lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Siyasar muslunci zama na Arba’in

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Idan muna so mu gane ana yin daidai kamar yanda muka ce dole ne a sanya wani alami wanda da shi za a dinga aunawa. Ba zai yiwu ba kayi kontirol din ayyuka ba tared aka sanya ma’auni ba daidai waje kaza an cimma natija daidai waje kaza da akamje an cimma natija, sannan kuma a ayyana wanne geji ne idan mutum ne yaje za agane ya kyautata ta yanda za a yaba masa a bashin allon yabo a kuma kyautata masa ama bashi kyaututtuka, sannan kuma a anya masa method hanyar da zai bi domin cimma wannan hadafi, sannan kuma a dinga kiyasta natijar da ya cimma a aikinsa wannan duk yana ciki, saboda haka auna aikin da mutum yake yi ba karamin muhimmi bane domin a gane kyautatawarsa, mua iya bada misali da manzon Allah (s.a.w) ansan yanda ake haka kabari da mikdarin fadinsa da tsayinsa amma lokacin da aka haka kabarin Ibrahim (as) `dan manzon Allah (s.a.w) sai ya zamanto wanda ya haka kabarinsa ya bubbuge wani wajen bai saita shi daidai ba sai manzon  Allah (s.a.w) da ya ga haka sai ya karbi abun haka da kansa ya saita kabarin ya shata shi daidai ba tareda wani waje ya fi wani waje tudu ba ko wani waje yayi loko ba, sannan sai ya tsaya ya yiwa mutane magana yace: idan dayanku yayi aiki ya kyautata shi.

 Wannan ya nuna muhimmanci tsari da kontirol da kyautata aiki ta yanda manzon Allah ( s.a.w) ya muhimmantar da kiyaye aiki da kyautata shi hatta kan kabari tareda cewa yana cikin jimami rashin dansa.

إذا عمل أحدكم عملاً فلتيقنه.

Idan dayanku yayi wani aiki to ya kyautata shi.

A wani wajen yana cewa;

آفات الأعمال عجز عمال.

Aibin aiki shine masu aikin su gajiya su kasa yinsa daidai yanda ya dace.

Akwai wata mas’ala da muke so mu kawo shine cewa wanda aka baiwa aiki yayi aiki tukuri kan aikin kada  a bashi aiki sai ya zama yayi aiki tukuru amma a wani aikin da bashi aka umarce shi ba, abinda aka baka shi zaka kiyaye idan baka iya ba kace baka iya ba. 

Tura tambaya