Deprecated: __autoload() is deprecated, use spl_autoload_register() instead in /home/net25304/al-alawy.net/req_files/model/htmlpurifier-4.4.0/HTMLPurifier.autoload.php on line 17
Ashura gagara misali da fahimta-tare da alkalamin sayyid Adil-Alawi (dz)
lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Ashura gagara misali da fahimta-tare da alkalamin sayyid Adil-Alawi (dz)

 

Na farko : dole ne ya san mafarin aiki da inda ya nufa, lallai duk wani koma bayan Allah yana da mafari da inda zai karkare ya kare ya zo karshe, kamar wanda ya nufi yin tafiya ya zama dole ya fara daga mafarar tafiya sai kuma inda ya nufa a tafiya sai kuma karshe, mafarar ayyuka da manufarsu a wasu lokuta suna kasancewa don Allah, wani lokacin kuma sukan kasantuwa babu sunan Allah cikinsu bai zartu kansu ba, kamar mafaru da manufofi da hadafofin shaidan babu banbanci cikin kasantuwarsu daga aljanni ko bil adam ko kuma daga rai mai yawan umarni da munana ko kuma daga jahilci da ta’asubbanci ko kuma daga duhu da sharri.. bai buya ba cewa ayyuka da hidindimu suna gangarowa ne daga gabbai, sannan tabbas dukkanin wani mamu yanada limami, limamin gabbai cikin motsin da suke da rshin motsinsu shi ne mariskan zahiri guda biyar, amma mariskan zuciya da limamin zuciya shi ne hankal, sannan limamin hankali shi ne tunani, sannan limamin tunani shi ne nauyaya biyu : littafin Allah da tsatson manzon Allah (s.a.w) tsarkaka. sannan daga mutane akwai wanda limamin tunaninsa sune limaman bata da kafirci da mufunci, sai hankalinsa da zuciyarsa da mariskansa da dukkanin gabban jikinsa cikin da’irar bata da wilayar shaidani da rundunarsa da gayyarsa.

Amma wanda limaminsa ya kasance limamin shiriya, mafarar rayuwarsa da manufarta za su zamanto kur’ani da zuriyar manzon Allah (s.a.w). ya zo cikin addu’a gabanin karatun kur’ani daga maulanmu imam Sadik (as) 

 (اللّهم إنّي أشهد أنّ هذا كتابك المُنزل من عندك على رسولك محمد بن عبد الله’، وكلامك النَّاطق على لسان نبيك، جعلته هادياً منك إلى خلقك، وحبلاً متّصلاً فيما بينك وبين عبادك، اللّهم إني نشرت عهدك وكتابك، اللّهم إجعل نظري فيه عبادةً، وقراءتي فيه فكراً، وفكري فيه إعتباراً، وإجعلني ممّن أتّعظ ببيان مواعظك فيه، وأجتنب معاصيك، ولا تطبع عند قراءتي على سمعي ولا تجعل علي بصري غشاوةً، ولا تجعل قراءتي لا تدبّر فيها، بل إجعلني أتدبّر آياته وأحكامه، آخذاً بشرايع دينك، ولا تجعل نظري فيه غفلة ولا قراءتي هذراً، إنك أنت الرؤوف الرحيم)...

Ya Allah tabbas ni ina shaidawa wannan littafinka ne saukakke daga gareka ga annabinka muhammadu ibn Abdullah, zancenka ne mai furuci kan harshen annabinka wanda ka sanya shi mai shiriyarwa daga gareka zuwa ga halittunka, kuma igiya sadaddiya cikin abin da ke tsakaninka da bayinka, ya Allah lallai ni na bude alkawalinka littafinka ya Allah ka sanya kallona cikinsa ya zama ibada ka sanya karatuna cikinsa ya zama tunani, kuma ka sanya tunani na cikinsa ya zama fadakuwa, ka sanya ni cikin wadanda suke wa’aztuwa da bayaninka cikinsa, in zama ina kauracewa sabonka, ka da ka toshe kunnuwana sa’ailin karanta shi ka da ka sanya lullubi a idona, ka da ka sanya karatuna ya zama karatu ba tare da zurfafa tunani da lura ba, bari dai ka sanya in dinga lura da tunani cikin ayoyinsa da hukunce-hukuncensa ina mai riko da shari’o’in addininka, ka da ka sanya nazari na cikinsa ya zama gafala, karatuna ya zama surutu, tabbas kai mai tausayi da jin kai ne.

Na biyu: ya zama dole a san hanyoyi da tafarki tsakanin mafara da inda za’a je, lallai yadda al'amarin yake shi ne cikin rayuwa kadai dai mikakken siradi daya ne rak bai da na biyu, amma hanyoyi da tafarkai lallai su gwargwadon adadin numfashin halittu ne, sai dai cewa idan suka sadu da siradi sai su kasance daga gaskiya cikin gaskiya zuwa ga gaskiya, idan kuma suka yanke daga barinsa kamar layuka yankakku daga dama da hagu daga barin layin tsakiya mikakke wanda manzon Allah (s.a.w) ya shata shi ya zana shi a ban kasa cikin wata rana ga sahabbansa ya ce: mikakken layi shi ne siradin Allah, layuka daga dama da hagu kadai layuka ne da hanyoyin iblisi da gayyarsa da rundunarsa da kabilarsa sakamakon yankewarsu ga barin mikakken siradi. Da wannan ma’auni da mizani zaka san hanyoyin Allah da hanyoyin iblis       

﴿ وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا وَإِنَّ اللَّهَ لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ ﴾(العنكبوت: 69)،

Wadanda sukai fafutika don mu lallai zamu shiryar da su tafarkanmu tabbas Allah yana tare da masu kyautatawa.

Ya zama mu san hanya da siradi.

Na uku: ya zama dole ka san kayan aiki da tsanuka da dalilai wadanda za su kai ka su sadar da kai daga mafara zuwa manufa (inda zaka je) wani lokaci kan kafafuwa zakai tafiya wani lokacin kan rakumi wani lokaci kan ingarman dok, kamar yadda ya kasance a zamanin da shude ya wuce zamanin da can. Amma wannan zamanin da muke ciki za kayi amfani da mota ne wani lokaci kuma jirgin kasa ko na sama, haka dai tare da banbantuwar kayayyakin sadarwa bisa yanayin zamanunnuka da garuruwa.

Wannan wani tabbataccen abu ne a dabi’ance da shari’ance, kamar yadda kur’ani mai girma yake ishara zuwa gareshi cikin fadinsa madaukakin sarki

﴿أَلَمْ تَرَى كَيْفَ ضَرَبَ اللَّهُ مَثَلاً كَلِمَةً طَيِّبَةً كَشَجَرَةٍ طَيِّبَةٍ أَصْلُهَا ثَابِتٌ وَفَرْعُهَا فِي السَّمَاءِ (24)

Ashe baka ga yadda Allah ya buga misali ba kalma kyawu kamar kyakkyawar bishiya ce tushenta tabbatacce reshinta cikin sama.

 تُؤْتِي أُكُلَهَا كُلَّ حِينٍ بِإِذْنِ رَبِّهَا﴾ (إبراهيم: 24 ـ 25).

Tana bada abincinta kowanne lokaci da izinin ubangijinta.

Wannan aya mai albarka tana ishara zuwa ga hanyar sani da yanayinta, kadai dai kana tsinkayar kan sanin bishiya lokacin da ka san asalinta tushenta daga mafara da manufa inda za a tuke aje. Reshenta daga hanyoyi daga tafarkai da siradi, kayayyakin sadarwarta da kayan marmarinta sun samu ne daga tsakankanin mafara da manufa

﴿تُؤْتِي أُكُلَهَا كُلَّ حِينٍ﴾.

Tana bada abincinta kowanne lokaci.

Mai isar sakon Allah:

 wanda ya kasance a mukamin isar da sakon Allah matsarkaki

﴿ الَّذِينَ يُبَلِّغُونَ رِسَالاتِ اللَّهِ وَيَخْشَوْنَهُ وَلا يَخْشَوْنَ أَحَداً ﴾ (الأحزاب : 39)

Sune wadanda suke isar da sakon Allah suke kuma tsoransa basu jin tsoran kowa.

Yau sune malamai magada annabawa, ya zama tilas su san wane ne mai isar da sakon Allah mene ne hakikanin isar da sakon Allah sai su san mafarai da manufofi da hanyoyi da siradi da kayayyakin sadarwa da, sannan sukai ga sakamako da ake bege hakan na kasantuwa karkashin ilimi da ma’arifa, da sannu zasu san waye mai isar da sakon Allah na hakika da kuma mene ne hakikar isar da sakon wane hakki yake da shi me kuma ya hau kansa daga nauye-nauye da wajibai da taklifofin addini da na zamantakewa cikin mukamin tablig isar da sakon Allah da wa’azi da shiriyar da mutane da nusantar da su zuwa gaskiya daidai zuwa ga siradi mikakke, ga masu isar da sakon Allah masu daraja da girma cikin watannin muharram da safar daga manya-manyan malumma da masu laccoci da masu halartar laccocin da ustazai da masu kawo gyara kyalli da tarsashin haskayen ashura ta shugaban shahidai (as) lallai dawwamammen sakon imam Husaini (as) cikin yunkurinsa da juyin juya halinsa.

 (كل يوم عاشوراء وكلّ أرض كربلاء)،

Kowacce rana ashura ce kuma kowacce kasa karbala ce.

Wannan shi ne sakon Husainiyya a dunkule a takaice cikin ashura daga muharram mai alfarma, cikin waki’ar daffi mai bakantawa cikin kasar karbala a ranar goma ga watan muharram mai alfarma.

Tabbas ranar ashura mai tsanani radadi waki’a mai tsananin bakantawa shahada mai girman gaske cikin ranar ashura goma ga watan muharram mai alfarma hijirar annabi na da shekaru 61 tana daga cikin lamurra wadanda suka gagara riska da fahimta, hakika hankalin bil adama ya gaza riskar hakikaninta kamar bai iya yiwuwa ga wani mutum ya iya siffanta ta kamar yadda take a hakika.

Bai buya ba cewa daga al’amurra wadanda ake siffanta su ake riskarsu kamar shan zazzakan ruwa lallai mai sha zai ji zakinsa zai riski hakan zai siffanta shi cewa kamar zuma, daga cikinsu kuma akwai wadanda ake iya riskarsu amma kuma a gaza misalta su kamar haduwar uwa da danta bayan fakuwarsa tsawon shekaru, lallai shi cikin lokacin farko daga haduwarsu lokacin da ta rungume shi lallai wanda ya halarci wajen zai riski tsananin kaunar uwa ga danta halin kuka sai dai ba zai iya siffanta abin daya gani daga tarba da kauna tsakanin uwa da danta ga waninsa, daga cikin al’amurran kuma akwai wadanda kwata-kwata basu riskuwa basu siffantuwa da misaltuwa sune wadanda suka fice daga kewayen ikon hankali kamar misalin wahayi da dukkanin abin daya  buyarwa dabi’a daga duniyoyin malakutiyya, kamar mukamai da masaukai da martabobi ambatattu ga manzon Allah muhammadu da imaman shiriya masu shiyarwa. Lallai su suna daga karagu daga wadanda basu riskuwa da misaltuwa, hankalin bil adama ya gaza harshensa ya kasa siffanta s, kadai dai muna tsinkayuwa kan hakikaninta a yau yayewar labule rufi, Allah yana sanya ido ya zao mai ketawa karfaffa, sai mutum  ya kasance mai kaifaffar basira kamar yadda yake cikin duniyar barzahu da lahira yaga komai tangararas 

﴿لَقَدْ كُنْتَ فِي غَفْلَةٍ مِنْ هَذَا فَكَشَفْنَا عَنْكَ غِطَاءَكَ فَبَصَرُكَ الْيَوْمَ حَدِيدٌ﴾(ق: 22).

Hakika ka kasance cikin gafala daga wannan sai muka yaye maka rufi saboda haka ganinka yau mai kaifi ne.

Ka sani cewa lallai daga asraru da tabbatattun al’amuran ashura kadai dai shi ne kashi na uku, bil adama duk yadda yakai ga daga ilimi da ma’arifa lallai shi bai gushewa cikin mafarin tafiyarsa a kan hanya, lallai shi kasshshe ne kan riskar al'amarin ashurar Husaini (as) da bainda yake kunshe a bayanta daga tabbatatun abubuwa da asraru da taskoki da biyayyun abubuwa na Allah, kamar yadda bai iya yiwuwa ga wani mutum ya iya siffantata da kamantata hakikanin kamantawa da siffantawa face Allah da masu zurfin ilimi muhammadu da iyalansa (s.a.w)  dukkanin abin daake fadi daga girman al’amarin ashura  shi daga garesu yake garesu yake komawa kadai bai wuce matsayin digon ruwa daga tafkunan haskayensu da ma’arifofinsa da asraransu , lallai su ma’adanan ilimin Allah ne da maboyar sirrinsa

Me annabi mafi girma ya gani a daren da ya tafi mi’iraji:

lallai daga mafi muhimmanci da girma abubuwan da suka faru da waki’o’in da suka afku a zamanin annabi (s.a.w) cikin rayuwarsa mai albarka shi ne mi’iraji madaukaki zuwa ga ubangijinsa girmansa ya girmama, tsakanin zira’i biyu ko mafi kusa daga haka, sai ya kusanta ya kuma matsa zurowa ya ga abin daya gani wajen tukar magarya, hakika Allah ya kebance shi da mi'i'raji zuwa gareshi cikin sura mai albarka cikin littafinsa mai girma (suratul isra’i)

Hakika wannan sura ta fara da tasbihi   

﴿سُبْحَانَ الَّذِي أَسْرَى بِعَبْدِهِ لَيْلاً مِنْ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ إِلَى الْمَسْجِدِ الأَقْصَى﴾(الإسراء:1)

Tsarki ya tabbata ga wanda ya tafiyar dare da bawansa daga masallacin harami zuwa masallacin al’aksa.

Sannan zuwa ga madaukakan mashawarta.

Bai buya ba cewa shi duk inda ya ambaci tasbihi  cikin kur’ani ko kuma cikin madaukakn hadisai, lallai kamar yadda yake shiryarwa zuwa ga ban mamaki haka ma yana nuni zuwa ga abin da ya ratayu da shi daga muhimman batutuwa wadanda suka ratayu da kasantattun da shari’antattu bisa abin daya zo cikin tasbihin, a wannan lokaci ya zama tilas a maida hankali a wuaren tasbihi, lallai yadda al'amarin yake yana daga cikin abubuwan da suke wajabta tsarkaka Allah tsark ya da girma ya tabbatar masa  girmansa ya girmama. Da kuma lallai cewa babu wani abu kwatankwacinsa, daga cikin abin dake kari a tauhidinsa da saninsa Allah matsarkaki da abin da yake da dangantaka da mukamin dayantuwarsa da tilotakansa a cikin zatinsa da siffofinsa da ayyukansa, kamar yadda yake sananne a wurin ahalinsa ambatacce a mahallinsa.

tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawansa manzonsa  daga masallacin harami zuwa masallacin al’aksa, sannan zuwa madaukaki ya ga abin da abin da ya gani hakika ya ga lallai cewa an rubuta kan ala’arshin Allah da koren launi wanda shi launin ma’arifa ne  

 (الحسين مصباح الهدى وسفينة النجاة)

Husaini fitilar shiriya ne kuma jirgin tsira ne.

mene ne  abin da al’arshi ke shiryarwa zuwa gareshi cikin wannan hadisi na ala’arshi, mene ne ma’anar fitilar shiriya lallai hakan na janyo tsayuwa kan sanin iliman muslunci da ma’arifofi masu yawa, idan muka yi karin haske kan ma’anar shiriya a luggance da isdilahi, to lallai ita ta dabi’ace da tsarin halitta da shari’a , lallai ita gamammiya ce daga rahamar Allah da jin kansa kebantattace daga rahamarsa da jin kansa, lallai ita shiriya ce ta fari da kuma sakamako, duk wanda ya karbi ta farko lallai Allah zai saka masa da shiriyoyi na sakamako

 ﴿ وَزِدْنَاهُمْ هُدًى ﴾ (الكهف: 16).

Muka kara musu shiriya.

Sannan mene ne ma’anar fitila? karanta fadinsa madaukaki tare da ni

﴿اللَّهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ الْمِصْبَاحُ﴾(النور: 33)

Allah shi ne haksen sammmai da kasa misalin haskensa kamar taga ce cikinta akwai fitila ita kuma fitila…

Sannan matsarkaki yana siffantawa, yana bamu siffofinn fitilarsa, da kuma cewa lallai shi haske ne kan haske Allah yana shiryar da wanda ya so da haskensa, ba komai bane wannan kayataccen misalin na kur’ani ga sanin  Allah face sai don mutum ya kewaya da hakikanin haka, domin shi Allah shi ne masauka shi kuma mutum  shi ne mai kewaya da ilimin Allah matsarkaki da kudurarsa da rayuwarsa.

  Haskensa mai girma da daukaka kamar taga ne wani dan rami dake jikin bango budadde kan geffan bago biyu wanda ake ajiye fitila cikinsa kamar fitilar kwai domin ya haskaka geffan bango da abin dake kewaye da shi haskensa ya mamaye fuskoki biyu.

Ya zo cikin hadisin maulanmu imam Sadik (as) cikin bayanin tawilin taga a fadinsa

 (أنها أمنّا فاطمة الزهراء ‘)()، والمصباح الرسول الأعظم والزجاجة أمير المؤمنين علي×، ونور على نور إمام بعد إمام، ويهدي الله لنوره من يشاء، هو صاحب الزمان والإمام المهدي الموعود في آخر الزمان،

Lallai taga ita ce fatima zahara (as) fitila kuma shi ne manzon Allah kwalaba shi ne sarkin muminai ali (as) haske kan haske shi ne imami bayan imami, Allah na shiriyar wanda ya so da haskensa shi ne sahibuz zaman imam mahadi wanda akai alkawalin dawowarsa a karshen zamani.

A wata maganar kuma daga wata fuskar sannan babu karo da juna cikin fuskoki ko da kuwa sun sassaba, lallai cewa Kalmar fitila ta farko wadda ta zo babu alifun da lamun ishara ce zuwa ga imam hassan almujtaba (as) ta biyu kuma wadda ta da alifun da lamun ishara ce zuwa ga imam Husaini (as) shugaban shahidai wadannan batutuwa da maudu'in na al'arshi da irfani wadanda ba'a iya siffanta su ko riskarsu da fahimtarsu

Imam Husaini (as) cikin al'arshin Allah mai girma da daukaka:

Tabbas Husaini ibn Ali shugaban shahidai (as) tun ranar farkon haihuwarsa an dauke shi an kaishi zuwa ga al'arshin Allah, cikin ranar karshe daga rayuwarsa ma an kaishi al'arshin Allah kamar yadda ya zo cikin tafsiri da tawilin fadin Allah madaukaki:

 ﴿يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ (27) ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَةً مَرْضِيَّةً﴾ (الفجر: 27 ـ 28 )،

Yake wannan rai mai nutsuwa* ki koma ga ubangijinki kina halin yarda yardajjiya.

Tabbas ne wanda ya karbi ransa tsarkakka.

Wannan sura ana kiranta da surar imam Husaini (as) kamar yadda ya zo cikin haadisin shugabanmu Sadik (as) daga al'arshi zuwa al'arshi cikin ala'arshi haka ma hakika an rubuta cikin al'arshi: 

 (الحسين مصباح هدى وسفينة النجاة)،

Husaini fitilar shiriya jirgin tsira.

Wannan ma na daga abin da ba'a iya riska da siffantawa.

Daga ziyarar imam Husaini (as).

Lallai malaminmu saduk (rd) cikin littafinsa mai suna (manla yahaduruhul fakihu) wanda kansa yake cewa:

أنّي ما أذكر فيه إنما هو حجّة بيني وبين الله سبحانه،

Lallai ni dukkanin abin dazan ambata cikinsa hujja ne tsakani na da Allah matsarkaki.

Wannan littafi nasa ya zama daya daga litattafai hudub na hadisi wajen manya-manyan malamanmu wadanda malaman fikihu suke dogara da su cikin tsamon hukunci shari'a na rassa, yana ambaton ziyara guda daya ta shugaban shahidai yana cewa hakika ita ce mafi ingancin ziyarori wajena cikin wadancan ziyarori masu girma.

 (السلام عليك يا حجّة الله وإبن حجّته، السلام عليك يا قتيل الله وإبن قتيله، السلام عليك يا ثار الله وإبن ثاره، السلام عليك يا وتر الله الموتور في السموات والأرض، أشهد أنّ دمك سكن في الخُلد، وأقشعرت له أظلّة العرش، وبكى له جميع الخلائق، وبكته السموات السبع والأرضون السّبع، وما فيهن وما بينهن، ومن يتقلّب في الجنة والنّار من خلق ربّنا، وما يُرى وما لا يُرى...) ().

Amincin Allah ya tabbata gareka ya hujjar Allah diyan hujjar Allah* amincin Allah ya tabbata gareka ya wanda ya bada ransa aka kashe don Allah dan wanda don Allah, amincin Allah ya tabbata gareka ya fansar Allah dan fansar Allah ya dayantaccen Allah wanda ya dayanta cikin sammai da kasa, na shaida lallai jininka ya zauna a madawwama, inuwar ala'arshi ta yankwane saboda shi, dukkanin halittu sunyi kuka saboda zubar da shi da kayi, sammai bakwai da kassai bakwai sunyi masa kuka haka ma abin dake cikinsu da dukkanin abin dake tsakankaninsu yay i kuk, da wanda yake jujjuyawa cikin wuta da aljanna daga abin da ubangijinmu ya halitta daga abin da ake iya gani dama wanda ba a iya gani….

Bai buya ba kan cewa yankwanewa da girgizuwa tare da abin daya dace da al'arshin Allah suna daga cikin abubuwan da ba a iya riskarsu  ba kuma a iya siffanta su, amma kukan dukkanin halittu  daga wadanda ake iya gani da wadanda ba iya gani to wannan yana daga kukan tsarin halitta al'amarinsa iin al'amarin tasbihi na halitta, lallai yadda al'amarin yake shi e babu wani abu face yana tasbihi da godiyar ubangijinsa  sai dai cewa basa iya fahimtar tasbihinsa kamar yadda Allah ya bada labara cikin fadinsa matsarkaki madaukaki:

﴿ تُسَبِّحُ لَهُ السَّمَوَاتُ السَّبْعُ وَالأَرْضُ وَمَنْ فِيهِنَّ وَإِنْ مِنْ شَيْءٍ إِلاَّ يُسَبِّحُ بِحَمْدِهِ وَلَكِنْ لا تَفْقَهُونَ تَسْبِيحَهُمْ إِنَّهُ كَانَ حَلِيماً غَفُوراً ﴾(الإسراء: 44)،

Sammai bakwai nayi masa tasbihi haka ma kassai bakwai nayi masa tasbihi da dukkanin abin da yake cikinsu  babu wani abu face yana tasbihi da godewa ubangijinsa sai dai cewa bakwa fahimtar tasbihinsu tabbas shi ya kasance mai hakuri da gafara.

To haka kuka kan shugaban shahidai (as) cikin duniyar halitta. BAllahntana abin daya zo cikin shari'o'in sama da abin da annabawa amincin Allah ya tabbata garesu suka aikata daga kuka kan shugaban shahidai kamar yadda ya zo cikin hadisai ingantattu, haka ya zo cikin shari'ar muslunci cikin hadisan manzon Allah mafi girma da tsatsonsa tsarkaka daga kwadaitarwa mai girma kan kuka kan musibar da ta faru a karbala da bainda ya faru kan shugaban shahidai da ahlin gidansa daga shahada da dauri.

Shin kana ganin zai yiwu ga wani bil adama ya riska ya siffanta abin daya gangaro ya kwararo daga hadisi daga mu'amala da kaziyyar ashura da abin daya faru a filin karbala? ina samsam ina, lallai wannan al'amari yana daga al'amarin da ba a iya riskarsa ko siffanta shi!!..

Kukan da halittu kewa shugaban shahidai (as) yana daga kukan halitta a kan hakikarsa ta yiwu wanda ya kasance yanada kunnen gaibu na barzahu zai iya jin abin dake nuni zuwa hakan, lallai cewa shi zai dinga yi masa kuka dare da rana maimakon ma kukan hawaye zai yi kukan jini ne, kamar yadda ya zo cikin ziyarar nahiya daga maulana sahibuz zaman (as):

 (لأندبنك صباحاً ومساءً ولأبيكينك بدل الدموع دماً).

Zan dinga kurajin kiranka safe da yamma lallai zanyi maka kukan jini maimakon kukan hawaye.

Kadai dai wanda ya tafi da jinin Husaini tsarkakakke zuwa al'arshin Allah ya ajiye shi a madawwama da aljannoni, shi ne kakansa Mustafa Muhammad (s.a.w) kamar yadda ya zo cikin jumlar hadisai daga shi'a da sunna.

Ya zo cikin mustadrak alal sahihaini  na hakim naisaburi da isnadinsa ya ce:

حدثني أبو بكر محمد بن أحمد بن بالويه، حدثنا بشر بن موسى الأسدي، حدثنا الحسن بن موسى الأشيب، حدثنا حماد بن سلمة، عن عمار بن عمار، عن إبن عباس (رضي الله عنه) قال: رأيت النبي’ فيما يرى النائم نصف النهار أشعت أغبر معه قارورة فيها دم.

Abubakar muhammadu ibn balawaihi ya bani labari, bashar ibn musa al'asadi ya bani labari, hassanu ibn musa ashibu ya bani labari, hammad ibn salma ya bani labari, daga ammar ibn ammar daga ibn abbas (rd) ya ce: na ga annabi cikin abin damai mafarki yake gani cikin rabin rana annabi ya yi fatsi-fatsi ya yi kura tare da shi akwai wata kwalaba cikinta akwai jini

فقلت: يا نبي الله ما هذا؟ قال: هذا دم الحسين وأصحابه لم أزل التقطه منذ اليوم.

Sai nace: ya annabin Allah mene ne wannan? Sai ya ce: wannan jinin Husaini da sahabbansa ban gushe ba ina tsintarsa tun daga wannan rana.

قال: (فأحصى ذلك اليوم فوجدوه قتل قبل ذلك اليوم) ثم هذا حديث صحيح على شرط مسلم ولم يخرجاه.

Ya ce: sai na kirga wannan rana sai suka same shi an kashe shi gabanin wannan rana. Sannan wannan hadisi ya inganta kan sharadin buhari da muslim sai dai cewa basu fitar da shi ba.

Maganarsa ta kare.

Makamancin wannan shi ne abin da ya gangaro daga cikin musnad ahmad ibn hambal wanda lafazinsa ya kasance kamar haka:

 حدثنا عبد الله، حدثني أبي، حدثنا عبد الرحمن، حدثنا حماد بن سلمة، عن عمار بن أبي عمار، عن إبن عباس، قال: رأيت النبي’ وسلم في المنام بنصف النهار أشعث أغبر معه قارورة فيها دم يلقتطه أو يتتبع فيها شيئاً، قال: قلت: يا رسول الله، ما هذا ؟ قال: دم الحسين وأصحابه لم أزل أتتبعه منذ اليوم.

قال عمّار: فحفظنا ذلك اليوم فوجدنا قُتل ذلك اليوم.

Abdullah ya zantar damu, babana ya zantar dani, abdur rahman ya zantar dani hammad ibn salmatu ya zantar dani daga ammar ibn abi ammar daga ibn abbas ya ce: na ga manzon Allah (s.a.w) cikin mafarki cikin rabin ya yi kura ya futu-futu tare da shi akwai wata kwalaba cikinta akwai jini da yake tsintarsa ko kuma cikinta  abu na binta, ya ce: sai nace:  ya manzon Allah mene ne wannan? Sai ya ce: jinin Husaini ne da sahabbansa tun daga wannan rana ban gushe ba ina bibiyarsa ammar ya ce sai muka kiyaye wannan rana sai muka samu an kashe Husaini a wannan rana, maganarsa ta kare.

Kwatankwacin wannan shi ne abin da ya gangaro daga cikin littafi biharul anwar daga ummul salamatu uwar muminai maza da muminai mata Allah ya kara mata yardarsa.

daga biharul anwar daga majalisil mufid da amali dusi Allah ya tsarkake ruhinsu, da isnadinsu daga maulana Sadik Jafar ibn Muhammad (as) ya ce:

قال: أصبحت يوماً أم سلمة رضي الله عنها تبكي، فقيل مِمَّ بكاؤك، فقالت: لقد قُتل الحسين الليلة، وذلك أنني ما رأيت رسول الله’ منذ مضى إلّا الليلة، فرأيته شاحباً كئيباً، فقالت: قلت: مالي أراك يا رسول الله شاحباً كئيباً؟ قال: ما زالت الليلة أحفر القبور للحسين واصحابه عليه وعليهم السلام().

Ummul sAllahma Allah ya kara mata yardarsa a wata rana ta wayi gari tana ta rusa kuka, sai aka ce mata me yasa ki yin kuka, sai tace: hakika an kashe Husaini a wannan dare, hakan ya faru ne ni banyi mafarkin manzon Allah tun da Allah ya karbi ransa sai a wannan dare, sai na ganshi  cikin halin damuwa da bakin cik, sain nace: yaya nake ganinka ya manzon Allah cikin damuwa da bakin ciki? Sai ya ce: dare bai gushe ba ina hakawa Husaini da sahabbansa (as) kaburbura.

Ya zo cikin sanannen hadisi daga bangarori biyu shi'a da sunna cewa manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda ya ganni cikin mafarki tabbas ni ya gani, lallai shaidani bai zuwa da surata, sai ka lura

وفي حديث مشهور عند الفريقين السنة والشيعة أنه قال’: من رأني في المنام فقد رآني، فإنّ الشيطان لا يتمثل بي، فتدبّر.

Burin zuwa ziyarar shugaban shahidai (as)

Daga cikin batutuwa wadanda ba a iya riska ba a iya siffanta su, shi ne abin da makusanta ke buri da fata daga ziyartar shugaban shahidai (as) babu wani mala'ika makusanci babu wani manzo da aka aiko face yana buri yana fatan ziyartar imam Husaini (as) cikin karbala yana neman izinin Allah kan haka, mala'ika makusanci kamar misalin Jibrilu da Israfilu da Mika'ilu da Azra'ilu, manzo aikakke misalin annabawa ma'abota girma misalin Nuhu Ibrahim Musa Isa (as).

Misalin Ibrahim badadin Allah wanda Allah ya siffanta shi cikin fadinsa madaukaki:

﴿ وَإِذْ ابْتَلَى إِبْرَاهِيمَ رَبُّهُ بِكَلِمَاتٍ﴾(البقرة: 124)

Lokacin da ubangiji ya jarrabci Ibarahim da wasu kalmomi.

Ya zabe shi, wannan Ibrahim badadin Allah kenan wannan shi ne irin matsayinsa da girmansa amma daga cikin burinsa shi ne ya ziyarci imam Husaini (as) mene ne karkashin kubbarsa madaukakiya daga girma da girmama da kyawu da kamala da har misalin ire-iren wadannan makusanta daga mala'iku da manzanni da annabawa suke daku da fatan halartar karkashin wannan kubba Husainiyyya madaukakiya wacce ake amsa addu'o'i karkashinta

Biharul-anwar mujalladi na 98 sh 59, kamilul ziyarat: sh 111.

بسنده عن إسحاق بن عمّار، قال: سمعت أبا عبد الله× يقول: ليس نبي في السموات والأرض، إلّا وييسألون الله تبارك وتعالى أن يؤذن لهم في زيارة الحسين× ففوج ينزل وفوج يعرج.

Da isnadinsa daga Is'hak ibn ammar ya ce: naji abu Abdullah (as) yana cewa babu wani annabi cikin sammai da kasa face suna rokon Allah matsarkaki madaukaki da ya basu izinin ziyartar kabarin Husaini (as) ayarin na sauka ayari na hawa.

Ya zo cikin wani hadisi daban:

: ليس من ملك في السموات إلّا وهم يسألون الله جلّ وعلا، أن يأذن لهم في زيارة قبر الحسين ففوج ينزل وفوج يعرج.

Babu wani daga cikin mala'iku cikin sammai da kasa face suna rokon Allah mai girma da daukaka da ya basu izinin ziyartar kabarin Husaini,wasu ayari na sauka daidai lokacin da wasu ayarin ke hawa. Shi Husaini (as) fitilar shiriya ne ga mala'iku da annabawa da wasiyyai da muminai maza da muminai mata lallai shiharshen Allah ne idon Allah ne hannunsa cikin bude kofofi.

Musa wanda Allah ke magana da shi (as) yana barci a kabarin Husaini (as):

Ya zama dole mu dandake mu tankade da rairaya da warwara cikin sanin misalin wadannan hadisai ingantattu. Lallai misalin Abu Hamza sumali wanda ya kasance daga kebantattu sahabban imam zainul abidin (as) ya kuma kasance da sikoki amintattu masu giman matsayi wanda shi ne ma'abocin sananniyar addu'ar lokacin sahur daga imam zainul abidin (as) lallai shi yana ziyartar imam Husaini (as) tare da wahala da tsoro sojojin banu umayya a daren juma'a a boye tare da tsoron azzalumai sai dai cewa mai gadin bakin kofa ya hana shi shiga duk yadda yakai ga tambayar dalilin hana shi shiga? Sai a bashi amsa da wannan dare dare ne na maziyarcin imam Husaini Musa kalimullahi (as) wannan al'amari na sanya hanakali mutum ya gaza ya rude daga riska da siffanta wannan al'amari, misali Musa kalimullahi wanda Allah ya siffanta shi

﴿وَنَادَيْنَاهُ مِنْ جَانِبِ الطُّورِ الأَيْمَنِ وَقَرَّبْنَاهُ نَجِيّاً ﴾ (مريم: 52). ﴿ وَكَلَّمَ اللَّهُ مُوسَى تَكْلِيماً ﴾ (النساء: 164)

Kuma muka kira shi daga gefan dutsen na dama kuma muka kusanto da shi yana abokin ganawa.

Allah ya zanta da Musa zantawa.

Musa ya na barci a kabari shugaban shahidai dare juma'a (as) yana neman kusanci zuwa gareshi.

Cikin biharul-anwar daga ikbalul a'amal: an rawaito daga Abu Abdullah ibn hammad al'ansaricikin wani littafin asalinsa cikin fasalin ziyarar Husaini amincin Allah ya kara tabbata gareshi sai ya fadi abin dalafazinsa shi ne:

عن الحسين بن حمزة الثمالي قال: خرجت في آخر زمن بني أميّة وأنا أريد قبر الحسين×، فانتهيت إلى الغاضريّة، حتى إذا نام النّاس إغتسلت، ثم أقبلت أريد القبر حتى إذا كنت على باب الحسين، خرج رجل جميل الوجه، طيّب الريح، شديد بياض الثياب، فقال: إنصرف، فإنك لا تصل، فانصرفت إلى شاطئ الفرات فإغتسلتُ به، حتى إذا كان نصف الليل، اغتسلت ثم أقبلت أُريد القبر، فلمّا إنتهيت إلى باب الحائر خرج إليّ الرجل بعينه فقال: يا هذا انصرف فإنك لا تصل، فأنصرفت فلمّا كان آخر الليل إغتسلت ثم أقبلت أريد القبر، فلّما إنتهيت إلى باب الحائر خرج إليّ ذلك الرجل، فقال: يا هذا إنك لا تصل، فقلت: فلِمَ لا أصل إلى إبن رسول الله’ وسيد شباب أهل الجنة، وقد خرجت أمشي من الكوفة وهي ليلة الجمعة، وأخاف أن أصبح ههنا، وتقتلني مسلّحة بني أميّة.

daga Husaini ibn Hamza sumali ya ce: na fito karshen mulkin sarakunan banu umayya alhalin ni ina nufin zuwa kabarin Husaini (as) sai na karkare zuwa gadiriyya ya yinda mutane sukai barci sai nayi wanka sannan na fuskanto ina mai jufar kabarin Husaini har lokacin da na tuke bakin kofar kabarin Husaini (as) sai wani mutum mai kyawun fuska ya fito mai daddadan kamshi mai tsananin farin kaya, sai ya ce: juya lallai kai ba zakayi sAllah ba, sai na juya na tafi gefen kogin furatu nayi wanka da ruwan kogin har lokacin da dare ya raba sai na tashi nayi wanka na nufo kabarin Husaini, ya yinda na karkare bakin kofar kabarin sai wannan mutumin na dazu ya kara fitowa ya ce juya ka tafi lallai kai ba zakayi sAllah ba, sai na kara juyawa na tafi ya yinda karshen dare ya yi sai na tashi nayi wanka na nufo kabarin ya yinda na karkare bakin kofar kabarin sai dai wannan mutumin ya kara fitowa ya ce ya kai wannan mutum juya ka tafi lallai kai ba zaka sallah ba, sai nace masa mene ne ya sanya ba zan sadar bag a dan manzon Allah shugaban samarin gidan aljannaalhalin na fito ina tafiya da kafafuwana tun daga kufa a daren juma'a ina halin tsoran kasantuwa a nan don soojin banu umayya su kashe ni.

فقال: إنصرف فإنّك لا تصل، فقلت: ولِمَ لا أصل؟ فقال: إن موسى بن عمران إستأذن ربّه في زيارة قبر الحسين× فأذن له، فأتاه وهو في سبعين ألف ملك، فانصرف فإذا عرجوا إلى السّماء فتعال، فانصرفت وجئت إلى شاطئ الفرات، حتى إذا طلع الفجر، اغتسلت وجئت فدخلت، فلم أر عنده أحداً، فصلّيت عنده الفجر، وخرجت إلى الكوفة

Sai ya ce: juya ka tafi bafa zakayi sallah ba, sai nace to mene ne ya sanya? Sai ya ce: lallai musa ibn Imrana ya nemi izinin ubangijinsa cikin ziyarar kabarin Husaini (as) sai ya bashi izini sai ya zo masa tare da shi akwai mala'iku dubu saba'in saboda haka ka juya ka tafi idan suka hau suka koma sai ka zo, sai na juya na tafi gefan kogin furatu har ya yinda alfijir ya keto sai na tashi nayi wanka naje na shiga sai naga banga kowa ba cikin kabarin sai nayi sallah a kabarin na fito na nufi kufa.  

Mafi kusa da wannan hadisi shi ne wani hadisin daban:

ويسأل أبو حمزة عن البّواب في تلك الليلة: (فقلت: فمن أنت عافاك الله؟ قال: أنا من الملائكة الذين أُمروا بحرس قبر الحسين× والإستغفار لزّواره، فانصرفت وقد كاد يطير عقلي لما سمعت منه().

Abu hamza yana tambayar mai gadin kofa cikin wannan dare: sai nace: wanene kai Allah ya yi maka afuwa? Sai ya ce: ni daga mala'iku wadanda aka umarce su da gadin kabarn Husaini (as) da nemawa maziyartansa gafara, sai na juya na tafi hankali ya kusa gigita daga bainda naji daga gareshi.

Ina cewa abin da Abu hamza Allah ya kara masa yardarsa ya rawaito bai buya ba imam dai kwayar idanu ko kuma da kashafin ubangiji, lallai yana daga gaibu wanda mai tak`wa ke imani da shi.

﴿ ذَلِكَ الْكِتَابُ لا رَيْبَ فِيهِ هُدًى لِلْمُتَّقِينَ (2) الَّذِينَ يُؤْمِنُونَ بِالْغَيْبِ ﴾ (البقرة: 2)

Wancan littafin babu kokwanto cikinsa shiriya ne ga masu tak`wa*wadanda suke imani da gaibu.

Ba wadanda suka kasance munafukai ba cikin zukatansu akwai ciwo ko raunin imani ko kuma masu karancin ilimi da ma'arifa lallai su zasu yi inkarin wannan su nesanta afkuwarsa, ta yiwu su dangantaka gullanci kan masu imani da irin wannan al'amari, kamar wahabiyawan zamaninmu daga wadanda Allah ya makantar da zukatansu sai suka kasance suna inkarin wannan al'amari a kanmu suka zama suna kidaya shi daga gullanci alhalin su basa fuskanta,kamar yadda basa fahimtar tasbihin halittu, lallai babu wani abu face yana tasbihi da godiyar mahaliccinsa, wannan yana daga cikin batutuwa na al'arshi, daga cikin mas'alolin da ba a iya riskarsu ba kuma a iya siffanta su, ku fadaka yak u ma'abota hankula.

Daga cikin madaukakan hadisai wadanda ba a iya fahimtatsru da siffanta su shi ne hadisin da ya zo cikin littafin biharul anwar da littafin kamilul ziyarat da wasunsu daga litattafan hadisi:

 بسند معتبر عن صفوان الجمال، قال: قال لي أبو عبد الله الإمام الصادق× لمّا أتىنا الحِيرَة: هل لك في قبر الحسين؟ قلت: وتزوره جعلت فداك؟ قال: وكيف لا أزوره والله يزوه في كلّ ليلة جمعة، يهبط مع الملائكة إليه والأنبياء والأوصياء، ومحمد أفضل الأنبياء ونحن أفضل الأوصياء.

Da isnadi ingantacce daga sufwanu jammal ya ce: Abu Abdullah Sadik (as) ya ce mini lokacin da firgici ya zo mana: shin zaka je kabarin Husaini? sai nace: raina fansarka ka ziyarce shi? Sai ya ce: ta yaya bazan ziyarce shi ba, Allah yana ziyartarsa cikin kowanne daren juma'a tare da shi akwai mala'iku da annabawa da wasiyyai da muhammadu shi ne mafificin cikin annabawa mune mafifitan wasiyyai.

فقال صفوان: جعلت فداك فنزوره في كل جمعة حتى ندرك زيارة الرّب؟ قال: نعم يا صفوان: إلزم تكتب لك زيارة قبر الحسين وذلك تفضيل ().

Sai sufwanu ya ce: raina fansarka zamau dinga ziyartarsa cikin dukkanin daren juma'a har mu samu damar risker ziyartar ubangijinmu? Ya ce na'am ya sufwanu : ka lazimta za a rubuta maka ziyarar kabarin Husaini da wannan fifiko da falala.

Ina cewa a bayyane yake cewa wannan hadisi madaukaki yana daga cikin abin dabil adama ke gaza riskar hakikarsa, da abin da ya zo cikin daga tabbatattun abubuwa da ma'arifofin Allah, tabbas Allah ba jiki bane ba ma'abocinsa bane kwata-kwata, wannan shi ne abin daya tabbatu da dalilai na hankali da nakal, lallai shi babu wani abu kwatankwacinsa, saboda haka ziyararsa ga waliyinsa cikin kowannen daren juma'a wanda ya sadukar da ransa don shi fansarsa kinaya ce kan saukar a rahamarsa da jinkansa kebantacce ga muminai maza da muminai mata daga maziyartan imam Husaini amincin Allah ya kara tabbata gareshi da mahaifansa da yayansa tsarkaka, sannan saukar Allah kabarin Husaini tare da mala'iku yana daga babin majazi kamar yadda akwai dalilan hankali kan haka da na mukamin wurin kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

﴿وَجَاءَ رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفّاً صَفّاً﴾ (الفجر: 22)،

Kuma ubangijinka ya zo tare da mala'iku sahu-sahu.

Kadai dai abin daake nufi daga (tare da) bashi ne (tare da) wacce ke hade da zamani ko bigire ba kadai tana daga tsayuwa da ilimi kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

 ﴿ وَهُوَ مَعَكُمْ أَيْنَ مَا كُنْتُمْ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِيرٌ ﴾(الحديد: 4)،

Shi yana tare da ku duk inda kuka kasance kuma Allah yan a sane da abin dakuke aikatawa.

Lallai Allah yana tare da masu tsoransa hakika ya kewaya da komai da ilimnsa da kudurarsa. Lallai shi masani mai iko rayayye ai tsayuwa  

 Allah ya tare da mala'iku wadanda suke saukowa don ziyarar shugaban shahidai (as) yana kewaye da su da iliminsa su suna daga mala'iku makusanta cikin daren juma'a kamar madaukakan mahsawarta suke saukowa tare da su rayukan annabawa da wasiyyai daga adamu har zuwa cikamakin annabawa (s.a.w) kamar yadda a kebance cikamakin annabawa shugaban manzanni mafi falala da fifiko annabawa baki dayansu ke halarta tare da su muhammadu (s.a.w) kamar yadda yake saukowa tare da wasiyyansa da halifofinsa da gaskiya Ali (as) tare da yayansa ma'asumai a'immar shiriya  shiryayyu.

Ba a nufin Kalmar (tare da) wacce keda dunkule da zamani ko bigire kamar yadda wahabiyawa Allah ya tozarta su ke kkarin bata sunanmu, da har za a ce Allah yana da jiki ya jikkantu, domin shi zamani da bigire suna daga abubuwan da suka lazimtuwa da abubuwa masu jik, lallai hakan korarre ne ba zai taba sabuwa ba kan Allah matsarkaki, duk wani abu da zahirinsa ke nuni zuwa wannan to dole ai masa tawaili domin a dace da abin daya tabbatu da hankali da nakali wanda sabaninsa ne, sai a lura.

Amma sufwanu lallai shi yana daga sukatu yardaddu ya nufi zuwa ziayarasa don ya samu ziyartar ubangijinsa da wannan ziyara, ma'ana ya riski rahamarsa kebantatta fa fairarsa mafi girma a tsarkaka, da kallon jinkansa wadda ke jawo kamala da cika kammaluwa ya kusanto tsakanin zira'I biyu ko mafi kusa daga haka daga madaukaki mafi daukaka, kamar yadda ya zo cikin adu'o'I da ziyarori ingantattu

 (وانظر إليّ نظرة رحيمية، استكمل بها الكرامة عندك).

Ka kalle ne kallon jinkaida zan cika kammaluwa da ita da karama a wajenka.

Imam ya yi ishara da haka da cewa za a rubuta masa ziyarar kabarin shugaban shahiadai Husaini (as) kamar yadda za a rubuta masa ziyartar ubangiji girmansa ya girmama haka daga falala tabbatatta mai cigaba ya zuwa ranar kiyama ranar fifiko

﴿ يَرْفَعْ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ ﴾(المجادلة: 11).

Allah yana daukaka darajar wadanda sukai imani da wadanda aka basu ilimi.

Ina cewa: tsarki ya tabbata ga Allah me yafi girmama daga wanda ake ziyarta, me yafi griman mukaminsa madaukaki da matsayinsa ma'abocin daukaka cikin duniyar halitta da duniyar shari'a, idan ya zamanto mai ziyartarsa a duniya yana da misalin wannan mukami mai girma kai kace da wannan ziyarar tasa ga imam Husaini yana ziyartar Allah a saman al'arshinsa, me kake tsammani daga wanda ake ziyarta (as) kuma?

Cikin wani ingantaccen hadisin

عن زيد الشحام عن أبي عبد الله× قال: من زار قبر الحسين بن علي÷ يوم عاشوراء عارفاً بحقّه، كان كمن زار الله في عرشه ().

Daga zaidul shahhama daga Abu Abdullah (as) ya ce: duk wanda ya ziyarci kabarin Husaini ibn Ali (as) tare da sanin hakkinsa to ya kasance kamar wanda ya ziyarci Allah cikin al'arshinsa .

Cikin wani hadisin daban 

ومن زاره يوم عاشوراء، فكأنما زار الله فوق عرشه.

Duk wanda ya yi ziyara ranar ashura kamar wanda ya ziyarci Allah ne a saman al'arshinsa .

A wani hadisin

عن مولانا الرضامن زار قبر الحسين× بشط فرات كان كمن زار الله فوق عرشه().

Daga maulana imam rida (as) cikin dukkanin ziyara da kebantattu ya ce: duk wanda ya ziyarci kabari Husaini gefan kogin furatu kamar ya ziyarci Allah ne a saman al'arshinsa.

Fadakarwa mai muhimmancin gaske: 

Ba buya babu kokwanto cewa lallai misalin wannan maganganu a misalin wadannan mukamai na al'arshi da irafani kadai dai su kinaya ne  da kuma amfani na majazi ba hakika ba, sakamakon imaninmu da kore jiki ga Allah matsarkaki da kore ganinshi da idanu duniya da lahira, domin shi furuci ga jikkantuwa na lazimta kafirci da kore Allah, domin shi jiki yana bukatuwa cikin samuwarsa ya zuwa rakkabuwa bangarorinsa duk abin daya zama murakkabi mabukaci zai kasance amuwarsa ba ta zama dole ba ta dogara ne daga waninsa. Sai dai cewa wanda shi samuwarsa cikin zatinsa a zatinsa ya koru da wannan siffa ya tsarkaka, duk wanda ya tafi kan jikkanta Allah ya kasance daga kafirai wanda suka kafircewa Allah, ana sanya cikin hukuncin najasa, kamar yadda yake cikin fikihun malamanmu na imamiya Allah ya karfafe su cikin hujjojinsu da karfinsu da yaduwar mazhabarsu da tabbatattun abubuwansu. Allah matsarkaki madaukaki babu tarkibi cikinsa, daya ne a bai da na biyu, bai a kwatankwaci bai da kishiya, babu wani abu irinsa, saboda ziyararsa saman al'arshinsa  na daga amfani na majazi da kinaya ba hakika ba, hakika manya-manyan malamanmu Allah ya saka musu da alheri sun ambatarwa hakan fusaku cikin bayani kan hakan.

Daya daga ciki shi ne kinaya daga kusanci bawa zuwa ga ubangijinsa kaikace shi yana bautarsa cikin hallararsa, yana ganinsa da zuciyarsa da basirarsa da hakikar imani kamar yadda sarkin muminai Ali (as) ya fadi:

 (لا تراه الأبصار ولكن تراه القلوب بحقائق الإيمان)

Idanu basu ganin Allah sai dai cewa zukatu na ganinsa da tabbatattun imani.

Yana jin ganawa da shi cikin sirarsa da zatin hankalinsa, lallai ita zuciyar mumini al'arshin Allah ce da haraminsa..kamar yadda ya zo daga maulana imam Sadik (as)

وإنّ الله عز وجل يناجيهم في سريرتهم، ويكلّمهم في ذات عقولهم ـ كما ورد عن أمير المؤمنين علي×.

Lallai Allah mai giram da daukaka yana ganawa dasu cikin sirrikansu yana magana da su cikin zatin hankulansu kamar yadda ya zo daga sarkin muminai Ali (as)

Na biyu: lallai ziyarar baa saman al'arshin Allah kanaya ce kan haduwarsa da annabawan Allah da manzanninsa, da ganawa da wasiyyai da a'imman shiriya tsarkaka, lallai ziyarar waliyyai tana daga ziyartar Allah, lallai su fuskar Allah ne wanda mutane ke fuskantowa zuwa gareta, lallai sune sunaye Allah kyawawa cikin sunaye na aiki banda na zati (ilimi da kudura da rayuwa) kamar yadda hakan ya zo daga garesu cikin hadisai ingantattu

 (نحن أسماء الله الحسنى)

Mune kyawawan sunayen Allah.

Bai buy aba lallai cewa siffofi na aiki kamar azurtarwa halitta, wadanda muke tabbatarwa Allah su ko kuma wadanda muke kore ga barinsa mai girma da daukaka bisa la'akari da abin dake rataya da ita, lallai shi yana azurta zaidu da zuwa hajji bai azurta amru ba. Takasance daga abubuwan da suke iya yiwuwa, babu kokwanto lallai cewa mafi girman tajalli ga wadanannan abubuwa masu iya yiwuwa cikin duniyar umarni da halitta, sune wadanda Allah ya fara da su da kuma su zai rufe sune muhammadu da iyalansa (as) haskayen Allah masu tajalli cikin halitunsa

 (وكمنتم أنواراً بعرش الله محدقين، فمن الله علينا بكم إذ جعلكم في بيوت أن أذن الله أن ترفع ويذكر فيها اسمه) ()

Kun kasance haskaye cikin al’arshin Allah kuna dawafi daura da shi, sai Allah ya yi mana kyauta da ku ya yinda ya sanya ku cikin gidaje da Allah ya yi izini a daga a ambaci sunansa cikinsu.

Lallai sune sunayen Allah kyawawa da wannan ma’ana, ziyartar Allah da wannan ma’amna na nufin ziyartarsu, ziyartarsu na nufin ziyartar Allah girmansa ya girmama, kamar wadanda sukaiwa manzon Allah Muhammad (s.a.w) mubaya’a karkashin bishiya kadai dai sunyiwa Allah matsarkaki mubaya’a ne, haka ma baka jefa lokacin da daka jefa sai dai cewa Allah ne ya jefa, sai a lura.

Na uku: ta hanyar ziyartar Husaini (as) mai ziyara ke samun matsayi madaukaki  daga kusanci na badini na ruhi daga ubangijinsa, zai zama kamar misalign wanda ya daukaka ya hau zuwa al’arshi, kamar wanda ya dare karagar sarki daga sarakunan duniya ya ziyarce shi, kamar yadda wannan ma’ana ta zo kan wanda yake ambaton Allah matsarkaki lallai cikin hadisi kudusi:

قال عز وجل:  (أنا جليس من ذكرني).

Ubangiji mai girma da daukaka ya ce:: lallai ni abokin zaman wanda ya tuna dani ne.

قال الإمام الصادق×: من أتى الحسين عارفاً بحقه كتبه الله في أعلا عليين().

Imam Sadik (as) ya ce: duk wanda yaje wajen Husaini yana mai sanin hakkinsa Allah zai rubuta shi cikin mafi daukakar masu daukaka.

Na hudu: ya zo cikin kasa’isu Husainiya na malam shaik Jafar tusturi (rd) cikin bayanin abin damai ziyarar Husaini yake samu daga siffofi cikin ziyararsa, cikin babi na hudu yana Ambato ladan kebantacce mai ban mamaki da siffa ta musammam. cikin shafi 297 yana cewa: amma kebantacciyar siffa da mai ziyara ke kebanta da ita tana samuwa da abin dahadisai suka hukunta, ya kamata mu Ambato su a kebance ita ce:

أن من زار الحسين فقد زار الله في عرشه،

Duk wanda ya ziyarci Husaini hakika ya ziyarci Allah a cikin al’arshinsa.

Wanda hakan kinaya ce zuwa kurewar samun kusanci zuwa ga Allah da daukaka ya zuwa ga darajar kamala, abin daya shAllahke wannan siffa shi ne wata siffar daban, shi ne lallai ta hanyarta zai riski ziyartar Allah gareshi, hakika ya zo cewa Allah na ziyartar Husaini a dukkanin daren juma’a, duk wanda ya ziyarci Husaini daren juma’a zai riski ziyarar Allah gareshi da kuma ziyararsa ga ubangiji, sai dai cewa ita ziyarar ubangiji kinaya ce kan kwarar fairarsa daga rahama kansa a wannan lokaci, duk wanda ya riski wannan ziyara ba zai yiwu ya zama ya haramtu daga wannan rahama ba, bai hankaltuwa ace bai samu nasibi ko daya daga gareta, sannan ziyartarsa ga ubangiji kinaya ce kan kurewar kusanci zuwa ga ubangiji, idan biyun suka hadu sai ya samu martabar tattaro rahamar Allah gareshi.

A cikin wata riwayar, lallai cewa duk wand aya nufi ganin Allah ranar kiyama to ya yawaita ziyartar Husaini (as) kamar yadda ya zo cikin ( littafin kamilul ziyarat:149, da biharul anwar m 98 sh 76) wadannan jumloli uku da ziyarar Allah ziyara tare da Allah bayani ne kan tukewar kurewar abin damutum zai yi tunani daga daukaka zuwa darajojin kusanci, saboda haka aka sanyawa wannan siffa babi mai ci gashin kansa, lallai ita tana kishinyantar dukkanin batutuwa tana kuma daukaka kansu. Cikin shafi na 17 yana cewa: lallai ziyartar Allah madaukaki  kinaya ce zuwa ga makurar kusanci zuwa gareshi, wannan bai kasance ga imanin ajiya da zuciyar da Allah ya san zata iya zamaewa da karkacewa bayan shiriya. Acikin shafi na 105: kashi na biyar: cikin abin daya bashi daga mafi daukakar ababen halitta  ina nufin al’arshi wannan kyauta tanada yanayiyyika: na farko cikin hususiyya shi ne kyautar al’arshi gareshi, sai muce: lallai shi hakika ya yi kyautar inuwa daga al’arshi gareshi , sai ya sanya masa wani majalisi da zai zauna cikinsa ranar kiyama tare da shi maziyartansa da masu kuka kan musibar da same shi, sai ya aiko musu da matayensu daga aljannasai suki su fifita zaman majalisinsa da zance tare da shi. Biharul-anwar m 45 sh 207: hakika Allah ya bashi daman al’arshi ya sanya masa matsuguni cikin barzahunsa, lallai shi daga daman al’arshi kowanne lokaci yana hango mafadarsa da abin daya afku da cikinsa, yana hango maziyartansa da masu yi masa kuka, yana nema musu gafara yana tattaunawa da su yan rokon kakansa da babansa da su nema musu gafara. Amali dusi: m 1 sh 45. Biharul anwar m 44 sh 281.

Hakika Allah a saman al’arshi ya bashi mahallin tattaunawa tare da maziyartansa wane hadisi ne hakika ya zo cikin kason ziyararsa cewa zai kasance daga masu tattaunawa da Allah  saman al’ashinsa, biharul anwar m 98 sh 73. Kamlilul ziyarat sh 141.

Al’arshi majalisin tattaunawar maziyartansa ne inuwarsa kuma ga wanda zai magana da shi, samansa ga wanda yake magana da Allah, hakika Allah ya bashi inuwowin al’arshi wacce take kwansarewa saboda zubar jininsa tayi kuka kansa.

Hakika ya bashi misalign al’arshi daga sinfofin mala’iku masu gadin kabarinsa masu dawafi a kabarinsa, biharul anwar m 43 sh 275, kitbauk irshad mufid:249.

Na biyu yanayi mafi daukaka daga haka mafi isarwa shi da muce: lallai shi ya bshi al’arshi kai kace dukkaninta gareshi tasa ce, saboda idan ya kasance tare da dan’uwansa ado ne gareshi kowanne abu na tashe da adonsa ne, da al’arshi zai magantu da ya ce lallai ni daga Husaini nake. Maganarsa ta kare an dage mukaminsa.

Kamar yadda kakansa Mustafa Muhammad (s.a.w) ya ce

كما قال جدّه المصطفى محمد’: (وأنا من حسين).

Ni daga Husaini nake) farinciki ga wanda ya kasance daga Husaini cikin hanyar Husaini cikin Husaini tare da Husaini duniya da lahira.

Jigo cikin ziyarori da wasunta shi ne ta kasance daga ma’arifa cikakka (kana mai sanin hakkinsa) sannan ita ma’arifa bas hi ne ilimi ko fahimta ba, banbanci nawa ne tsakanin masani da mai fahimta wanda shi ne ma’aboicin hikima da kuma banbanci tsakaninsu da arifi.

Sannan ita ma'arifa a mafhumance da misdaki   tana daga mafuhimin kulli mushakka, kamar misalin haske na zahiri da yake da martabobi, ina zaka hada hasken kyandir da hasken rana cikin haskakarsa da bayyanarsa tare da cewa dukkaninsu sunansu haske, lallai yadda al'amarin yake duk da cewa shi ne duk da kasantuwar dukkanin biyun hasken rana da hasken kyandir sunan haske yana gasgatuwa kansuda kasantuwar shi mabayyanin kansa da waninsa, sai dai cewa wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa?!

Duk  sa'ailin da mutum ya karu cikin ma'arifa da irfani sai ya karu cikin haske da kusanci, lallai shi ta hanyar ma'arifarsa da yankewarsa zuwa ga ubangijinsa yana keta hijabai wadanda sun haura dubbai kai sun kai dubu saba'in a duniyar malakutiyya cikin ayyukan Allah, dubu casa'in cikin duniyar jabarutiyya cikin siffofin Allah, amma cikin duniyar lahutiyya cikin zatin Allah to wannan babu wanda ya san adadinsu sai Allah matsarkaki, sai idanuwan zukata su kekketa hijabai har su tuke ga ma'adanin girman Allah (Muhammad manzon Allah s.a.w) zuciyarsa ta zamanto ratayayya da daukakar tsarkin Allah girmansa ya girmama, kamar yadda ya zo cikin munajatin sha'abaniyya na imamanmu tsarkaka (as)

 (إلهي هب كمال الإنقطاع إليك، وأنر أبصار قلوبنا بنظرها إليك، حتى تخرق أبصار القلوب حُجب النّور، فتصل إلى معدن العظمة، فتصير أرواحنا معلقة بعزّ قدسك وجلال مجدك...) ().

Ya Allah ka bani kamalar yankewa zuwa gareka* ka haskaka zukatanmu da kallonta zuwa gareka* har idanuwan zukata su kekketa hijaban haske, su isa zuwa ga ma'adanan girma, rayukanmu su zamanto ratayayyu da daukakar tsarkinka da girmamar girmanka.

Ranar ashura misali ce madaukaki ga Kalmar Allah madaukakiya:

Idan muka so tsayawa da tsinkayar kan wani abu ko da kuwa kankani ne daga girman ranar ashura gwargwadon karfin bil adama, daga masdarorin ma'arifa da tsayuwa kan tabbatattun abubuwa shi ne abin daya gangaro daga hudubobi shugaban shahidai da addu'ao'insa da kalmominsa, musammam ma cikin hanyar karbala daga garin madina, lallai shi ya yi huduba a kan hanyarsa ya zo cikin hudubarsa mai haskaka:

 (من كان فينا باذلاً مهجته، موطّناً على لقاء الله نفسه، فليرحل معنا، فإني راحل مصبحاً إن شاء الله تعالى).

Dukkanin wanda ya kasance cikinmu ya shirya bada ransa, ya tsugunar da ransa kan saduwa da Allah, to ya taho tare da mu, lallai ni mai tafiya ne mai wayar gari inhsa'Allah ta'ala.

Cikin misalin wannan rana ta ashura yake rokon ubangijinsa :

 (بحق يس والقرآن الكريم، وبحق طه والقرآن العظيم، يا من يقدر على حوائج الناس، يا من يعلم ما في الضمير، يا منّفساً عن المكروبين، يا مُفرجاً عن المغمومين، يا راحم الشيخ الكبير، ويا رازق الطفل الصغير)...

Don matsayin yasin da kur'ani mai girma, don matsayin daha da kur'ani mai girma, yaw nada yake da iko kan biyan bukatun mutane, ya wanda yake da sani kan abin dake cikin zukata, ya mai yaye bala'in wadanda suke cikin bala'I, ya mai tafiyar damuwar masu damuwa, ya mai tausayin tsoho tukuf, ya mai azurta yaro karami.

Wannan shi ne Husaini ibn Ali (as) hakika ya tsaya ranar ashura da yunkurinsa da saurarsa wacce ba a iya fahimtarta ba a iya siffanta ta.

Sha'a'irul Husainiyya suna daga mafi girman ibadar kusanci zuwa ga Allah matsarkaki:

Yaku masoya muminai maza da mata, yak u shi'ar Muhammad da iyalan gidansa, ya ma'abota bukukuwan jaje da ta'aziyya da maukibobi, ku sani cewa lallai dukkanin abin dakuke aikatawa muke aikatawa cikin raya bukukuwan ta'aziyya da jaje da bakin ciki daga sha'a'air Husainiyya halastattu wadandu suna daga ibadojin Allah matsarkaki, da kuka kan musaibar da ta sami iyalan manzon Allah (s.aw) lallai suna daga mafi girman kusanci da lada, babu ma'ana fadin lallai abin damutane ke aikatawa cikin ta'aziyya da zaman makokin Husaini daga dukan kirazu da dukan jiki da sarkkoki a bayyane da abin daya yi kama da haka wai kadai hakan yana daga gullanci da wuce iyaka. Ko kuma wai yana cikin karo da wayewar wannan lokaci da cigaban da ya samu, na'am kadai yana cin karo da wayewar yammacin turai wacce tana daga jabun wayewa fadaddiya a dabi'ance, sai dai cewa tana tare da wayewarmu ta muslunci ta Allah, lallai ita tana daga kololuwar wayewa da cigaba da ma'arifa, dukkanin abin damuke aikatawa cikin raya zaman makokin Husaini kadai shi yana ma daga takaitawa da yin kasa a gwiwa, inba haka b, ace wanda tsarkakakken jininsa dawwamamme ya zuba, wanda inuwowin ala'arshi ke kwansarewa saboda musibar da ta same shi, dukkanin halittu ke masa kuka daga halittun da kae iya gani da wadanda ba a iya ganinsu, lallai dukan jiki da sarkoki har jikin ya yi bakin kirin jini ya zuba ba a kidaya yin hakan a wuce gona da iri, bari dai mu bamu gushe ba muna takaitawa cikin da'irar takaitawa da kasa agwiwa kan batun shugaban shahidai (as) da mu'amala rayayya da ita da girmama shahadarsa a ranar ashura kan abin da ya faru cikin kasar karbala madaukakiya, hatta idan muka bada ranmu mai daraja don jajen Husaini (as) don ziyararsa musammam ziyarar arba'in da miliyoyin mutane suke halarta a wannan zamani da muke ciki, lallai hakan bai bakin komai, lallai kadai dai shi kamar misalin digon ruwan ne cikin tafki idan aka kwatanta shi da abin dashugaban shahidai (as) ya sadaukarwa ubangijinsa.

تركت الخلق طّراً في هواكا

وأيتمت العيال لكي أراكا

فلو قطعتني في الحبّ إربا

لما حنّ الفؤاد إلى سواكا

Nayi ban kwana da dukkanin halittu don soyayyyar da nake maka. Na maraitar da iyalina don shaukin ganinka* da zasu yi gunduwa-gunduwa dani cikin soyayyarka da har abada zuciyata ba zata karkata zuwa ga waninka ba.

Husaini (as) adon al'arshin Allah:

Haka ne bawai ala'arshin Allah yana kawatuwa da Husaini (as) a kansa ana rubutu da koren launi:

 (الحسين مصباح الهدى وسفينة النجاة)

Husaini shi ne fitilar shiriya jirgin tsira.

Kadai ba bari dai dukkanin halittu duk wani abu wanda yake wanin Allah matsarkaki yana kawatuwa da Husaini (as) hatta manzon Allah (s.a.w) farkon halittar Allah mai girma da daukaka rahama ga talikai, da shi aka fara da shi za a rufe lallai shima yana kawatuwa da Husaini (as) cikin fadinsa Husaini daga gareni yake nima daga Husaini nake, waye Husaini ne me ya sanarda kai Husaini (as) hasken Allah mafi haskaka sirrinka mafi girma. Sunansa mai girma, lallai shi ranar kiyama kowacce rai zata kuraji tace wayyo kaina kai hatta annabwa da waliyyai face manzon Allah muhammadu Mustafa (s.a.w) zai yi shela ya ce ya al'ummata cikin wannan rana mai tsanani Fatima zahara (as) zata tsayar da zaman makokin danta shugaban shahidai imam Husaini (as) cikin tsakiyar taron lahira, lallai ita za ta dora rigar Husaini rigar tana jike da jininsa tsarkakakke a kanta ta nemi mafi iya hukuncin masu hukunci ya nemar mata hakkin danta Husaini (as) sai wani sautin magana ya zo daga tushen girmama da umarnin daga rigar Husaini (as) kuma a baiwa zahara damar neman abin datake so  a wannan lokaci sai ta nemi ceton zuriyar ta da shi'arta da masoyanta da masoyan masoyanta.

Wannan fa duk kan rigar Husaini kenan fa me kake zato kan Husaini alhalin shi ne fa fitilar shiriya kuma jirgin tsira.

Sannan daga riwayoyin al'arshi da suka ratayu da shugaban shahidai (as) lallai shi ne ya kasance idan ya kasance ranar haihuwarsa cikin ala'arshi ranar wafatinsa cikin ala'rshi, an kuma rubuta shi kan al'arshi, to lallai bayan shahadarsa har zuwa ranar kiyama yana hango mafadarsa da wanda ya sauka cikinta yana hango rundunarsa yana hango maziyartansa, shi ne mafi saninsu da sunayensu a sunayen iyayensu da darajojinsu da masaukansu wajen Allah, lallai shi yana kallon mai masa kuka sai ya nema masa gafara, ya roki iyayensa da su nemawa mai masa kuka gafara, yana cewa:

أيّها الباكي لو تعلم ما أعد الله لك، لكان فرحك أكثر من جزعك.

Ya kai mai kuka da kasan abin daAllah ya yi maka tanadi da farin cikinka yafi rakinka yawa.

 A wani hadisin

 (وإنّه يستغفر له من كل ذنب وخطيئة).

Lallai shi yana neman masa gafara daga dukkanin zunubi da kuskure.

Farin cikin ga wanda ya san imam Husaini (as) hakikanin sani ya ziyarce shi ya yi kuka kansa, ya tsayar da makoki da ta'aziyya, ya kasance cikin hidimarsa zuciya da jiki ruhi da gagar jiki ya sadauar da rai da dukiya cikin tafarkinsa, lallai shi zai rabauta da farincikin duniya da lahira, wannan shi ne farinciki mai girma karshen maganarsu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.

 

Tura tambaya