lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Kada ku riki wannan kur'ani abin kauracewa

 

Cikin misalin wannan zamani da wanda yake halaka yake halaka, wanda kuma Allah ya datar da shi yake tsira musulmi yana bukatar kur'ani mai girma wanda cikinsa akwai waraka ga mutane daga dukkanin  cututtuka da kuma kariya kuma shi mafaka da rahama daga dukkanin bala'I da wahala, inda Allah madaukaki yake cewa:

: وَنُنَزِّلُ مِنَ الْقُرْآنِ مَا هُوَ شِفَاءٌ وَرَحْمَةٌ لِلْمُؤْمِنِينَ وَلَا يَزِيدُ الظَّالِمِينَ إِلَا خَسَاراً (الإسراء: 82).

Kuma muna saukarwa daga ku'ani abinda yake waraka da rahama ga muminai kuma babu abinda yake karawa azzalumai face hasara.

Hakika hadisi ya zo daga manzon Allah (s.a.w) cikin fadinsa

«فإذا التبست عليكم الفتن كقطع الليل المظلم فعليكم بالقرآن فإنه شافع مشفّع وماحل مصدّق، ومن جعله أمامه قاده إلى الجنة ومن جعله خلفه ساقه إلى النار وهو الدليل يدل على خير سبيل ..» (1).

Idan fitintinu suka rikita ku kamar misalin yankin dare mai tsananin duhu to kuyi riko da kur'ani lallai shi mai ceto mai cetarwa kuma gasgatacce ne, dukkani wanda ya sanya shi a gabansa zai jagorance shi zuwa aljanna sannan duk wanda yayi watsi da shi zai kaora shi zuwa wutashi dalili ne mai shiryarwa zuwa mafi alherin tafarki.

Muhimmancin tafsirin kur'ani da mahangar tunani da zamantakewa

Mene ne muhimmanci tafsirin kur'ani mai girma a mahangar tunani da zamantakewa?

Hakika mutum ya banbanta da sauran halittu ta fuskanin tunani, amma ta fuskar ci da sha da motsi da barci da girman jiki bai da banbanci da sauran dabbobi daga cikin halittu, amma fifitarsa to wannan ta kasantu ne sakamakon tunani da yake yi, tare da haka hakika hankalin mutum tauyayye ne sakamakon nadama yake yi a wani lokaci, zaka samu da yawan lokuta mutum yana yin nadama, saboda haka kasantuwarsa ma'abocin tauyayyen tunani yana bukatuwa zuwa ga wahayi, Allah madaukaki ya  saukar mana kur'ani wahayi daga gareshi, shine abin kwaikwayon hankulanmu wanda da shine muka fifitu.

Sannan shi kammalallen addini ya zama dole yayi kallo zuwa ga dukkanin mas'aloli, wannan shine abinda muke samu cikin kur'ani mai girma, alal misali cikin kur'ani Allah na magana zuwa ga yaran da basu balaga ba inda yake cewa:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِيَسْتَأْذِنْكُمُ الَّذِينَ مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ وَالَّذِينَ لَمْ يَبْلُغُوا الْحُلُمَ مِنْكُمْ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ مِنْ قَبْلِ صَلَاةِ الْفَجْرِ ... (النور: 58).

Yaku wadanda kukai imani wadanda hannayenku suka mallake su da yaran da basu balaga zasu nemi izininku sau uku gabanin sallar alfijir

Sannan cikin wata ayar fuskantar da maganarsa zuwa ga muminai yana mai umartarsu da yakar jagororin kafirci inda yake cewa:

فَقَاتِلُوا أَئِمَّةَ الْكُفْرِ إِنَّهُمْ لَا أَيْمَانَ لَهُمْ لَعَلَّهُمْ يَنْتَهُونَ‏ (التوبة: 12).

Ku yaki jagororin kafirci lallai su babu alkawari garesu tsammaninsu sa daina.

Maganar kur'ani na kallon daidaikun mas'aloli kai hatta juzu'ai da gamammun mas'aloli masu muhimmanci a mustawan gina al'umma musulma da kariya kan samuwarta.

Haka zalika kur'ani yana bijira zuwa ga mas'alolin tauhidi  daga ciki shine fadinsa:

تعالى: أَفَلَا يَنْظُرُونَ إِلَى الإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ* وَإِلَى السَّمَاءِ كَيْفَ رُفِعَتْ‏ (الغاشية: 17- 18).

Ashe ba zasu kalli rakumi ba yaya aka halicce shi* haka zuw aga sama yaya aka dagata.

Hakama yana bijira zuwa ga mas'alolin tabligi, inda madaukaki yake cewa:

وَكَانَ رَسُولًا نَبِيّاً* وَكَانَ يَأْمُرُ أَهْلَهُ بِالصَّلَاةِ وَالزَّكَاةِ وَكَانَ عِنْدَ رَبِّهِ مَرْضِيّاً (مريم: 54).

Kuma ya kasance manzo kuma annabi* ya kuma kasance yana umartar iyalansa da sallah da zakka ya kuma kasance yardajje wurin ubangijinsa.

Kasantuwarsa manzo kuma annabi mas'ala ce ta dayanta a kankin kans, sannan umartar iyalansa sallah da zakka mas'ala ce ta jama'a, muhimmanci tafsirin kur'ani ya boyu cikin bayaninsa da sadar da shi zuwa ga mutane, shi tafsirin kur'ani ma'anarsa shine bayaninsa.

Mukaddimomi kan fa'idantuwa daga kur'ani

Mene ne asasin da za a iya gini kansa domin smaun damar amfanuwa daga kur'ani mai girma ta hanyar tafsirinsa?

Fa'idantuwa daga kur'ani yana bukatar mukaddima ta aiki, alal akalla ya dace ga wanda zai kutsa kansa cikin wannan hanya domin neman sani yayi karatu nma tsawon shekaru goma cikin hauzar ilimi kuma ya samun kammalallen sani kan luggar kur'ani ma'ana harshen larabci ya dandake cikin sanin ka'idojinsa, hakama wajibi ya ksance yana tsinkaye kan litattafan tafsiri ya kuma zamanto yanada kewaya da riwayoyi, bawan nada wadannan matakai sai ya kai ga marhalar tafsirin kur'ani da kur'ani, alal misali Allah madaukaki yana cewa:

الْمَالُ وَالْبَنُونَ زِينَةُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ...

`ya`ya da dukiya sune adon rayuwar duniya.

Sannan a wani gurin kuma yace:

يَا بَنِي آدَمَ خُذُوا زِينَتَكُمْ عِنْدَ كُلِّ مَسْجِدٍ ... (الأعراف: 31)،

Ya ku bil Adam ku riki adonku wurin kowanne masallaci.

Ma'anar aya ta biyu sai ya zamanto shine cewa idan kunyi niyyar zuwa masallaci to ku tafi da `ya`yanku sannan ku riki kudade.

Sannan zai iya yiwuwa a fassara aya da riwaya misali cikin fadinsa mabuwayi:

فَلْيَنْظُرِ الإِنْسَانُ إِلَى طَعَامِهِ‏ (عبس: 24).

Mutum ya yi kallo zuwa abincinsa.

 فعن زيد الشحّام: «قلت للإمام أبي جعفر الباقر (ع): ما طعامه؟ قال: علمه الذي يأخذه، عمّن يأخذه.

An karbo daga Zaidu Shahham: yace na tambayi baban Jafar mene ne abincin nasa? Sai yace: iliminsa wanda yake daukowa, ma'ana ya duba daga wurin wanne mutum zai dauko ilimi.

Abinda ake nufi da abincin a nan ba abincin na zahiri ba abinci na badini ma'anawi.

Sannan wani lokaci akan iya fassara kur'ani da lugga, Allah madaukaki yana cewa:

وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا (النساء: 35)

Idan kuna jin tsoran sabawar junansu.

Sai uya zamanto anan bai amfani da Kalmar (iktilaf) ba, wannan yana daga cikin balagar kur'ani da yin bayani na hakika kan abinda yake wakana a zahiri domin ita Kalmar (inshikak) ana amfani da kan abu guda misalin fadinsa:

اقْتَرَبَتِ السَّاعَةُ وَانْشَقَّ الْقَمَرُ (القمر: 1)

Tashin kyama ya kusanto wata ya tsage.

Kaga anan wata ai abu guda daya sai ya tsag, mata da miji suna wayar gari karkashin igiyar aure matsayin abu guda daya saboda haka ne ma aure yake tsagewa ya rabe sakamakon saki, da yace sun sassaba da juna ma'ana (iktalafa) da dole mu kaddara abubuwa guda biyu ba abu guda daya ba.

Fadinsa madaukaki:

وَامْسَحُوا بِرُءُوسِكُمْ‏ (المائدة: 6)

Ku shafi ba'arin kawukanku.

Yana shiryarwa cikin shafar wani sashe daga kai da ace zai ce:

«وامسحوا رؤوسكم»

Ku shafi kawukanku.

To da ya zama wajibi shafar dukkanin kai

 Sannan za mu iya fa'idantuwa cikin tafsiri daga sha'anin saukar aya, misali fadinsa madaukaki

فلَا يُسْرِفْ فِي الْقَتْلِ‏ (الإسراء: 33)

Kada ya wuce gona da iri ciki kisa.

Da zamu dauke shi kamar yanda yake ba tare da kallon sha'anin saukar ayar ba to da zai ka ga ma'anar kisan daya ko biyu sai dai cewa an hana wuce gona da iri cikin hakan, amma idan mukai la'kari da sha'anin saukar ayar zamu samu cewa akwai wani abu ya da ya rataya da yaki tsakanin kabila biyu, saboda haka da kallon wani yanayi da hali kada a wuce gona cikin kisa saboda kowanne guda zai iya kisa amma banda ketare iyaka.

Shi hana ketare haddi yana nuni ga wani abu da yake wakana lokacin jahiliya, a wannan zamanin ma zamu iya ganin misalsalansa, lokacin da wani daga wata kabila yake kashe dan wata kabila guda daya sai su taso su yi ta zubar da jinin yan kabilarsa da basu da laifi komai basu san hawa ba basu san sauka ba.

Shiriya daga Allah madaukaki

Ta yaya zamu iya fahimtar kur'ani sannan wanne abu ne zai taimaka mana kan hakan?

Shi fahimtar kur'ani da aiki da shi shiriya ce daga Allah madaukaki, sannan ya kamata ga wanda yake san fahimtar kur'ani bayan neman taimako daga Allah matsarkaki ya nufi wajen kwararrun malamai cikin wannan fanni wadanda suka sadaukar shekaru masu yawan gaske cikin neman ilimi da ma'arifofin kur'ani.

Shi kur'ani akwai bayyanannun ayoyi cikinsa akwai kuma mutashabihai, ya zama dole ga gama garin mutane su koma zuwa ga tafsirai ingantattun wurin ma'abota ilimi.

Amma idan matasanmu suka ce zasu komawa kur'ani kai tsaye ba tareda malami ba lallai zasu karkacewa hanya.

Ba'arin wasu mutane suna da'awar cewa wannan zamani da muke ciki zamani na tafsiri maudu'i ba zamani na tafsiri tartibi ba, hakika wannan magana ba daidai ce ba, wannan ba zamani bane na tafsiri maudu'i bas hi wannan take kawai; shi tafsiri yana iya kasancewa tartibi kuma yana iya kasancewa maudu'i gwargwadon yanda zuruf ya hukunta, shi tafsiri maudu'I yana zuwa ne bayan tartibi wand ashine jigon ginin tafsirion kur'ani, bayan masana tafsiri sun kammala tartibi sai su kutsa maudu'an kur'ani mai girma.

Hikima da wa'azi mai kyawu

Wacce hanya kur'ani yake bi cikin kiran muatne zuwa ga Allah?

ادْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ وَجَادِلْهُمْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ‏ (الأنعام: 152).

Kayi kira zuwa ga tafarkin ubangijinka da hikima da kyakkyawan wa'azai kayi jayayya da su da magana da  tafi kyawu.

Wannan shine usukubin kur'ani cikin da'awa, hikima da wa'azi mai kyawu samammu ne cikin kur'ani kamar yanda jidali da magana da tafi kyawu shima akwai shi cikin kur'ani, kamar fadinsa madaukaki

وَضَرَبَ لَنَا مَثَلًا وَنَسِيَ خَلْقَهُ قَالَ مَنْ يُحْيِي الْعِظَامَ وَهِيَ رَمِيمٌ* قُلْ يُحْيِيهَا الَّذِي أَنْشَأَهَا أَوَّلَ مَرَّةٍ وَهُوَ بِكُلِّ خَلْقٍ عَلِيمٌ‏ (يس: 78- 79).

Kuma ya buga mana misali ya manta halittarsa yace wane ne yake raya kashi bayan ya rududduge* kace wanda ya halicce shi da farko shine zai raya shi kuma shi masani ga dukkanin halittu.

Wannan amsa an bada ta da magana mafi kyawu.

Kur'ani da ilimi

Ta wacce hanya zamu iya amfanuwa da kur'ani mai girma ta fuskanin ilimin dabi'a, shin za a iya kawo mana misalai da samfuri?

Shi kur'ani littafi ne da aka saukar da shi domin shiriyar da mutane, na'am yayi ishara zuwa ga ba'arin al'amura misalin fadinsa madaukaki:

 وَالتِّينِ وَالزَّيْتُونِ‏ (التين: 1)

Ina rantsuwa da baure da zaitun.

Me ya sanya ya cudanya baure da zaitun bai cudanya shi da ruman ba? Ta yiwu akwai wata fa'ida a ilimance kan yin hakan, kamar yanda baure ana ambace sau day arak cikin kur'ani amma zaitun an ambace shi har karo bakwai a wurare bakwai da lafazinsa wuri daya kuma da ishara, cikin wannan akwai wani sako na ilimi, ta yanda binciken ilimi ya guda tun shekaru da suka gabata cikin daya daga kasashen turai wand aya tabbata cewa cin kwaya guda ta baure da kwayoyi bakwai na zaitun yana da wani tasiri mai amfani a lafiyance.

هَذَا مُغْتَسَلٌ بَارِدٌ وَشَرَابٌ‏ (ص: 42)

Wannan abin wanka ne mai sanyi da kuma abin sha.

Sai muka ga Allah bai ce (abin sha mai sanyi) ba sai yace: abin wanka mai sanyita yanda cikin akwai fa'ida ga jikin mutum.

A misalin wannan zamani muna magana da juna ta hanyar sadarwar zamani telefon da wanda yake mafi nisan bigire kai har takai ga muna iya ganin hotonsa mai motsi, idan muka koma kur'ani zamu samu Allah cikin kissar Sulaiman (as) yana bamu labarin mas'alar karagar Bilskisu

قَالَ الَّذِي عِنْدَهُ عِلْمٌ مِنَ الْكِتَابِ أَنَا آتِيكَ بِهِ ... (النمل: 40).

Wanda ilimin littafin yake gareshi yace ni zan zo maka da shi…

Waccan karagar cikin wancan lokaci za a zo da shi daga kasar Yaman a kawo shi Falsdinu cikin kiftawar idaniyar, bawai a nakalto hotonsa daga can ba kadai, ta yiwu nan gaba ilimi ya bayyanar mana cewa zai kai wannan mataki ta yanda za a dinga dauko abubuwa daga wani muhalli zuwa wani muhalli cikin kiftawar ido.

Karatun kur’ani tara da sanya lura

Wacce rawa uslubin shiriyarwa yake takawa, sannan kuma mene ne yah au kanmu dangane da kur’ani mai girma?

إِنَّكَ لَا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ (القصص: 56).

Lallai kai baka shiryar da wanda ka so sai dai cewa Allah yana shiryar da wanda ya so.

وعن الإمام الرضا (ع): «إنّ الناس لو علموا محاسن كلامنا لاتّبعونا».

An karbo daga Imam Rida (as) fadinsa: hakika da mutane zasu san kyawanan zantukanmu da sun mana biyayya.

Wazifar da take kanmu cikin karanta kur’ani da lura da kuma aiki da shi da bayaninsa ga matasa.

A matsayin nasiha muna cewa: abin ban takaici a wannan zamani kur’ani ya wayi abin kauracewa daga garemu, akwai siffofi hudu na zargi cikin da sukai bayanin kan haka cikin wadannan surori kamar haka:

 (البقرة: 74 (الأعراف: 176) (الجمعة: 5) \(الأعراف: 179).

Sai dai cewa akwai mafi tsananin zargi daga wadannan ayoyi, shine fadinsa madaukaki kan ma’abota littafi

يَا أَهْلَ الْكِتَابِ لَسْتُمْ عَلَى شَيْ‏ءٍ.

Ya ku ma’abota littafi baku bakin komai.

Kamar yanda muka sani alal akalla jaki da kare da dutse dukkanin su abu ne, amma sai kur’ani ya kira su da cewa ku ba komai bane, to me yasa, har zuwa yaushe, sai Allah ya cigaba da maganarsa yace:

 حَتَّى تُقِيمُوا التَّوْرَاةَ وَالإِنْجِيلَ ... (المائدة: 68)؟

Har sai kun tsayar da attaura da linjila.

Sabaoda haka wazifar da ta hau kanmu shine mu tsayar da kur’ani don kada mu kasance kwatankwacinsu daga masu kauracewa kur’ani da barinsa ta yadda manzon Allah (s.a.w) rana kiyama zai kai kara gurin Allah yana mai cewa

وَقَالَ الرَّسُولُ يَا رَبِّ إِنَّ قَوْمِي اتَّخَذُوا هَذَا الْقُرْآنَ مَهْجُوراً (الفرقان: 30).

Kuma manzo yace ya ubangijina lallai al’ummata sun kauracewa wannan kur’ani.

Daga karshe muna cewa amincin Allah ya tabbata gareku.

 

 


Tura tambaya