lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Raya ambaton Ashura

Kasantuwar shahadar Imam Husaini (a.s) da sahabbansa ta yi tasiri gaske cikin tunanin al'ummar musulmi haka ya haifarwa da Umayyawa babbar matsalar da jawo sanya alamar tambaya cikin halascin hukumarsu da mulkin da suka dare karagarsa da zalunci, domin gudun kada wannan babbar musiba da ta faru a tarihi ta fada cikin kwandon mantuwa, Imam Zainul Abidin (a.s) ya raya wannan tarihi ta yawan kukansa kan shahidan da aka kashe, babu shakka wannan hawaye nasa mai radadi da kukansa mai cike da bakin ciki ya kasance yana da asalin na soyayya da tausayi domin girman wancan musiba ta Karbala ta kai girma da matsayin da babu wanda ya halarceta ya gani da idonsa da ya iya manta, amma babu yaya Imam Sajjad yayi mu'amala da wannan maudu'I da yake da tasirin gaske da kuma yake dauke da natija ta siyasa, raya Ashura da tunawa da ita ya hana mantawa da ta'addanci da zalunci da Daular Banu Umayya ta aikata.

Imam a duk lokacin da yaji kishurwa ya so ya sha ruwa da zarar ya kalli ruwan sai kaga hawaye yana kwarara daga idanunsa, lokacin da aka tambaye shi dalilin kwarara hawayensa, sai yace: yay aba zanyi kuka ba alhalin Sojojin Yazidu sun iya kyale dabbobin daji masu kai bara su sha ruwa amma daidai wannan lokaci sun tsohewa mahaifina duk wata hanya da zai kai ga ruwa domin ya sha sun kashe shi yana cikin matsananciyar kishirwa.

Imam yace: duk sanda na tuna da kisan da akaiwa `dan Fatima sai na fashe da kuka, Imam ya dinga bijiro da wannan maudu'I da batu a wurare daban daban.

Tura tambaya