lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Malamai magada Annabawa (2): takaitaccen tarihin Ayatullah Assayid

Malamai magada Annabawa (2): takaitaccen tarihin Ayatullah Assayid Muhammad Takiyu Kunsari

Wane ne Ayatullah Assayid Muhammad Takiyu Kunsari?

An haife shi a garin Kunsar a kasar Iran cikin watan Ramadan mai albarka a shekara ta 1305 hijri, ya taso cikin dangi masu daraja da aka san su da ilimi da falala da ladabi.

A shekara ta 1322 gabanin cika shekaru goma sha bakwai da haihuwa ya yi hijira zuwa birnin Najaf mafi daukaka domin karatun ilimin addini, bayan ya samu damar kammala marhalar suduhu sai ya fara halartar darasussukan Ayatullahi Shaik Kurasani da darasussukan Ayatullah Assayid Muhammad Kazim Yazdi, bayan wafatin Shaik Kurasani ya ciratu zuwa halartar darasussukan Ayatullah Shaik Shari’atu Isfahani da darasin Ayatullah Aga Diya’ud dini Iraki.

Ya rungumi karatun Akliyat wajen Shaik Ali Kujani, ya fa’idantu matuka daga darasussukan sa cikin gwagwarmayar korar yan mulkin mallakar Birtaniya, Assayid Kunsari ya kasance yana zauna a Iraki lokacin ruruwar yakin duniya na farko sai ya hadu da Ayatullah Shaik Muhammad Takiyu Shirazi wanda akafi sani da Mirza sani da Ayatullah Mustafa Kashani sukai tarayya cikin yakar mamayar yan mulkin mallaka na Birtaniya, fagagen gwagwarmayar su sun tattaro tsakanin koramar garin Dajlatu da Furatu, bayan gwabza yaki mai tsanani daga su  Assayid da bangaren yan mulkin mallakar Birtaniya makiya Assayid ya samu rauni sakamakon harbi wanda hakan ya hana shi cigaba da kwamawa da yan mulkin mallaka makiya wanda hakan ya kai gay a fada hannun makiya daga sojojin Birtaniya, bayan fitowar sa daga kurkukun Birtaniya sai ya koma mahaifar sa ta Kunsar da take a Iran, a nan ma bai huta ta yanda take ya dauki nauyin jagorantar yakar gwamnatin Shahinsha Rida Khan tareda sauran malaman addini, bugu da kari yayi tarayya cikin gwagwarmayar mallakawa dukkanin yan kasar ma’adanan danyan fetur, haka zalika yayi kira al’umma da kada su sake su yi tarayya cikin zabubbuka wanda ake kira majalisar kasa.

Za a iya takaice gudummar sa cikin abinda zai zo:

1-karfafa system din Hauza ilimiya a birnin Qum:

A cikin shekara ta 1340 hijri bisa bukatar Ayatullah Al’uzma Shaik Abdul-Karim Ha’iri wanda ya assasa Hauza a birnin Qum mai tsarki-Assayid Muhammad Takiyu Kunsari ya zo birnin Qum mai tsarki ya sanya hannun sa kan hannun Shaik Ha’iri domin karfafar rukunan Hauza ilimiya wacce gwamnatin Shahinsha koda yaushe take mata dakon sharri, bayan wafatin Shaik Ha’iri Assayid Muhammad Takiyu ya hadu da Ayatullahi Assadri wanda ya bar duniya a shekara 1373 hijri sunyi aiki domin hakkakar da haduffan Shaik Ha’iri cikin tarbiyantar da daliban addini da shiryar su domin sauke wajiban su na isar da sako da tsayar da sallah juma’a.

2- daga cikin bayyanannun hidimomin sa da ya gabata kansu akwai tsayar da sallar juma’a wacce take da kunshe da sasannin siyasa hakan ya kasance a shekara ta 1360 a makarantar Faiziyya da ke kusa da hubbaren Sayyida Ma’suma (as) sakamakon cikar masu halarta sai aka mai da sallar zuwa masallacin Imam Hassan Askari (as).

za a iya cewa Assayid Kunsari ya mike kan raya wannan ibada wacce aka kaurcewa tsahon shekaru.

3-jagorantar sallar neman ruwan sama:

Tana daga cikin hidimomin sa na zamantakewa wacce ya gabatar da ita ga al’ummar Iran, cikinta Ayatullahi Araki ya rawaito mana wannan kissa gameda sallar neman ruwan sama yana cewa: birnin Qum mai tsarki ya fuskanci fari na karancin ruwan sama mai tsanani, mutanen gari sun nemi da ya jagorance su sallar neman ruwa amma sai yaki yarda, bayan magiya mai yawa da naci daga manyan mutane sai ya amsa bukatar su, kusan mutum dubu ashirin suka fito wajen garin Qum suka yi sallar neman ruwan sama cikin jagorancin sa, bayan idar sallar da Kankanin lokaci sai ga ruwan  sama mai tarin yawa ya sauko da wani yanayi mai jan hankali albarkacin addu’ar wannan bawan Allah.

Wafatin sa:

Assayid Kunsari a kwanakin karshen rayuwar sa ya jarrabtu da rashin lafiya wacce bata dau lokaci mai tsayi ba, ya amsa kiran ubangijin sa a bakwai ga watan Zul hijja/1371, an dauko jana’izar sa tsarkakka daga Hamdan zuwa birnin Qum mai tsarki, an raka jana’izar sa da rakiya mai cike da kwarjini an kuma binne shi kusa da malamin sa Ayatullah Al’uzma Shaik Abdul-Karim Ha’iri cikin Hubbaren Sayyada (as).

An kulle Hauzozi birnin Qum da Najaf bisa nuna jaje da bakin ciki ga wannan babban rashi ga muslunci a

 

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.

Tura tambaya