ne da  basa rabuwa da juna basa banbanta cikin kowanne irin abu cikin duniya da lahira, da nassin hadisin saklaini sananne tabbatacce daga litattafn hadisan shi’a da sunna  kamar yadda ya zo daga manzon Allah (s.a.w) sannan ba boyayyen abu bane cewa duk wanda ya koyi ilimi ya samu sanin wanbi abu daga kur’ani da tsatso tsarkaka, lallai shi da wannan mikdari mutumtakarsa zata samu da imani da da kamalar rayuwarsa shi daya da rayuwarsa da sauran jama’a, za ta bayyana cikin tafiyarsa da sulikinsa cikin rayuwarsa ta game gari da kebantacciya.

Maganar mu cikin kur’ani da saukarsa kan zuciyar annabi mafi karamci (s.a.w)  domin ya kasance  mai bushara da gargadi daga ubangijin mai rainon talikai, daga cikin mutane akwai masu ganin kur’ani ya sauka kamar misalin saukar ruwan sama daga nesa can, ma’ana cikin saukarsa ya kasance yanki-yanki a yayyanke  da nesanta, idan ya kasance a samaniya, lallai bai kasance tsakankanin mutane ba sai bigirensa ya zama nesa-nesa mai wofinta, idan ya kasance a doron kasa tsakankanin mutane, lallai shi bai kasance a samaniya ba cikin madaukakan halittu, shi nesa-nesa idan aka auna shi da kasa to ya na samanta ne haka akasin haka, bayan saukar kur’ani daga masdarinsa da farko da sannu zai yanke, a wannan lokaci kuma masu tafsrinsa suke fara tafsirin kur’ani irin tafsrin duniyar kasa shimfidadda, hannu dniyar kasa bai iya kaiwa ga yin tafsirn duniyar sama ta al’arshi, misalin wannan tafsiri ga kur’ani da sannu zamu shaki kamshin tafsirin duniyar kasa da turbaya kai hatta ko da ya zurfafa bincike cikinsa, lallai kamar misalin wanda ya yi nusto ne cikin tafki domin fito da gwalagwalai, sai dai cewa tafki na wanzuwa a ban kasa daga kasa, sai tafsiri a wannan lokaci ya kasance ya yanko daga sama ya damafaru da kasa amma a wajeen masu dandake bincike  daga malamai bayin Allah nagargaru lallai shi saukar kur’ani mmai girma kadai dais hi da yanayin igiya mikakka mara yankewa daga sama, bari gfe guda na hannun Allah matsarkaki daya gefan kuma na hannun mutane, lallai shi daga tajalli yake bai ksance daga nesa-nesa ba nesanta, sai ya sauka daga wajen Allah matsarkaki madaukaki da haruffansa da lafuzzansa da ma’anoninsa a kan zuciyar tsarkakka ga saukar igiya mikakk, duk wanda ya yi riko da shiya tsira ya `daga zuwa sama, kamar misalin wanda ya yi riko da igiya mikakka domin fitowa daga cikin rijiya da fada cikinta, sannan ya `daga da shi zuwa sama, ga ubangijinka tukewa ta take, duk wanda ya yi imani da wannan ya kuma nufi tafsiri da yin sharhin kur’ani mai girma, to fa lallai shi kari kan tafsrinsa na kasa lallai zai tafsrinsa irin tafsirin sama na malakutiya  daga la’arshi ubangiji mai rainon bayi, a wannan lokaci banbancin nawa ne tsakanin tafsiran guda biyu na sama da na kasa, banbanci nawa ne tsakanin sauka irin ta ruwan sama da kuma irin ta mikakka igiya (tajalli) da (nesa), shi kur’ani mao girma igiya ce karfaffa, kuyi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba, lallai Allah ya rataye shi tsakaninsa da tsakankanin bayinsa, wannan igiya bata kasance yankakkiya ba kamar misalin igiya da ta yanke ta fada gidan wani mutum, lallai shi ba zai samu dagawa ba zuwa madaukaka, bari daga igiya mikakka gefe guda da yake hannun Allah da iliminsa da ikonsa da rayuwarsa.

Shin saukar kur’ani sauka ce irinta ruwan sama daga nesanci da ma’anar kasantuwa daga sama, bai kasance kasa ba haka ma akasin hakan, ko kuma shi daga sauka irinta igiya daga tajalli wanda amirul muminina ali (as) cikin nahjul balaga inda yake cewa:

               

 (فتجلّى لهم سبحانه في كتابه من غير أن يكونوا رأوه).

Sai ubangijin matsarkaki ya yi tajalli garesu cikin littafinsa ba tare da ya kasance sun ganshi ba.

 

Duk wanda da farko tafsirinsa daga kasa duk yarda ya kai ga zurfafa kamar misalin zurfafar kogi, sai ka kamsashi kamshin turbaya da kasa ya launantu da launin kasa da fatarsa mai launi-launi. Idan aka ce shi ruwa cikikn saukansa da tattararsa  yana zama tafki, kamar yadda tafki yake da sama da zurfi, zahiri da badini, duk wanda ya ga tafki, lallai shi wani lokaci samansa da zahirinsa, wani lokacin kuma zurfinsa da badininsa, sai muce idan hakan ya kasance ya kasance daidai ya inganta sai dai cewa duka biyun suna tukewa zuwa ga kasa, lallai shi tafki daga kasa yake gareta yake komawa, kamar yadda kake gani cikin misalin tafsirin fakruz razi da jarullahi zamakshari da wanda ya kasance da irin tunaninsu, ya yinda da suke ganin saukar kur’ni daga irin misalin saukar ruwan sama ba tare da ya sadu ba bayan saukarsa da sama daga duniyar badini da jabrut. Amman wanda yake ganin cewa saukarsa daga irin mahangar saukar mikakkiyar igiya ne mai saduwa da hadewa kamar misalin ayatollah husaini taba’taba’I a cikin tafsirinsa almizan fi8 tafsiril kur’an, lallai shi zaka shaki kamshin malakutiyya badini, yanada zahiri kamar yadda yake da zurfafa mafi girma cikin tawilinsa, kadai dai wanda dai wanda yake sanin kur’ani shi ne wamda aka saukarwa kur’anin akai magana da shi da kur’anin, kamar yadda kake kamsasar kamshin kasa daga gareshi, ka ga haskayen al’arshi, kamar yadda ya kasance daga tafsirin mala’ikanci da shuhudi daga tafsirin badinin da gaibu.

Daga wanda yake tafsirin kur’ani wani lokaci ya kanyi tafsirinsa daga wajen Allah na farko yana daga tajalli na biyu kuma daga nisanci. 

 Na farko yana ganin cewa dukkannin ni’imomi daga wajen Allah matsarkaki suke

 

﴿وَمَا بِكُمْ مِنْ نِعْمَةٍ فَمِنْ اللَّهِ ﴾.

Babu wata ni’ima da take gareku face daga Allah take.

 

Kamar yadda yake ganin cewa lallai abin da yake cikin doran kasa  na daga runudunonin Allah

 

﴿وَلِلَّهِ جُنُودُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ﴾.

 

Ga Allah sojojin sammai da kasa suke.

 

Sai ya ga kasa sai dai cewa ita tana rataye tanada alakantuwa da sama, da bainda ke amafanar da mutane da al’umma  cikin tafsiri da tawili ga kur’ani mai girma da abin da ya kasance mahangar mai tafsirin dangane da saukar kur’ani daga misalin mikakkiyar igiya  mara yankewa daga Allah matsarkaki, lallai duka wanda ya yi riko da shi daga wadanda Allah ya kareshi ya tseratar da shi, domin ismarsa da tabbatuwar ilimi da ma’arifa da daukaka cikinsa, ya kasance misdakin abin da riwaya ta zo cikinsa (karanta ka daukaka) ma’ana da iliminka da riko da igiyar darajarka zata daukaka ka `daga zuwa ga aljannar Firdausi madaukakiya tare da makusanta  cikin aljanna korama cikin matsugunin gaskiya wajen sarki mai iko, duk wanda yake da ittisali da dangantaka da sama da iko mudlaki da ilimi mudlaki da rayuwa mudlaka wacce take daga siffofi  na zati da subutiya ga Allah madaukaki matsarkaki ka da ya debe tsammani daga rahamar Allah, kamar yadda kada ya yi magana da debe sarai da munanawa da abubuwa marasa kyau, bari dai kowanne lokaci ya kamata ya rayu cikin kyawawan fata da rahama da nishadi, sannan kur’ani da tsarkakakken tsatso  hakika ce kwaya daya daga wanda shi daya ne dayantacce  da ubangijin masu raino girmansa ya girmama. Babu shakka duk wanda ya kasance daga ahalin wannan hakika, lallai shi zai kasance ma’abocin dayanta Allah a zahirinsa da badininsa zai kira zuwa ga Kalmar tauhidi da kuma hada kai. Zai hada kan al’umma da jama’a.

Sannan ka sani lallai sabani da rarrabuwa da kungiyanci da bangarori wani lokaci daga kasa tsakanin ahlin kasa, to wannan zai iya yiwuwa a magance shi da dinke barakarsa da hada zukata da sahu-sahu hakan na kasancewa ta hanyar wa’azi da nusantarwa daga masukawo gyara cikin al’umma da ma’abota addini cikin warware matsaloli da sabani da kawar da rigingimu da jayayya  ta daidaiku da jama’a da dinke Baraka da hada kawuka da sahu-sahu.

Sai dai cewa yana kasancewa sababin sabanin da rigima da juna da kiyayya da gaba daga abin da sama ta wurgo daga Allah Allah madaukaki matsarkaki, to fa maganin wannan bai kasancewa misalin yin wa’azi , bari ya zama tilas a komawa Allah ayi masa magiya da kan’kan da kai da kuka zuwa gareshi matsarkaki har ya dauke bala’in da fitintunun da musibun daga kafadun mutane lallai wannan sabanin da sassabawar na daga azabar Allah, kadai wani lokaci yana kasancewa ta fuskanin wurgowa wani lokacin kuma da yanayin cune kamar yadda ke cikin surar ma’ida  dangane ga yahudawa da nasarawa, lallai tare da yahudawa ya bayyana sabaninsu da rigima da juna da yanayin wurgowa kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

           

﴿ وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمْ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ ﴾.

 

Muka wurga kiyayya da gaba tsakankaninsu har zuwa ranar kiyama.

 

Amma dangane da nasarawa kiristoci to bayanin ya zo kansu da yanayin cune.

 

﴿ فَأَغْرَيْنَا بَيْنَهُمْ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ﴾.

 

Sai muka cuna adawa da keta tsakaninsu har zuwa ranar kiyama.

 

Cikin wata ayar daban ishara ta zo ga asalin azabar  da saukarta  daga sama daga kasa sai Allah madaukaki yace:

 

﴿قُلْ هُوَ الْقَادِرُ عَلَى أَنْ يَبْعَثَ عَلَيْكُمْ عَذَاباً مِنْ فَوْقِكُمْ أَوْ مِنْ تَحْتِ أَرْجُلِكُمْ أَوْ يَلْبِسَكُمْ شِيَعاً وَيُذِيقَ بَعْضَكُمْ بَأْسَ بَعْض﴾.

 

Ka shi mai iko ne kan aiko da azabba kanku daga samanku ko kuma daga karkashin kafafuwanku ko ya gauraya ku kungiyoyi ya dandanawa sashenku musibar sashe.

 

Azaba mai sauka daga sama a wani lokaci tana zuwa misalin walkiya mai konewa wani lokacin kuma misalin azaba tsakankaninsu, it ace mafi tsananin azaba daga ta farko. Duk wanda yake ganin kur’ani ya sauka  misalin mikakkakiyar igiya da kuma tajalli daga Allah matsarkaki, to lallai shi babu makawa zai kira cikin maganganunsa da nusantarwarsa ya zuwa hadin kai tare da kashe-kashensa musammam ma hadin kai na muslunci a kebance kuma hadin `yan shi’a, domin su zauna kan walimar Allah mai girma da daukaka, shi ne kur’ani wanda ya yi tajalli cikinsa Allah da girmansa da kyawunsa da kamalarsa.

Ina hada ku da Allah kan hadin kai da hada kawukan musulmi da muminai, ina hada ku da Allah kan hadin kan dayanta Allah da hadin kan mutumtaka.

Idan kuma kuka ki yi to ku sani  lallai shi sabani da rigingimu tsakankanin muminai kadai dai sabani tsakankanin muminai azaba ne daga Allah matsarkaki, azaba da samanku daga karkashin kafafuwanku  mafi tsanani    

﴿ يَلْبِسَكُمْ شِيَعاً وَيُذِيقَ بَعْضَكُمْ بَأْسَ بَعْضٍ ﴾

 

Sai dayanku ya kafirta dayanku ya tofa miyau a fuskarsa kamar yadda ya zo cikin hadisan tankada da rairaya cikin karshen zamani ya tofa miyau a fuskarsa kamar yadda hakan ya zo cikin hadisan tanakade da rairaya a cikin karshen zamani wannan yana daga cikin mafi tsananin azaba kan al'umma  cikin rasa kyautata zato da rashin aminci tsakankanin junansu, kowannensu yana bugun dan'uwansa yana cin namansa, kungiyoyi su dinga dukan juna dabangaranci tsakaninsu, Allah ya sanya azabarsu tsakaninsu  alhalinsu su suna daga al'umma guda daya kan mazhaba daya.

Duk wanda ya kasance ma'abocin tauhidi ciki badininsa da zuciyarsa lallai shi zai bayyana shi cikin maganganunsa da da'awarsa cikin zantuaknsa da ayyukansa, sai ya zamanto yana kira zuwa ga hadin kai da daidaita juna. Daga cikin zamnatakewa da juna da rayuwa da juna cikin zaman lafiya  da kyautata yan zama waje guda shi ne kiyaye hakkokin ragowar mutane da rashin cuatr da `yancinsu na mutuntaka, ammam wanda ya kasance mushriki  cikin zuciyarsa da badininsa, lallai hakan zai bayyana cikin fuskarsa cikin maganganunsa wadda bayanta akwai sassabawar mutane da rarraba su zuwa bangarori da kungiyoyi azabarsu tsakanin junansu.

Ma'abocin taiuhidi a hakika bai ganin mutum matsayin dabba mai magana kamar yadda masana ilimin mandiki sukai bayaninsa a haka  bari yana ganinsa rayayye mai imani da Allah sai ya zama yana alakanta shi da rayuwar Allah matsarkaki da sama, ya komar da shi zuwa asalinsa da ma'adanarsa, lallai ruhinsa daga duniyar badini daga sama kamar yadda ya zo ckin fadinsa madaukaki:  

﴿وَنَفَخْتُ فِيهِ مِنْ رُوحِي﴾

Na yi busa cikinsa daga ruhina.

 

Ruhi mala'ika ne mai girma da ya fi jbrilu girmama ana kiransa da sunan ruhil mukaddas ko akdas shi yana daga malakut mafi daukaka,

 ﴿ آمَنُوا اسْتَجِيبُوا لِلَّهِ وَلِلرَّسُولِ إِذَا دَعَاكُمْ لِمَا يُحْيِيكُمْ ﴾

 

Ya ku wadanda sukai imani ku amsawa Allah da manzonsa idan suka kiraku zuwa ga abin da yake rayaku.

 

Suna kiranku zuwa rayuwa madawwamiya ta har abada ba ta yammaci ko gabshi, bari igiya mikakka daga Allah matsarkaki ga wanda ya yi riko da ita

 

﴿وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعاً وَلا تَفَرَّقُوا﴾.

Kuyi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba.

 

Lallai Allah yana so masu riko da karfaffiyar igiyarsa da kur'aninsa mabayyani da Muhammad da iyalnsa tsarkaka, karshen zancenmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.

 

Bawan Allah sayyid adil alawi

15 ga watan Ramadan shekara ta 1438

Tura tambaya