lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasul karijul fikhi shekara 1442- Ruku’u

Fikhu (1) 23 ga watan Muharram shekara 1442

Fasalin Ruku’u:

Wajibi ne yin ruku’u sau daya a cikin kowacce raka’a cikin sallolin farilla da na nafiloli, face cikin sallar bayyanar ayoyin ubangiji, iata cikin sallar aya a kowacce raka’a a yin ruku’u biyar kamar yanda bayani zai zo a nan gaba shi ruku’u rukuni ne salla n abaci idan a ka barshi da gangan ko kuma cikin mantuwa da rafkana, haka tan abaci idan a kayi kari cikinsa cikin sallar farilla face sallar jam’i ita cikinta Karin baya cutarwa tareda niyyar bibiya, sannan wajiban da ya kunsa wasu al’amura ne:

Ina cewa: bayanin mukaddima da sharer fage zuwa ga sallah da jumlar daga wajibanta da kuma bayanin hukunce-hukuncen kabbarar harama da tsayuwa da kira’a karatun sallah zamu tsunduma bayani kan ruku’u da bayanin hukunce-hukuncenta hakan zai kasance cikin mukamai:

Na farko: bayaninta cikin hukumul taklifi (hukunci na taklifi) da bayanin muhallinsa, lallai wajibi ne cikin kowacce raka'a da sallar farilla da nafila a zo da ruku'u guda daya, lallai ita ruku’u wajibi ce cikin kowacce raka’a face abinda ya fita da dalili kamar misalin cikin sallar bayyanar ayoyin ubangiji daga kisfewar rana da wata kamar yanda bayani zai zo nan gaba, sannan dalilin wajabcin ruku’u: da farko dai yana daga larura daga addini kamar yanda ya zo cikin littafin Aljawahir kuma kamar yanda jiga-jigan Malamai sukayi ikirari da ita.

Na biyu: dalilin da ya zo daga littafin Allah mabayanni:   

﴿وَارْكَعُوا مَعَ الرَّاكِعِينَ﴾

Kuyi ruku’u tareda masu ruku’u

Na uku: abind aya zo daga sunnar Annabi tsarkakka da hadisan Ahlil-baiti (a.s) mutawatirai da suke fa’idantar da yakini, daga cikinsu akwai abinda Manyan Shehu Muhammadawa uku: cikin Alkafi Alfakihu da Almuhazzab:

1 ـ الوسائل عن الكافي في حسنة علي بن إبراهيم أو مصّححته: محمد بن يعقوب عن علي بن إبراهيم عن أبيه عن إبن أبي عمير عن حمّاد وعن الحلبي، عن أبي عبد الله عليه السلام قال: الصلاة ثلاثة أثلاث: ثلث طهور، ثلث ركوع، وثلث سجود([i]).

Daga littafin Alwasa’il daga Kafi cikin Hasanatu Aliyu IBN Ibrahim da ingantattun riwayoyinsa: daga Muhammad Ibn Yakub daga Aliyu Ibn Ibrahim daga babansadaga Abu Umairu daga Hammad daga Halabi, daga Abu Abdullahi (a.s) yace: sallah sulusai uku ce: sulusin dahara, sulusin ruku’u, sulusin sujjad.

2 ـ وعن محمد بن إسماعيل عن الفضل بن شاذان عن حمّاد بن عيسى عن ربعي بن عبد الله عن محمد بن مسلم عن أحدهما عليه السلام قال: إنّ الله فرض الرّكوع والسجود.

Daga Muhammad Ibn Isma’il daga Fadalu Ibn Shazan daga Hammad Ibn Isa daga Raba’i Ibn Abdullahi daga Muhammad Ibn Muslim daga dayansu (a.s) yace: hakika Allah ya farlanta ruku’u da sujjada, wannan hadisi Shaik ya rawaito shi da isnadinsa haka ma wanda ya gabace shi.

3 ـ محمد بن الحسن بإسناده عن الحسين بن سعيد عن النضر عن عبد الله بن سنان عن أبي عبد الله عليه السلام قال: إنّ الله فرض من الصلاة الركوع والسجود. الحديث.

Daga Muhammad Ibn Hassan da isnadinsa daga Husaini Ibn Sa’idu daga Nadaru daga Abdullahi Ibn Sinan daga Abu Abdullah amincin Allah ya tabbata a gareshi yace: Allah ya farlanta ruku’u da sujjada a cikin sallah.

5 ـ وبإسناده عن محمد بن أحمد بن يحيى عن محمد بن عيسى عن يوسف بن عقيل عن محمد بن قيس عن أبي جعفر عليه السلام في حديث: أنّ أمير المؤمنين عليه السلام كان يقول: إنّ أوّل صلاة أحدكم الرّكوع.

Da isnadinsa daga muhammmad Ibn Ahmad Ibn Yahaya daga Muhammad Ibn Isa daga Yusuf Ibn Akilu daga Muhammad Ibn Kaisu daga Abu Jafar (a.s) cikin wani hadisi: lallai Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi ya kasance yana cewa: hakika farkon sallar dayanku shine ruku’u.

 سماعة قال: سألته عن الركوع والسجود هل نزل في القرآن؟ قال: نعم قول الله عز وجل: ﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا ارْكَعُوا وَاسْجُدُوا﴾،

Hakika bayani kan hadisin Samma’atu ya gabata yace: na tambaye shi dangane da ruku’u da sujjada shin aya ta sauka cikin kur’ani? Yace: na’am cikin fadin Allah Azza wa Jalla: yaku wadanda kuka yi Imani kuyi ruku’u da kuyi sujjada. Da waninta daga hadisai masu daraja cikin wannan babi kamar yanda ya zo a cikin littafin Hada’ik juz 8 sh 234-235.

Na biyu: adadinsa shine ruku’u guda daya cikin kowacce raka’a daga sallar farilla da nafila face abinda ya fita da dalili kamar misalin sallar kisfewar rana lallai itab ruku biyar biyar cikin kowacce raka’a, yana shiryarwa zuwa ga haka dalilai kamar haka:

1-sallama da ijma’in dukkanin musulmai sunna da shi’a.

2- sakamakon samuwar nutsuwa sauke taklifin shari’a cikin fadinsa ta’ala: (yaku wadanda sukayi Imani) lallai yana samuwa da tabbatuwa karo daya.

3-jumlar riwayoyi masu daraja kamar yanda ya zo cikin Wasa’ilul shi’a babi 24 daga babukan ruku’u babin ya kunshi riwayoyi hudu:

1 ـ محمد بن علي بن الحسين بإسناده عن الفضل بن شاذان عن الرضا عليه السلام قال في كيفية صلاة يجب في كلّ ركعة ركوع واحد وسجدتان إلّا الكسوف.

Daga Muhammad Ibn Aliyu Ibn Husaini da isnadinsa daga Fadalu Ibn Shazan  daga Imam Rida (a.s) yana bayani cikin kaifiyya sallah yace wajibi ne cikin kowacce raka’a a yi ruku’u guda daya da sujjada guda biyu face cikin sallar kisfewar rana ko wata.

4-kadai an kirayi raka’a da sunan raka’a sakamakon la’akari da ruku’un da yake cikinta kamar yanda manyan Malamai guda biyu Assayid Hakim cikin Mustamsakihi juz 6 sh 292 da Assayid Kuyi cikin Attakrirat juz 15 sh 1 a wannan zamani suka yi ishara zuwa gareshi, kadai ruku’u a tabbatuwa cikin yinta guda daya a kowacce raka’a, a lura.

Na uku: lallai ita ruku’u tana daga rukunan sallah, abinda ake nufi da rukuni a isdilahin fikhu shine cewa sallah tan abaci idan ya baci da kari cikin sani ko cikin mantuwa face abinda ya fita da dalili, kamar cikin sallar jam’i, lallai cikin sallar bay abaci cikin surar da mai bin lima ya dago daga ruku’u gabanin dagowar Limami, bayani kan wannan gaba zai zo nan gaba da yardarm Allah.

Bai kamata wani yayi ishkali kan kasancewar ruku’u daga rukuni kamar yanda wadannan dalilai da zasu a kasa suke shiryarwa kansa:

1-sallamawa da ijma’i Almuhassal da Mankuli.

2- yana daga abinda hakikar sallah ta tsayu kansa, lallai ita sallah na amsa sunanta ne cikin yinta tareda ruku’unta da sujjadarta.

3- gayyar adadin riwayoyi ingantattu cikin wannan babi.

Cikin Alwasa’il babi 10 daga babukan ruku’u cikin babin gurbatar sallah cikin barin ruku’unta da gangan ko cikin rafkana har yayi sujjada, da kuma wajabcin maimaitawa da sakaewa cikin wannan babi akwai riwayoyi guda biyar, daga cikinsu akwai:

3 ـ عن محمد بن الحسن عن صفوان عن أبي بصير عن أبي عبد الله عليه السلام قال: إذا أيقن الرّجل أنه ترك ركعة من الصلاة وقد سجد سجدتين وترك الركوع إستأنف الصلاة، وعنه عن صفوان عن منصور عن أبي بصير مثله([ii]).

Daga Muhammad Ibn Hassan daga Safwanu daga Abu Basir daga Abu Abdullah (a.s) yace: idan mutum ya samu yakini kan cewa bai yi ruku’u ba halin kuma ya riga yayi sujjada guda biyu ya bar ruku’u a baya dole ya sake sallah, misalin wannan hadisi ya zo daga gareshi daga Safwanu daga Mansur daga Abu Basir.

4ـ وبإسناده عن زرارة من أبي جعفر عليه السلام أنه قال: لا تعاد الصلاة إلّا من خمسة الطهور والوقت والقبلة والركوع والسجود. الحديث محمد بن علي بن الحسين بإسناده عن زرارة مثله.

Da isnadinsa daga Zuraratu daga Abu Jafar (a.s) yace: ba a sake sallah sai sakamakon afkuwar abubuwa guda biyar: rashin ingancin dahara, lokaci, Alkibla, ruku'u, Sujjada. Misalin wannan riwaya shine hadisin Muhammad Ibn Aliyu Ibn Husaini da isnadinsa.

Alhurru Amili yana Allah ya tsarkake sirrinsa yana cewa: ina cewa: hakika abinda yake shiryarwa kansa ya gabata, da sannu abinda zahirinsa ke cin karo da ita zai zo nan gaba, da kuma cewa shi andora shi kan nafila.

Haka zalika babi 14 babin gurbatar sallah cikin kara ruku’u ko da kuwa hakin rafkana ne da kuma rashin bacinta da Karin sujjada daya a bisa mantuwa, babin ya kunshi riwayoyi guda uku.

Zamu cigaba.


Tura tambaya