lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

MASH'ARUL HARAM

1-an kiraye shi da wannan suna na Mash'arul haram a Muzdalifa sakamakon an ciro shi daga Kalmar zulfa (kusanci) ko kuma ace (taro), bawa na kusanta bayan saninsa da Allah matsarkaki ya kara fadaka da nauyin da ke kansa, ya tsinkayi yardar Allah da zuciyarsa, kamar yadda a wannan bigire yana haduwa da`yan'uwansa talakawa cikin Mash'arul haram, lalle yana kusa kusa da makka mai karamci.

() 2 ـ قال جبرئيل لابراهيم  7: إزدلف إلى المشعر الحرام فسمّيت المزدلفة.

2-Mala'ika Jibrilu ya cewa Annabi Ibrahim (as) kusanto zuwa ga Mash'arul haram to daga nan ne ake kiransa da Muzdalifa (makunsata)

3-bayan mahajjata sun kwararo daga Arafat zuwa Mash'arul haram a daren goma na Zul hijja to za su kwana a Mash'arul haram zuwa wayewar rana ta goma, sannan mustahabbi ne a wannan dare su tsinci tsakuwar da za su yi jifa da ita su tattara don hakan ya yi ishara kan cewa kai kana tanadi kana tattara makamanka domin yakar Shaidaninku cikin garjin rana.

 فاعدوا لهم ما إستطعتم من قوّة .

Kuyi tanadi gwargwadon ikonku daga dukkanin karfi.

4- mahajjaci zai tattara tsakuwa har guda 48 domin ya jefi Shaidan da su mustahabbi ne ya kara adadin zuwa guda 70, daga cikin karamomin Mash'arul haram fiye da shekaru dubu ana diban tsakuwowinsa amma duk da haka babu wata shekara da aka samu sun karanta, me yiwuwa mustahabbanci cikin kara adadin tsakuwar jifan na ishara zuwa ga yawaita tanadar makaman yakar makiya.

5-an kiran kasa mai tsarki da matattara mahada sakamakon Adamu ya hada sallar magariba da isha'i cikinta kamar yadda hakan yake sunna[1]

6- Mash'arul haram wani bigire ne mai albarka da ke da nisan kilomita 12 daga Arafat daga hanyar Makka da take tsakanin manyan duwatsu biyu, tsayuwa a mash'arul haram na daga cikin rukunan hajji, an kira ta da wannan suna na mash'arul haram sakamakon tana daga cikin ibadojin Allah ma'ana mahallin ne da ake neman yardar Allah, kamar yadda yake a bayyane cewa yana daga alamomi cikin ayyukan hajji.

7- a daren kwarara zuwa Mash’arul haram ba rufe kofofin sammai ga muminai sabaoda haka mustahabbine mai karfi raya wannan dare da ibada da addu'a da ambaton Allah matsarkaki, lalle Allah yana begen addu'a a irin wannan dare mai albarka a wannan bigire mai albarka.

8- tsayuwa a Mash'arul haram domin yaye hijabi har a yiwa mahajjaci izini da ya kawo abin hadayarsa ranar idi da hajji mafi girma.

9- a Arafat kake sanin makiyinka, zuciya mai yawan umarni da mummuna da Shaidanun mutane da aljannu, a Mash'arul haram kake daukar makami kake shiri domin yaki da jihadi da gwagwamarya, a Mina cikin kwanaki uku zaka jefi Shaidanu zaka yaki makiyan addini da akida da kyawawan dabi'u, cikin ranar nasara zaka shiga Makka mai karamci kana halin samun nasara domin yin dawafi daura da daki mai alfarma kana mai ziyara cikin soyayya da rabauta da cika da farin ciki da nasara daga Allah da datarwarsa.

10- zaka samu rahamar Allah da sauka a Mash'arul haram.

11- Mash'arul haram mahallin ambaton Allah da godiya kan shiriyarsa da datarwarsa:

 (فَاذْكُرُوا آللهَ عِنْدَ آلْمَشْعَرِ آلْحَرَامِ وَآذْكُرُوهُ كَمَا هَدَاكُمْ وَإِن كُنْتُمْ مِن قَبْلِهِ لَمِنَ آلضَّالِّين)َ[2]

Ku kirayi Allah a Mash'arul haram ku kiraye shi kamar yadda ya shiryar da ku lalle gabaninnsa kun kasance daga batattu.

12- Mash'arul haram waje ne na neman tsoran Allah da falala, lalle kowanne mutum guda ya zama wajibi ya kamata ya jiyar da zuciyarsa tsoron Allah da tsantseni daga ayyukan haramun ya nemi falala ya kauracewa munanan halaye, mafificin guzuri shi ne guzurin tsoron Allah lalle hakan abin nema ne cikin dukkanin ayyukan hajji, sai dai cewa yana tajalli a Mash'arul haram kari kan kan kari.

13- Mash'arul haram bigiren kankan da kai da kushu'i kamar yadda ya zo cikin riwaya daga Imam Sadik (as).

14- lalle daga cikin zikirin Allah a mash'arul haram shi ne ka tuna da kyawun Allah cikin sifofinsa cikin boyayyen sirrinka ka shaida hakan cikin hakikanin samuwarka ka jiyar da hakan cikin dukkanin motsinka da shu'urinka, babu wata jahiliya bayan wannan rana, bari dai sulukinka da tafiyarka zuwa ga Allah matsarkaki bisa hasken sanin Allah da ilimi da shu'uri da fahimta da hikima da shuhudi cikin malak da malukutiyya cikin fakuwa da bayyana.

15- tsayuwa cikin Mash'arul haram na nufin cewa mai iko a rayuwa shi ne ibadar Allah ba taken shugabannin duniya ba da ma'abota alfarma da dukiya da mulki, ka rayu a kasar hakika ba tare da katangar gidaje ba, ba tare da haima ba babu rufi babu kayatattun ababen kallo babu lambuna babu girman kai babu son kai, kai bari dai kai da kankin kanka zaka durkusa ka tsinci duwatsun jefa don ka jefe makiyinka a tsakar rana da dukkanin wayewa da fadaka.

16- lalle hakika cikin addu'o'i akwai sirrika da hikimomi da suka shallake tunanin mai tunani, duk wanda ya lura cikin addu'ar hajji da ayyukansa zai tsinkayi taskoki daga ilimummuka da sirrika, lalle mustahabbi ne cikin Mash'aul haram cikin adu'arka ka fadi:

 (فک رقبتي من النار)

Ka kwance wuyana daga wuta.

Ma'ana katserarta dani daga tsiyata, lalle wadannan da suka tsiyata suna cikin wuta, suna madawwama cikinta matukar dawwamar sammai da kassai, da farko ya zama dole in kubuta daga talautuwa da haramtuwa da tsiyata domin in shiga kwazazzabon azurtattu cikin aljanna wadda fadinta ya kai fadin sammai da kassai wadda aka tanade ta don masu takawa azurtattu

 (وَأَمَّا آلَّذِينَ سُعِدُوا فَفِي آلْجَنَّةِ خَالِدِينَ فِيهَا مَا دَامَتِ آلسَّمواتُ وَآلارْضُ).[3]

Amma wadanda suka azurtu suna cikin aljanna suna madawwama cikinta matukar dawwamar sammai da kassai.[1] Biharul anwar:juz  96 sh 266

[2] Bakara:198

[3] Hudu:108

Tura tambaya