lisdin makaloli sababun makaloli makaloli Mukalolin da akaranta dayawa.

Bahasi kan rayuwar Imam Sajjad amincin Allah ya tabbata gareshi

Bahasi kan rayuwar Imam Sajjad amincin Allah ya tabbata gareshi Cikin bahasinsa kan rayuwar Imam Sajjad (as) Assayidul Ka'id yayi Karin bayani kan cewa gamammen minhajin wannan Imam (as) yana taimakawa cikin fahimtar kebantattun abubuwa masu yawan gaske cikin rayuwarsa, faraway daga wannan mafara ta hanyar bijiro da gamammiyar karkatar A'imma (as) bisa la'akari da cewa dukkaninsu sun kasance suna yin aiki tukuru suna kai komo zuwa ga cimma hadafi guda daya wanda shine kafa hukumar muslunci ta adalci. Cikin wannan bahasi za a dora kan bahasin da ya gabata a halkar da ta gabata.

Gamammiyar fuska ga rayuwar Imam Sajjad (as)

Imam Sajjad (as) ya yi gogayayya da faruwar waki'ar Ashura d ata kasance gaban idonsa a shekara ta 61 da kuma shahadantar da shi da kai da guba a shekara 91 da hijira, ya cigaba ya dora kan hadafin samar da hukumar Ahlil-baiti (as), saboda haka ya kamata da farko muyi bayanin juzu'iyat din aikin Imam da marhalolin da gifta ta kansu da usluban da yayi amfani da su hakama da dukkanin kalmomin da ya bayyana kai da dukkanin motsinsa da addu'o'insa da munajatotin da suka so cikin Sahifa Sajjadiya da sauransu…. Dukkanin wannan tareda kallon kaddul am (gamammen mataki). Haka zalika matakan da ya dauka tsawon rayuwarsa.

Imamanci:

1-matsayarsa kan Ubaidullahi bn Zayad da Yazidu wacce ta fifita da jarumta da sadaukarwa.

2-matsayarsa wacce ta ffifta da nutsuwa kan Masraf bn Ukbatu, wannan mutumin da mike tsaye kan ganin ya rusa Madina da halasta dukiyoyin mutanenta karkashin umarnin Yazidu cikin shekara ta uku na mulkinsa.

3-motsin Imam kan kishiyantar Abdul-Malik bn Marwan wanda ya kasance mafi karfin halifofin Banu Umayya mafi makircinsu ta yanda matsayarsa kansa a fifita da tsanani a wani lokaci a wani lokacin kuma tsakatsaki.

4-matsayar Imam (as) kan Umar bn Abdul-Azizi.

5-mu'amalar Imam tareda sahabbansa da mabiyansa da wasiyyarsa ga abokansa.

6-matsayar Imam kan malaman fada da masu taimakon azzalumai.

Dukkanin wadannan matsayu da motsi ya kamata a karance da dikka, a iya tunani na ina ganin cewa tareda lura da gamammiyar hanyarsa lallai dukkanin wadannan juzu'iyyat da abubuwa suna da datattun ma'anaoni bayyanannu, da sannu zaka fahimci cewa wannan babban mutum ya karar da baki dayan rayuwarsa cikin fafutika da kai koma cikin tabbatar da tsarkakakken hadafi wanda shine kafa hukumar Allah a ban kasa da tabbatar da muslunci, hakika yayi amfani da mafi falala da dacewar hanyoyi, ya cigaba da jan ragamar ayarin muslunci da suka kasance bayan waki'ar Ashura, ya zartar da aikinsa da nauyi da mas'uliyarsa ta asali wacce nan gaba zamu iya ishara kanta filla-filla, wacce dukkanin A'imma da annabawa da salihai suka mike kanta. Imam kasance yana kiyaye siyasa da jarumta da yin dikka cikin ayyuka, bayan shekara 35 daga jihadinsa da bai samu hutun cikinsa ba Imam ya bar duniya cikin karamci da daukaka hakika ya dauki nauyin wannan sako mai girma domin ya mika shi ga imamin da zai zo bayansa Imam Bakir (as).

Hakika ciratar imamanci zuwa ga Imam Bakir (as) tareda mas'uliyar kafa hukumar Allah a ban kasa na bayyana karara cikin riwayoyi, cikin wata riwaya mun samu Imam Sajjad (as) yana tattara `ya`yansa yana mai musu ishara zuwa ga Muhammad bn Ali Albakir (as) yana mai cewa:    

«احمل هذا الصندوق وخذ هذا السلاح وهذه الأمانة بيدك».

Dauki wannan akwatu karbi wannan makami da wannan amana da hannunka.

Lokacin da ya bude akwatun sai yaga kur'ani a cikinsa da wani littafi.

A iya fahimtata wannan makami d aya bashi ishara ce kan jagorancin gwagwarmaya sannan wannan littafi shi yana nuni zuwa ga fikra da Akidojin muslunci, hakika Imam Sajjad (as) ya ajiye su don imamin da zai zo bayansa bayan yayi bankwana da duniya ya tafi zuwa ga rahamar Allah cikin kwanciyar hankali da nutsuwa da izza.

Wannan itace gamammiyar sura da fuska ga rayuwarsa (as) sai dai cewa idan muna son karanta juzu'iyat da abubuwan da suka faru to ya kamata da farko muyi shimfida da sharer fage ga yanayin d aya gabata gareta, domin cikin rayuwarsa akwai wani gajeran fasali iyakantacce da zamu fara Ambato shi sannan daga bayansa muyi bayanin gamagarin rayuwarsa da kuma bayani dalla-dalla da fadada yanayi da sauye-sauye zamani da zuruf na wancan lokaci.

Fasalin makoma takaitacce shine marhalar bayan waki'ar karbala ma'ana marhala kamu da daurin da ya kasance takaitacce sai dai cewa ya kasance mai tasiri matuka da bada darasi ta yanda muka same Imam a wannan yanayi cikin jarumta da dakiya da karfi. Hakika Imam Sajjad (as) ya shata jarumta mai girma gaske ta hanyar zantukansa da ayyukansa a wannan lokaci da yake cikin dauri da rashin lafiya, wannan marhala ta banbanta sa sauran marhalolin rayuwarsa ta yanda ya wayi gari yana aiki karkashin kasa da dalili cikin tsakaita da dikka da dabi sannu-sannu, ya kasance a wasu lokutan yak an zauna tareda Abdul-Malik bn Marwan a majalisi guda yana mu'amala da shi mu'amala matsakaiciya.  Amma cikin wannan fasali lallai zamu ga Imam (as) ya fito da sura da zazzafar fuskar gwagwarmaya ta yanda muka same yaki kame bakinsa daga dukkanin kankanuwar magana, gaban taron mutane ya kasance yana yin martani da raddi da amsoshi da suke girgiza turakun makiyi.

A  cikin kasuwar garin Kufa cikin murya guda a zamani guda Imam (as) shi gwaggonsa Zainab da `yar'uwarsa Sukaina (as) yana huduba yana farkar da mutane suka bayyana hakika.

A Sham (siriya) a majalisin Yazid Imam ya bayyana hakikanin abubuwa da mafi bayyanar bayani ta yanda hudubarsa ta kunshi kalmomin cancantuwar Ahlil-baiti  da halifanci, wannan huduba ta tona asirin hukuma mai mulki da tona irin zalunci da tsanantawa da Sarkin ya kasance yana aikatawa kan mutane da basu sani, anan ba zamu iya kawo hudubar ba da bayanin ma'anoninta.

Marhalar bayan dauri:

Wani lokanci tambaya kan zuwa da cewa shin me yasa Imam (as) bayan sakinsa ya koma daukar matakin tsakatsaki da yin takiyya ya koma yin addu'a da tsakatakin ayyuka kan zazzafar gwagwarmaya alhalin a marhala da ya kasance cikin dauri ya kasance daukar zafafan matakai da tsage bayani.

Amsa shine marhalar dauri ta kasance wata marhaba ta musammam ta yanda Imam (as) tareda nesanta da kasantuwarsa Imami ya kamata ya tanadi yanayi ga motsin kafa hukumar muslunci, a wannan lokaci ya kasance mai bayyanar da zaluncin wadanda suka zubar jinin muminai a Karbala a ranar Ashura,, Imam Sajjad (as) a wannan lokaci bai kasance kan hakikarsa ba kadai dai shine ya kasance harshen da Imam Husaini (as) yake magana da shi wanda yayi tajalli cikin wannan matashin dan gwagwarmaya a Sham da Kufa, ba da ban Imam Sajjad (as) ya kasance mai zafafawa ba da bayani karara da tsage lamari da babu wata hakika da zata rage ga aikin da zai nan gaba, saboda fagen aikinsa na gobe jinin Husiani (as) da aka zubar, kamar yanda jinin Husaini shima a kankin kansa yayi shimfida da sharar fage ga motsin shi'a a tsahon tarihi.

 ya kamata ya gargadi mutane sannan cikin wannan mataki da sannu-sannu sai a fara dauki ba dadi da gwagwarmaya mai asali mai zurfi mai nisan zango.

Saboda hakane matakin Imam da Sayyada Zainab (as)  a wannan marhala ya kasance bayanin yunkurin Imam Husaini (as) domin fahimtar da mutane kisan Husaini da kuma kan wannan dalili aka kashe shi da sannu hakan zai yi tasiri a nan gaba gobe cikin da'awar Ahlil-baiti (as) sabanin ace basu fahimta ba. Saboda haka dominn samun tsinkaya da fadada wannan fahimta kan mustawan jama'a ya kamata a sadaukar da duk abu mai yiwuwa ga wannan motsi na Imam Sajjad (as) cikin wannan fuska misalin Zainab misalin Fatima sugra da Sukaina da dukkanin fursunoni gwargwadon ikonsu, dukkanin wadannan bangarori sun tattara don bayyana sirrin jinin Husaini da aka zubar cikin bakunci cikin dukkanin yankunan musulmai da wadanda suke gifta su tun daga Karbala har zuwa Madina, lokacin da Imam Sajjad (as) a shiga Madina ya kamata ya bayyana hakikar abinda ya faru a gaban taron mutane da suke kishirwa sanin hakika, hakika hakan ya faru farkon shigarsa Madina, saboda wannan fasali ya kasance gajere kuma wani yanki na musammam a rayuwarsa, yanki nag aba yana fara da farkon dawowarsa Madina a matsayin dan kasa, karatunsa na bude shafi daga gidan annabta (s.a.w) haraminsa.

Kiyaye sirri:

Wata rana wani mutum ya zo wajen wani Arifi sai yace masa: ya Shaik ! hakika na zo wajenka don ka sanar da ni wani abu daga sirrikan ubangiji, sai wannan Shehi ya bashi amsa: gobe ka zo zan gaya maka, lokacin da mutumin ya tafi sai wanna Shehi ya kamo bera ya ajiye shi cikin akwatu ya kulle shi kyam wayewar gari ke da wuya sai ga wannan mai tambaya ya zo yace bani amsar d akai ini alkawari, sai ya bashi wannan akwatu yace masa: kada ka sake ka bude sai zuwa wayewar gari sannan ka dawo mini da ita.

Sai ya tafi yayin da ya isa gida sai ya gaza yin hakuri kan sanin abinda yak e cikin akwatu, yayi bakin iyawarsa kan ganin bai bude wannan akwatu sai zuwa gobe amma tareda ya gaza hakuri daga karshe dai sai ya bude akwatun kwatsam sai ga bera ya fito daga cikinta yana yunkurin tserewa.

Sai ya koma wajen wannan Shehi yace masa, ya Shehi! Na nemi sirrikan Allah daga gareka amma sai ka bani bera cikin akwatu? Sai ya bashi: yakai wannan miskini mun baka bera cikin akwatu ka gaza kiyaye shi shin kana tsammanin zaka iya kiyaye sirrin Allah.

Kukan jini maimakon na hawaye:

Arifi ma'abocin wa'azi Alhaji mulla Suldan Tabrizi ya rawaito yana fadin: cikin mafarki Allah ya datar dani da gani hallarar Bakiyatullahi rayukanmu fansa gareshi.

Sai nac masa: shugabana : ya zo cikin ziyarar nahiya mukaddasa cewa ku cikin nmaganarku tareda kakanku Husaini (as) kuna cewa: zan kirayake cikin kuka safiya da maraice, zan yi maka kukan jini maimakon hawaye, shin hakan ya inganta?

Sai yace: eh ya inganta.

Sai nace wacce irin musiba ce da kake mata kukan jini maimakon hawaye? Shin musibar da afku kan Aliyul Akbar ce?

Sai yace: a' a da Aliyul Akbar yana raye da shima ya yi kuka kan wannan musiba kukan jini bana hawaye ba.

Sai nace masa: shin musibar Abbas ce, sai yace: a a da Abbas yana raye da yayi kukan jini kan wannan musiba.

Sai nace: to lallai musibar shugaban shahidai ce?

Sai yace: da shugaban shahidai ya kasance raye da yayi kukan jini kanta.

Sai nace: to wacce musiba ce haka?

Sai yace: lallai ita wannan musiba ba komai bace face fursunantar da Sayyada Zainab amincin Allah ya tabbata gareta.   

 

 


Tura tambaya