lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Addu’a mabudin ibada

Addu’a mabudin ibada tare da Alkalamin Sayyid Adil-Alawi

Daga cikin addu’o’in da na jarraba su da kaina cikin neman farin ciki kuma hakika na lazimce su tun lokaci mai tsawo kuma nag a alheri da farin ciki cikin rayuwata shi ne addu’ao’in da suka zo cikin littafin (Mafatihul Jinan) cikin zirin addu’ar bayan idan sallar asubahi, ya zo daga shugabana Sadik (as) fadinsa: mene ne ya hanaku karanta wannan addu’ar sau uku safe da yamma

 

 (اللهم مقلب القلوب والأبصار ثبت قلبي على دينك، ولا تزغ قلبي بعد إذ هديتني، وهب لي من لدنك رحمة إنك انت الوهاب، وأجرني من النار برحمتك، اللهم امدد لي في عمري، وأوسع عليّ في رزقي، وانشر علي رحمتك وإن كنت عندك في أم الكتاب شقياً فاجعلني سعيداً، فإنك تمحو ما تشاء وتثبت وعندك أم الكتاب)

Ya Allah ya mai jujjuya zukata da idanu ina rokon Allah ka tabbatar da zuciyata a kan addininka, kada ka karkatar da zuciyata bayan ka riga ka shiryar dani, ka bani rahama daga gareka lallai kai mai yawan kyauta ne, ka tseratar dani daga wuta da rahamarka, ya Allah ka tsawaita rayuwata, ka yalwata arzikina, ka yada rahamarka a kaina, idan wurinka na kasance cikin uwar littafi shakiyi to ka mai da ni mai arziki, lallai kai kana shafe abin da ka so ka tabbatar da abin da ka so gareka asalin littafi yake.

Ina hadaku da Allah ina hadaku da Allah kan riko da wannan addu’a da na samata suna da makullin farin ciki domin bude kofofin rana da dare, me yafi kyawu daga abinda yake boye bayan kowacce kalma daga kalmomin cikin addu’ar daga ma’anoni da mafhumai da ilimummuka, fadinka (allahumma) ma’ana ya Allah, lallai kai ka shiga hallarar ubangijin talikai kana mai munajati da shi kan akiransa kana siffanta shi da cewa shine mai jujjuya zukata da idanu mai sassauya karfi da halaye mai tafiyar da dare da rana, idan zuciya ta kasance busashshiya to ya ubangiji ka sauyata zuwa ga mafi kyawun hali ka maida ta zuciya mai taushi lafiyayya, idan cikinta akwai gaba to sanya kauna da soyayya cikinta da makamanta haka, idan zuciya ta kasance cikin halin jujjuyawa da sauyi sai nka sameta tana karkace hanya da kangarewa kafafuwa su zame, to Allah ina rokonka ya ubangiji ya abin bauta ta ka tabbatar da zuciyata kan addininka da ka yardar mini da shi wand ashine muslunci    

 (ورضيت لكم الإسلام ديناً)

Na yardarm muku da muslunci addini.

Lallai cikinsa akwai alherin duniya da lahira, da zan Imani da shi inyi aiki da shi tareda tabbatuwar kafafuwa to kada ka zamar da zuciyata ta ynada ba zata karkata ga hagu ko dam aba ma’ana ga waninka wane da wan, bayan ka rigaya ka shiryar dani madaidaicin tafarki da wilayar sarkin muminai Aliyu bn Abu dalib (as) sannan ya ubangiji lallai kai mai yawan kyauta ne kana kyautar arziki da falala da alheri ga wanda ka so ba tareda lissafi ba, kuma ba tareda cancantuwa ba, domin ita kyauta karamci da girmamawa da tareda cancantuwa ba, kadai dai ina neman hakan daga gareka domin kai mai yawan kyauta, sannan ka kubutar dani daga azabar wutarka da fushinka da rahamarka ta jin kai kebantatta da muminai cikin duniya da lahira.

Tura tambaya