lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

sakafa da sakafantacce a mahangar muslunci

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai tsira da aminci su kara tabbata ga mafi daraja da daukakar halittu baki daya Muhammad da mutanensa zababbu tsarkaka, tsinuwa madawammiya ta kara tabbata kan makiyansu baki daya har zuwa ranar tashin kiyama.

Ya ubangiji ka yalwata kirjina ka yassare mini lamarina ka cire kulli daga kan harshena don su fahimci magana ta.

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ya zo cikin hadisi madaukaki cewa:

 

 (ان أبي ذرّ& قال: يا رسول الله| ما فضل من تذاكر في طلب العلم، فقال له الرسول| كان كمن ختم القرآن الكريم، ثم قال له كمن ختم القرآن؟ فقال له الرسول|: كان كمن ختم القرآن اثني عشر ألف مرة.

 

Lallai bau zarru gifari (rd) yace: ya manzon Allah wacce falala ce daga yin muzakarar ililmi, sai manzon Allah (s.a.w) yace masa: ya kasance kamar misalin wanda ya sauke kur’ani mai girma tunda bakara har nasi, sannan yace masa: ya kasance kamar wanda ya sauke shi karo dubu.

Da sannu kowannenmu zai rabuta da kari daga ilimi da ma’arifa da tadabburi cikin kur’ani mai girma  bayan kammala kowacce muhadara mafi karancin abin da zai rabauta da shi shi ne samun lada daga saukar kur’ani sau dubu goma sha biyu, me yafi kyawunta daga abin da muke kai muke cikinsa, wannan yana biye da kyakkyawar niyyar mutum da fafutikarsa da kaikawonsa kamar yadda Allah madaukakin sarki ke fadi:

 

﴿وَأَنْ لَيْسَ لِلإِنسَانِ إِلاَّ مَا سَعَى﴾.

Lallai babu abin da ke ga mutum sai abin da yayi sa’ayi.

 

(وإنّما الأعمال بالنيات وأنّ لكل إنسان ما نوى)

 

Kadai ayyuka na tare da niyyar da akayi su lallai kowanne mutum na tare da abin da yayi niyya.

 Ya zo cikin riwaya daga imam sadik (as) cikin fadinsa:

 

 وفي الرواية عن الإمام الصادق×: (يحشر الناس في يوةم القيامة على نياتهم).

Ranar kiyama za a tashi mutane kan niyyasru.

 

﴿ الم * ذَلِكَ الْكِتَابُ لا رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِلْمُتَّقِينَ * الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ وَيُقِيمُونَ الصَّلاة وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ﴾.

Alif, lamu mim*wancan littafin babu kokwanto cikinsa*shiriya ga  masu tsoron Allah* wadanda suke imani da gaibu suke tsayar da sallah daga cikin abin da muka azurta su suke ciyarwa.

 

Asasi kur’ani shi ne littafin shiriya kamar yadda aya mai albarka take ishara zuwa ga haka sai dai cewa shiriya ga wanda Allah ya shiriyar.    

﴿إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ﴾.

Lallai kai baka shiriyar da wanda kake so sai dai cewa Allah yana shiriyar da wanda ya so shi ne mafi sani da masu shiriyuwa.

 

Lallai kur’ani tabbatacce cikin kasantuwarsa daga Allah yake da ingancin hakan sai dai cewa fahimtarsa ba ta saukaka ga kowa ga kowa ba ma’ana da shi shi tabbas daga Allah yake sai dai cewa babu masu iya fauskantarsa sai wadanda akai masu magana da kur’anin, saboda shi kur’ani akwai ayoyi bayanannu cikinsa da masu kamanceceniya da juna ta yadda Allah madaukakin sarki ke cewa:

﴿إِنَّهُ لَقُرْآنٌ كَرِيمٌ * فِي كِتَابٍ مَكْنُونٍ * لا يَمَسُّهُ إِلاَّ الْمُطَهَّرُونَ * تَنزِيلٌ مِنْ رَبِّ الْعَالَمِينَ﴾.

Lallai shi kur’ani ne mai girma* cikin wani littafi tsararre* babu masu shafarsa sai wadanda aka tsarkake* sauka ne daga ubangijin talikai.

 

Anan wajen bata nufi taba littafin Allah ba duk da kasantuwar akwai hani na shari’a mutum ya taba shi alhalin baya cikin tsarki, ya haramta gareshi ya taba rubutun kur’ani alhalin bai da tsarki, sai dai cewa abin nufin da shafa cikin wannan aya shi ne rashin yiwuwa cimma hakikaninsa da zurfin ma’anoninsa ga wadanda ba Muhammad da iyalansa tsarkaka, ma’anar mai rowatacciyar shiryarwa shi ne sabanin fuskanta daga mutane kowacce aya tana dauke da fiye da ma’ana guda daya wannan ya nuni kunsar girman kur’ani  da cewar shi ayarsa bata faduwa ta fassaru da ma’ana daya, muna lura cewa akwai tafsirai daban-daban mabanbanta cikin fadinsa madaukaki:

 

﴿إِنَّا أَعْطَيْنَاكَ الْكَوْثَرَ﴾.

Lallai mu munyi maka kyautar kausara.

Sayyid daba’daba’I cikin tafsirin mizan ya fitar da fiye da ma’ana goma sha hudu kan ma’anar kausar: alheri mai tarin yawa, korama a cikin aljanna, fadima zahara….har zuwa karshen ma’anonin.

Tabbas a’immatu ahlul-baiti (as) tare da malamai sun bada himma da kokari mai girma cikin baiwa kur’ani kariya bayan manzon Allah (s.a.w) hakika malamai sun wallafa dubban litattafai da darasussuka karfafa cikin kur’ani da ilimansa da ma’arifofinsa, da bainda ya alakantu da shi daga ilimin lugga da kira’a da tafsiri da tarihi da tashri’I, kadai masu tsarkin niyya daga mabiya kur’ani ke kwadayin al’umma ta dawo zuwa ga kur’ani ta rike hanya da tsari da kundin tsarin ga rayuwa, tushen karbar wayewa da tunani da sakafa, ma’aunin gane daidai da ba abin da ba daidai ba, abin komawa cikin neman warware sabani, tushem hadin kai  da watsi da rarrabuwa.

 

﴿وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعاً وَلا تَفَرَّقُوا وَاذْكُرُوا نِعْمَةَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنْتُمْ أَعْدَاءً فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُمْ بِنِعْمَتِهِ إِخْوَاناً وَكُنْتُمْ عَلَى شَفَا حُفْرَةٍ مِنْ النَّارِ فَأَنْقَذَكُمْ مِنْهَا كَذَلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمْ آيَاتِهِ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ﴾.

Kuyi riko da igiyar Allah baki daya kada ku rarraba ku tuna da ni’imar Allah yayinda kuka kasance abokan gaba da juna ai ya hada zukatanku sai kuka wayi gari da ni’imarsa `ya’uwan juna  kun kasance kanbakin ramin wuta sai ya tseratar da ku daga ita Allah yana bayyana muku ayarsa tsammaninku kwa shiriya.

 

﴿وَأَنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيماً فَاتَّبِعُوهُ وَلا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ﴾.

Lallai wannan hanyata ce mikakka ku bita ka da ku hanyoyi sai su rarrabaku daga barin hanyarsa wadancananka yayi muku wasiyya da shi tsammaninku kwaji tsoran Allah.

 

Me sakafar kur’ani take nufi? Sau da yawa Kalmar sakafa da ma’abocinta na kai kawo, sau da yawa wanda ke amfani da Kalmar na nufin wasu adadin ma’arifofin wadanda mutum ke samunsu. Sannan sakafantacce bisa wannan fahimta shi ne wanda ya tattaro wadannan ma’arifofi ko kuma wanda ya samu shaidar kammala karatu musammam cikin mustawan jami’a, wannan abin da mafi yawan mutane ke fuskanta kan Kalmar saka da sakafantacce, cikin wannan takaitaccen bahasin muna son yin bahasi ciki muna son sanin ma’anar sakafa da sakafantaccen mutum karkashin mahangar kur’ani:

 Kamus-kamus din harshen larabci sun bayyanar Kalmar daga (sakafa) sai suka sanya wasu ma’anoni a gabanmu kamar haka: ya zo cikin littafin mufradatul ragibul isfahani: Kalmar (sakfu) shi ne hazikanci cikin riska abu da aikinsa, daga nan ne aka aro (musakafa) ana cewa (sakiftu kaza) idan ka riskeshi da kwayar idanunka saboda kaifin nazari, sannan ake izini cikinsa akai amfani cikin riska ko da kuwa tare da shi babu sakafa.

  Ya zo cikin kamus din mu’ujamul wasid (asakafa shai`un ) ma'an ay mikar da karkatarsa ya daidaita shi, (sakkafa insanun) ma'ana ya wayar da shi ya tarbiyantar da shi ya ilimantar da shi, idan mun san mafhumin sakafa cikin kamus-kamus harshena larabci ma'ana cikin sashen ma'anoninsa: kaifin basira da dandakewa  cikin fuskantar ma'arifa  da hazaka da kwarewa cikin ilimi da ma'arifa da sani, da daidaita karkatacce da mikar da shi da cire kare-kare daga cikinsa, daga wannan mafarar ya zama wajibi mu fahimci isdilahin sakafa da sakafantacce muyi amfani da kalmar, ba zamu kirayi mai koyon karatu ba da sakafantacce mataukar dai bai bi daidaitaccen suluki ba, ya tsarkake sulukinsa da shaksiyarsa daga karkata daga barin gaskiya da tabarbarewar halaye da kyawawan dabi'u, lallai sakafar kur'ani na nufin dadaita sulukin mutum da tace shi da tsara gina kai ga mutum kan tushen mai kyawu da dokokin kur'ani, domin ya kasance ya siffantu da kur'ani cikin tunaninsa da sulukinsa da tsarin tunaninsa, wanda hakan ake kira da (istikama) daidaituwa  

﴿اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ﴾.

Kashiryar da mu tafarki madaidaici.

﴿فَاسْتَقِمْ كَمَا أُمِرْتَ وَمَنْ تَابَ مَعَكَ وَلا تَطْغَوْا إِنَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ﴾.

Ka daidaita kamar yadda aka umarceka tare da wadanda suka tuba tare da kai kada kai dagawa lallai shi yana ganin abin da kuke aikatawa.

 

Saboda haka ya hana karkacewa da ratsewa yana kuma inkarin wannan suluki karkatacce.

 

﴿فَأَذَّنَ مُؤَذِّنٌ بَيْنَهُمْ أَنْ لَعْنَةُ اللَّهِ عَلَى الظَّالِمِينَ * الَّذِينَ يَصُدُّونَ عَنْ سَبِيلِ اللَّهِ وَيَبْغُونَهَا عِوَجاً وَهُمْ بِالآخِرَةِ كَافِرُونَ﴾.

Sai mai yekuwa yayi yekuwa tsakaninsu lallai la'anar Allah kan azzalumai* wadanda suke kora ga barin tafarkin Allah sune nemanta karkata alhalinsu suna kafircewa lahira.

 

Lallai kur'ani yana kawowa mutane wayewa da sakafa da samun canji da sauyi.

Lallai sakafar kur`ani tunani wacce yakewa mutum magana da ita wadda ita ce ma'abociyar shaida da hadafin ilimi, dukkanin tunaninsa da sakafarsa  shi ne don aiki, kai hatta sakafar akida da hankali, ita ce asasi mafara ga suluki da aiki, shi ya sanya yake watsi da fada babu cikawa hakan ya zo cikin fadinsa madaukaki:

﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا لِمَ تَقُولُونَ مَا لا تَفْعَلُونَ * كَبُرَ مَقْتاً عِنْدَ اللَّهِ أَنْ تَقُولُوا مَا لا تَفْعَلُونَ﴾.

Ya ku wadanda sukai imani menene ya sa kuke fadin abin da bakwa aikatawa* ya girma kasantuwarsa abin kyama ace kuna fadin abin da bakwa aikatawa.

 

A wani muhallin kuma yana alakanta tsakanin imani na nazari da aiki na dabbakawa.. ana ganin rabasu guda biyun da juna matsayin wata babbar asara ga mutum, Allah madaukakin sarkina cewa:

﴿ وَالْعَصْرِ * إِنَّ الإِنسَانَ لَفِي خُسْرٍ* إِلاَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَتَوَاصَوْا بِالْحَقِّ وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ *﴾.

Na rantsuwa da zamani* lallai mutum yana cikin hasara* sai dai wadanda sukai imani sukai aiki nagari sukai wasicci da gaskiya sukai wasicci da hakuri.

 

Sannan ya fuskantar da mutum aiki da dabbaka tunani da sakafa ta nazari cikin suluki da matakai, ya yi kira zuwa ga jikkantuwa da ita a aikace cikin rayuwa, zamu karanta cikin wadannan bayanai:

﴿وَقُلْ اعْمَلُوا فَسَيَرَى اللَّهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالْمُؤْمِنُونَ﴾.

Kace kuyi aiki da sannu Allah zai ga aikinku da manzonsa da muminai.

 

﴿وَأَنْ لَيْسَ لِلإِنسَانِ إِلاَّ مَا سَعَى * وَأَنَّ سَعْيَهُ سَوْفَ يُرَى﴾.

Lallai ba abin da kega mutum sai abin da yayi sa'ayi*lallai da sannu za a ga sa'ayinsa.

 

﴿قَدْ أَفْلَحَ مَنْ زَكَّاهَا * وَقَدْ خَابَ مَنْ دَسَّاهَا﴾.

Hakika wanda ya tsarkaketa ya rabauta* tabbas ya tabe wanda ya turbude shi.

 

Haka kur'ani yake gina sakafar tunani da aiki.. babu sakafantacce sai wanda ya tsafatace ya gyara sulukinsa da tunaninsa daga karkacewa daga munanan halaye, yayi kwadayi cikin istikama da kyawawan halaye.

 Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.

Amincin Allah ya kara tabbata ga mafi alherin halittu Muhammad da iyalansa tsarkaka

 

Tura tambaya