lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

SIRRIKAN ARAFAT

DA SUNAN Allah MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Dukkanin godiya da yabo sun tabbata ga Allah mai rainon talikai, tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halitta Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Allah matsarkaki madaukaki yana cewa:

(لَيْسَ عَلَيْكُمْ جُنَاحٌ أَن تَبْتَغُوا فَضْلاً مِن رَبِّكُمْ فَإِذَا أَفَضْتُمْ مِنْ عَرَفَاتٍ فَاذْكُرُوا آللهَ عِنْدَ آلْمَشْعَرِ آلْحَرَامِ وَآذْكُرُوهُ كَمَا هَدَاكُمْ وَإِن كُنْتُمْ مِن قَبْلِهِ لَمِنَ آلضَّالِّينَ * ثُمَّ أَفِيضُوا مِنْ حَيْثُ أَفَاضَ آلنَّاسُ وَآسْتَغْفِرُوا آللهَ إِنَّ آللهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ [1] .(

Allah matsarkaki da daukaka na cewa: babu laifi kanku ku nemi falala daga ubangijinku idan kuka kwararo daga Arafat ku ambaci Allah wajen masha'arul harami ku ambace shi kamar yadda ya shiryar daku duk da cewa gabaninsa kun kasance daga batattu* sannan ku kwararo ta inda mutane suka kwarara ku nemi gafarar Allah lalle Allah mai gafara ne mai jin kai.

1-daga cikin wararen ibada masu alfarma akwai Arafat wadda ita wani bigire ne mayalwaci da yake tsakanin makka da mina da nisan kilo mita 22 cikin kudu maso gabas daga makka nada nisan kilo mita 18 murabba'i kusa kusa, wuri ne da mahajjata ke tattaruwa a rana ta tara ga Zul hijja daga farawar zawalin rana ya zuwa faduwarta ana kiran wanna taro da sunan tsayuwar Arafat, lalle shi yana daga cikin rukunan hajji.

 «الحجّ عرفة ليدلّ على عظمة يوم عرفة وكأنّه هو الحجّ بتمامه ، فمن تركه متعمّداً بطل حجّه .

2-ya zo cikin ingantaccen hadisi daga Annabi (s.aw) shi hajji Arafat ne domin ya yi nuni ya zuwa ga girman ranar Arafat, duk wanda ya barshi da gangan lalle hajjinsa ya gurbata.

3-an kiraye ta da Arafat sakamSkon kasarta tafi daukaka daga waninta daga wuraren ibada daga Mina da Muzdalifa da Harami mai daraja.

4- an kiraye ta da wannan suna sakamakon fadin Jibrilu ga Adamu (as) da Ibrahim (as) da Manzon Allah (s.a.w) : ka san ayyukan ibadarka cikin hajji.

5- cikin Arafat akwai wani dutse da aka fi saninsa da dutsen rahama da dutsen Rafat a can samansa akwai wani farin sawu wanda yake ishara gameda abin da ya zo cikin riwaya da ke hakaitar da haduwar Adamu da matarsa Hauwa'u bayan saukowar su wannan duniya da rabuwar su zamani mai tsayi suna ta kuka kan kuskuren da suka aikata sai Allah ya amsa musu ya gafarta musu to shi ne suka hadu a wannan bigire mai albarka, daga haka ne aka kiran wajen da sunan Arafat, Allah ne mafi sanin daidai.

6- saharar Arafat na ishara ranar Arafat kan hadin kai da soyayya karkashin haimar Allah da kuma saharar ranar kiyama da tashin mutane da fitowarsu daga kabari zuwa ga ubangijinsu suna ta gudu suna addu'a suna kuka da shashshaka da neman fakewa da ubangiji mai girma da daukaka.

7- kasar Arafat kasa ta samun gafara, da yawa-yawan zunubai ba a gafartasu face a Arafat, kamar yadda cikin falalar watan Ramadan lalle shi watan gafara ne, duk wanda ya haramtu ya rasa gafararsa to ba za a kara gafara ta masa ba har sai shekara ta zagayo, ko kuma ya riski taron Arafat sannan mafi girman zunubi ga ahalin Arafat shi ne waninsu ya fita daga Arafat alhalin yana debe tsammani daga rahamar Allah cikin gafarta masa zunubansa, babu wata rana kamar ranar Arafat cikin kubuta daga zunubi da zabar wuta kullaliya, ubangiji na gafara ga wanda ya yi tsayuwar Arafat kai hatta ahalinsa da dukkanin wanda ya fake da shi a garinsu..

8- Arafat shi ne mahajjaci ya san cewa Allah ya kewaya da shi da ilimi, idan ka bayyana zance lalle shi Allah ya san abin da ya ke boye, saboda haka ka sani cewa Allah yana ji yana kuma gani yana kuma sani kuma shi mai iko ne kan komai.

 (وعرفت قبض الله على صحيفتک وإطلاعه على سريرتک وقلبک( [2]

  A Arafat ne Allah ya damki takardar ayyukanka ya tsinkaya kan sirrinka da zuciyarka.

9- a rafat ne shaidani yak eke kaskanta da wulakanta matukar wulakanta bisa abin da ya gani daga yalwar rahamar Allah ga wadanda sukayi hajji da umara sannan lalle kuma ita wannan rahama ba ta hada da shi ba sakamakon kasantuwarsa la'ananne har zuwa ranar kiyama.

10- a filin Arafat mutum ke kara kammaluwa cikin saninsa da iliminsa yana kuma samun kamala daga makobtakar kammalallu da suka halarci taron Arafat musammam jagioran mahajjata sahibuz zaman(aj) wanda samuwarsa ne kasa da sama suka samu tabbatuwa da samuwarsa aka azurta dukkanin mutane, wanne arziki yafi girma daga kasantuwarsa cikin bigire matsarkaki shugaban tsarakaka yana numfashi cikin wannan bigire, sallar mahajjaci da addu'arsa da ayyukansa  za su  cudanya da sallar da addu'ar sahibuz zaman(aj) sai iamam ya zamanto mai cetonsa cikin mi'irajinsa da isarsa ga kololuwar kamala daga girma da kamala.

11- Arafat tunatarwa ce ga ranar tashi daga kabari daga ranar kiyama dukkanin mutane na cikin kankan da kai da kushu'I da fakewa da Allah matsarkaki.

12- waliyyan Allah girmansa ya girmama suna halartar taron Arafat, kamar yadda yake cikin bakan sauka su waliayai sune tsanin fairer Allah da saukarta, haka ma su tsani ne na faira cikin bakan hawa da mi'iraji zuwa ga Allah matsarkaki madaukaki.

13- `yar takaitacciyar tsayuwa a Arafat tana tuna mana tsayuwarmu a duniya kaskantatta, me ya fita takaituwa it aba komai bace face kallo guda ne cikin rayuwa ta har abada.

14 arafat mahallin ne na tsumayi don shiga haramin Allah domin dawafi da ziyara  da soyayya da shauki, lalle duk wanda ke nufin shiga daki ko gida babu makawa zai tsaya bakin kofa yana mai neman izinin shiga. Shi gida ya tattaro dakuna da falonsu, shi gida an ciro shi daga Kalmar da'ira da ihada ma'ana bigiren da aka kewaye shi da katangu, shi kuma daki an ciro kalmarsa daga wurin barci kamar yadda ya zo a harshen riwaya ya tattataro falo da dakuna wanda mutum ke barci ciki.

15-  Arafat mahallin tsarkaka:

عن الامام الصادق  7: «لا يصلح الوقوف بعرفة على غير طهارة .

An karbo daga imam sadik (as) bai kamata mutum ya tsaya a rafat batare da tsarki ba.

Saboda haka mustahabbi ne yin wanka domin ranar Arafat haka ma mustahabbi ne yin alwala, ya kamata ya tsarkake zahirinsa da yin wanka da alwala, sannan ya tsarkake badininsa da hawayen tuba da nadama da istigfari, lalle mafi falalar ayyuka cikin Arafat shi ne yin addu'a.

16- Arafat mahallin w da wliayar sarkin muminai ali(as)

 (آليَوم أكمَلْتُ لَكُمْ دينَكُم ) [3] نزلت بعد أن نزل قوله

(A yau ne na kammala muku addininku) wannan aya ta saukar fadinsa madaukaki

تعالى : (يَا أَيُّهَا آلرَّسُولُ بَلِّغْ مَا أُنْزِلَ إِلَيْکَ مِن رَبِّکَ وَإِن لَمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ وَآللهُ يَعْصِمُکَ مِنَ آلنَّاسِ )[4]  التي نزلت في يوم عرفة .

 (Ya kai manzo ka isar da abin da aka saukar maka daga ubangijinka idan b aka aikata haka to baka isar da sakonsa ba lalle Allah zai baka kariya daga mutane) wacce ta sauka ranar Arafat.

A Arafat cikin kowacce shekara imami ma'asumi sahibuz zaman (aj) yana halarta.

عن الامام الصادق  7 قال : «يفقد الناس إمامهم ، يشهد الموسم فيراهم ولا يرونه »[5] .

Daga imam sadik (as) ya ce: mutane za su nemi imaminsu su rasa sai imamin ya halarci taron Arafat ya gansu amma sub a za su ganshi ba.

وعن السفير الخاص بالامام  7 محمّد بن عثمان العمري قال : والله انّ صاحب هذا الأمر ليحضر كلّ سنة يرى الناس ويعرفهم ويرونه ولا يعرفونه[6] .

Daga jakadan Imam Mahadi na musammam muhammadu ibn usmn amari ya ce: wallahi ma'abocin wannan al'amari yana halarta taron Arafat cikin kowacce shekara yana ganin mutane yana saninsu su suna ganinsa amma basu san kowaye ba.

17- Arafat mahallin addu'a da yankewa zuwa ga ubangiji, lalle addu'a na daga cikin mafi falalar ayyukan Arafat, me ya fi yawa daga addu'o'in da aka rawaito daga makarantar Ahlul baiti: kamar addu'ar Imam Sajjad (as) cikin littafin Sahifa Sajjadiya da addu'ar Imam Husaini (as) wadda take cikin Mafatihul jinan da sauransu.

18 arafat na daga cikin mafi kyawu surar hadin kan musulmi, cikin mahalli guda a zamani guda lokaci guda tareda dukkanin kungiyoyi da al'ummu da kabilu daban daban da launuka mabanbanta daga garuruwa da kasashe mabanbanta manesanta da makusanta, wannan n daga abin da ke gigita mai hankali da lura, sannan bayan tsayuwarsu a Arafat saisu kwarara zuwa mahs'arul harami  halin kasantuwarsu miliyoyi jama'a.

 


[1] Bakara:198-199

[2] Asrar wa ma'ariful hajji:198

[3] Ma'ida:3

[4] Ma'ida:67

[5] Kafi: juz 1 sh 327

[6] Alfakihu:juz 2 sh 520

Tura tambaya